← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 215

Sashe 62

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fita fes cikin tsakiyar hijabin kalar luxury Morocco din jikinsa. Hasken dake fitowa daga cikin wayar ya haske fararen idanunta dake sheqi kamar an diga mai. Bai fasa saukowa ba kaman yadda taci gaba da takawa idanunta kafe akan wayar,har sai da cikin jikinta taji kamar ta iso qofar da zata sadata da parlor din. Daga kan da zatayi ta tsinceta dab dashi sanda yake stair din qarshe. Sai ta juya a hankali da zummar yi masa yadda ta saba wato komawa don ta kubcewa hada numfashi dashi. _Daga abu hurairah RA yace,manzan Allah S A W yace: "ku kashe baqaqe guda biyu koda kuna cikin sallah; MACIJI DA KUNAMA_ Taku biyu kacal tayi ya cimmata,ya kuma sanya hannunsa ya dawo da ita baya,sai gata tsaye cak a gabansa kaman ba inda ta matsa. Idanunta tsakiyar nasa idanun da suka qaa girma kadan saboda ciwon kan dazu,yayin da hucin numfashinsa ya dinga fita cakude da qamshin turaren jikinsa yana kaiwa ga hancinsa. "Wanne kalan dodo ne ko abun tsoro a jikina da kike gani?" Ya jefa mata tambayar a zafafe yana ware mata idanunsa. Ja baya tayi niyyar yi da sauri saboda yadda ta dan tsorata kadan da yadda idanun nasa suka qara girma,ga wani shimfidadden kwarjini dake fita daga cikinsu ya daki zuciyarta lokaci guda ya kuma ninka gudu da bugun zuciyartata. Hannunsa qwaya daya ya sanya yasake dawo da ita gabansa yana sake bude mata girman dukkanin idanunsa. "Ki nunan abinda ke baki tsoro a jikina nace!" Ya fada da dan tsawar takaicin abinda takeyi masan. Shi tun farko mutum me dan kai tsaye,koda laifi kayi masa yafison ka fuskanceshi kai tsaye.....haka koda matsala kake dashi yafiso ka tunkareshi kai tsaye ku warwareta. So take ta maida masa me zafi ko zata fanshe abinda ya gaya mata ranar nan,amma sai ta lalubi kwanyarta da bakinta tsaf ta rasa komai kamar an mata sata. Ringing din wayarsa ne ya sanyashi maida dubansa ga wayar. Kusan a tare idanunsu suka kai kai,kuma daga shi din har ita sunga sunan da yake rubuce a kai FAREEDA KHALED MUSTPHA. Maida dubanta tayi ga fuskarsa ba tare da tasan dalilin hakan ba,sai kawai ta zabi ta zille ta tsakanin qofar ragon da yayi mata,saidai kuma tana motsawa kamar hankalinsa yana maqale ne a jikinta ya daga kai ya watsa mata idanunsa bayan ya maida wayar aljihu ya sakeyin kicin kicin da fuska. "Daga yau duk ranar da kika qara ganina kika koma kaman kinga dodo saina biki har cikin dakin na zaneki tas ciki da baya". Maganar tayi mata banbarakwai,kamar wata nadra ko haneefa?,wannan mamakin ya bayyanata tsakiyar qwayar idanunta da baisan me yasa yake yawan sanya nasa idanun a cikinsu ba duk sanda magana irin haka ta hadasu. "Kina mamaki ne?,ko kina ganin kin wuce duka?,ki gwada koda gobe ne ki gani.....and,daga yau kada ki sake ganina baki gaidani ba......tunda ko banza ana ci dake ai ko?,koda ban baki abinda wadancan suke bakin ba" Ya qarashe maganar yana sakar mata hanya. Cikin qasa da second uku ruwan hawaye ya tararwa idanunta,ya za'ayi ya qara mata ciwo akan wancan ciwon,tana jin lallai yau ta barshi ya tafi haka yaci bulus din da ba'a taba cinta a kanta ba "Ka daina burga kaman kana da abun bayarwar.......ni bana buqatar ragowar su fareeda tunda akwai masu fresh......." Cak maganar ta tsaye mata a maqoshi sanda yayi wani irin waiwayowa