← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 215

Sashe 134

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sanda yake miqewa zai wuce ciki "Zo nan muhammadu" Ta kirashi,sai ya dawo ya samu waje yana zama kujerar dake fuskantarta. "Wannan ciwon da yaqici yaqi cinyewa ina ganin ya kamata a auna yarinyar nan asan me yake damunta,kada mutane suna zamansu lafiya taje tana yawo da ciwo tana yada ma mutane tunda gata ga yadda take a baya". Sosai maganar maamah ta sokeshi,ya kuma fahimci inda ta sanya gaba,anni kuwa sai da tayi da gaske ta iya controlling kanta. Idonsa ya lumshe kana ya budesu ya gyara zamansa. "Ba wani ciwo da ameenatu take dauke dashi a jikinta......tunda nine mutum na farko dana fara karbar mutuncinta na 'ya mace......ciwonta na yanzun kuma nine silarsa.....ga bayanin nan a rubuce" Ya fada yana zaro takardar,sai kuma ya dakata yana dubansu. "Naji dadin ganinku a tare gaba daya" Ya fadi yana sake zura hannunsa a aljihun rigarsa. Dollars dubu biyu ya fiddo sabbi kar a miqe,ya miqawa maamah takardar ya kuma miqawa anni kudin. "Abba......alhaji hamza kibiya ta hannuna ya karbawa musaddiq mahmud jadda auren amna......bisa sadakin dala biyu biyu lakadan ba ajalan ba......ta hannun wakilinsa abokinsa alhaji muhyidden kibiya da tarin shaidu cikin masallacin annabi muhammad SAW,bisa yarjewar waliyyansu ni muhammad fu'ad jadda da kuma abba wato alhaji hamza kibiya"...... TURQASHI!......FU'AD.....NACE ME JADDA?,WANNE IRIN MATCH KA TARO HAKA?,KO TAKARDAR DA MAAMAH TA WARWARE BAKA BARI TA GAMA DUBAWA BA?. TO NIDAI JAMAA WANNAN FADAN YAFI QARFINA NAYI NAN *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 115 _____________________________ _kin dade kina cizon yatsa kan yadda ake kacalcala suturun yaranki da dinkuna marasa ma'ana?_ _HUGUMA na miki albishir da wajen zazzafan dinki na MS KIDDIES WEARS,irin dinkunan yaran da kike gani a Instagram TikTok suna burgeki kuma bakisan inda zakikai ayi miki ba ko kina tsoron tsada_ _Zafafan dinki na gayu da ado kiga yaranki sun fita dagwas dagwas_ _ready _MS KIDDIES na nan kano gwammaja_ *TRUSTED AND TRUSTED mun gwada mun gani* _Maza tuntubeta a nan_ +234 708 865 2858 Ko Instagram account dinta https://www.instagram.com/ms_kiddies_wers_by_nafs?igsh=MTljZWQwM2FsaXlxaA== ______________________________ 115 Dukkanin wani da yake numfashi a wajen saida jinin jikinsa ya daskare na wucin gadi,qwaqwale da yawa suka dakata da aiki na wasu mintuna,yayin da idanuwa sukayi warwaje a kansa. Kowa dubansa yake d wani irin madaukakin mamaki da tarin ba zata,dukkaninsu kowa kwanyarsa ta kasa fahimta ko sarrafa maganarsa. "Mem.....me kake cewa fu'ad?" Anni mutum qwaya daya da tayi qarfin halin sake tambayarsa tana jin yadda jinin jikinta uske tsinkewa. A nutse ya dubi annin nashi,yana da qwarin gwiwa da zato me yawa a kanta,don haka kansa tsaye yace. "Na aurar da amna ga musaddiq cikin masjid nabawi bisa shaidu da wakilai da sadaki dala dubu biyu" Sai a sannan kwanyar wasu daga ciki ta harba ta kuma dawo da aiki,ciki harda amna. Wani tsananin tsoro taji yana shigarta,ta shige jikin anni tana buya a bayanta gami da cukuikuyeta,idanunta kuma suna sauka kan fuskar maamah. Wannan fuskar da take bata wani tsoro haka kawai,fuskar da batason kallonta saboda duk wani yanayi da alamu na rashin wanzuwar alkhairi tattare da ita tana ganinsu......a yau mamallakiyar wannan fuskar itace a mazaunin surukarta?. Shi kuwa musaddiq kama hannun saddiq yayi ya riqe da kyau yana qoqarin tuna maganganunsa da hamman masa mintuna ashirin baya da suka wuce kafin ya shigo cikin asibitin. Abubuwa biyu ke masa kai kawo suna gwarabkiya cikin zuciyarsa,farinciki da kuma fargaba da wani sofane na tsoro dan kadan. Kalaman bakin maamah wani irin daci da dafi ne dasu wanda ya kasa sabawa da jinsu,baya qaunar komai ya hadashi da ita alkhairi ko sharri,dadi ko akasinsa. Idanu kawai anni ta zuba ma fu'ad tana jin tsigar jikinta na tashi. Wanne irin tashin hankali ne haka fu'ad din ya rakito mata tana zaman zamanta tana lallaba tsufanta?. Wacce masifar ce ke shirin wanzuwa?,meye kuma zai afku gaba ga amnanta?. "Allah ya sanya alkhairi......yasa anyi a sa'a" Lafuzzan suka fita daga bakin maamah da tayi qoqarin ware idanunta daga qanqancesu da tayi. Ba wanda kalamanta basu bawa mamaki ba.......kaman yadda suka janyo hankalinsu ga fuskarta wadda ta maida idanunta kan takardar hannunta tana qoqarin hana zuciyarta tsananin bugun da takeyi,tare da fatan gumin dake yanko mata ya tsane jikin atamfar jikinta ba tare da kowa ya gani ba. Abu guda daya data sani shine......tabbas fu'ad ya siyawa amna tikitin salwantar rayuwarta