daidai sanda yake dab da zarcewa falon. Batasan ta juya ba har ta soma tafiya zuwa dakinta ba sai da taji tana taka lallausan carpet din dake shimfide daga tsakiyar wajen. Dif wuta ta dauke masa,zuciyarsa ta shiga raya masa nau'ikan hukunci mafi tsauri daya dace yayi mata. Saidai kiran wayarsa ya sake katse masa duk wani hanzari,ya duba kiran a fusace yana tunanin fareeda ce,amma ganin maamah ya sanyashi tattare duk wani bala'i daya taso masa ya hadiyeshi,sannan ya daga wayar yace da ita a taqaice "On my way" "To ka hanzarta" Maamah ta fadi tana jin dadin yana hanya bawai yaqi amsa kiran nata bane. Kai ya jijjiga yana takawa a hankali yana ficewa,saidai a ransa yaci alwashin dole ya ajiye mata abun tunawar da bazai sake fadin magana ta maida masa ba. Duka duka shekarunta nawa amma sanadin aure raini yana neman shiga tsakani?". Ya fada qasan ranshi sanda yake tayar da motar. Da wani irin speed yake jan motar,wanda dama sabonshi ne gudu a mota,ba tun yau ba ba kowa ke iya shiga mota ba indai shine zai tuqa. Idonsa ya lumshe yana tuna abinda tace masan,sai wani sashe na zuciyarsa ke gaya masa.....zai wahala cikakkiyar budurwa me kunya ta iya fadin hakan.....ita kuwa bata cikin kowanne sahu,dom haka idan ta fadi sama da haka ma fuad kada kayi mamaki.....kowa yasai rariya yasan zata zubda ruwa. Har ya isa gidan maamah wannan kalmar ta kasa fita a ranshi "Ragowar su farida....kamar ma kana da abun bayarwar" Har cikin ransa ya gamsu ta rainashi,sai ya samu Kansa da kallon Kansa a side mirror,yana tuna dararen da yake kashewa a tsaye ba tare daya isa ya kwanta ba bare ya samu cikakken bacci saboda tsananin yadda ya kame kanshi. Da wannan bacin ran,da kuma tunanin hukunci mafi tsananin daya kamata ya dauka ya isa parlor din maamah. Mamaki na gasken gaske ya cikashi lokacin da yayi sallama ya tsinci fareeda cikin masu amsa masa sallamar tasa. Tana zaune hankali kwance saman sofa din parlor din. Sanye take da riga da wandon Palazzo daya bude sosai daga qasa. Rigar me gajeran hanny ta lafe a jikinta ta kamar yadda Palazzo din ya fidda shape din hips din ta zuwa qugunta. Bandana ce kawai saman kanta,hannunta riqe da wayarta. Kallo daya tak ya mata ya dauke kansa kai kace bai taba sanin wata halitta a duniya me ire iren kama da ita ba. Qasan maqoshinsa kuwa kawai kaiwa da kawowa maqogoronsa yakeyi,adams apple dinsa yana motsi daga sama zuwa qasa,ya taka a nutse kuma kai tsaye ya wuce gaban maamah din a ladabce. Tunda yayi sallamar ya shigo taji gaba daya an tsinke duk wata jijiya daka iya baiwa dan adam kuzari daga jikinta. Tunda take haukan son fuad bata taba tunanin haduwarsa da kyansa ya zarta yadda ta gagganshi bama sai yanzu data ganshi cikin shigar mutanen Morocco,wanda nan Nigeria zaka ga suna kama da tufafin da sarakuna ke sanyawa musamman idan suna ganawa da baqi cikin gida. Numfashinta cak yaso tsayawa,muhammad fuad ya wuce yadda take hangensa a nesa,a take taji tabbas zata iya sadaukar da komai data mallaka don ta samu fuad din a matsayin mijin aure (Anya....fuad din fa me tsada ne......amma muje zuwa,tunda kin kama maamah wataqila kina da rabo). Kusan duka gaisuwar da sukayi shida maamah da gajeriyar gabatarwar da maamah tayi masa bata ji ba "Baquwar taka ce muhammadu.......ina me umartarka ka saurareta ka kuma fahimceta.....duk wanda yayo tattaki qafa da qafa ya taho gareka saboda yana sonka ba qaramin masoyi bane,idan Allah yaso kuma matarka ce" Ta fadi maganan qarshe tana yunqurawa ta miqe. Daga kai yayi yana duban maamah sanda take jifan fareeda da murmushi,da salo kuma na bada goyon baya take cewa "Gashinan fareeda,bari na shiga na fito kafin ku gama" _idan Allah yaso kuma matarka ce_ yaji amsa kuwwar maganarta ta qarshe tana nanata kanta cikin kunnuwansa. Maganar sai taso ta masa kama da maganar data masa daidai sanda ta tilastashi auren waccar yarinyar.......me yake shirin faruwa?.ya tambayi kansa. "It will never happened" Ya fada yana qaryata komai da zuciyarsa ke qiyasta masa zai iya faruwa. "Hi......ka ganni har gida?,yanzu ka yarda garin masoyi baya nisa ko?" Ta fada tana sakar masa murmushi,murmushin nata dake daidai da diban garwashin wuta ta watsa masa. Wannan bai dameta ba,yanayin fuskarsa duka bata sakashi a mizanin damuwa ba.......zai gata ta zame tana saukowa qasa. Ta qaraso dab dashi tayi Zaman raquma tana dubansa "Please Muhammed kada kayi rejecting dina.....na maka alqawarin zame maka duk kalar matar da kakeso kake buri" Ta furta da tsananin narkewa. "Stop it please......ke me yasa baki nemawa kanki martaba mutunci da kima?". Ya fada bayan ya daga mata hannu ya dakatar da ita daga maganan farko launin idanunsa sun fara sauyawa saboda bacin rai. A rikice ta girgiza kai ganin yana juye mata zuw wannan fuad din me wahalar samu.....wannan fu'ad din me tsananin tsauri "Mutunci martaba da kima duka susha zamansu muddin zan samu muhammad fuad". Shuru ya ratsa qarshen maganarta,ya xuba mata ido yana sansano alamu alamun hauka tattare da ita,sai ya matsar da fuskarsa kusa da tata kadan,da wani sauti can qasa wanda tsanantar bacin rai da kuma sarawar da kansa yayi ya dawo da ciwonsa sabo fil ya tilas masa maganar a haka yace "Gashi shi kuma muhammad fu'ad din saida wadannan abubuwan ake samunsa......." Daga haka ya miqe tsam da zafin nama,sai gata ta miqe tare dashi cikin tsoro da fargabar kada yaqi tsayawa ya saurareta duk da kuwa ta dangana da mahaifiyarsa. "Umarni nake baki......ki tattara kayanki kibar gidan nan,kada na dawo jibi na sameki,don gobe ma tayimin kadan,bazan iya shaqar iska a wajen da kika dade a cikinsa ba". Yana kaiwa qarshe ya juya da zafin nama me gauraye da fushi ya soma fita. Ta dauka zata jure saita kasa,ta bishi a baya da gudu gudu tana kiran sunanss,saidai ko ta kanta baibi ba,ya bude motarsa ya shige ya kunna ya tasheta da wani irin qarfi ya fusgeta yana fita a gidan,don ko sanda ta qaraso sawayen motar kawai ta samu,saita zube a wajen tana qwala kiran sunansa,abinda kunnuwan maamah suka jiye mata kenan,ta fara saukowa da sassarfa daga sama. Baisan yadda yakai kanshi gida ba saboda tashin hankali da tsananin ciwon kan daya saukar masa,shidai yaji daya daga cikin security nasa na cewa yabar motar daga nan zai qarasa shigo da ita ya gyara parking din. "Sai yaushe maamah zata canza?,sai yaushe zata zama cikakkiyar uwa?,sai yaushe zata zabi girma da mutunci sama da kudi?,sai yaushe?,sai yaushe?". Kusan wannan shine abinda ya sanyashi kwana ya kuma tashi da ciwon kan daya hanashi fita,ya kuma kashe dukka wayoyinsa don baya qaunar ya nemi wani ko shi a nemeshi. *_WASHEGARI__* *_BAQIN DARE_* *_MUHAMMAD JADDA RESIDENT_* *10:45 NA DARE* Tunda ta fara kallon film din hankalinta bai kwanta
Chapter 62 · 0% Book details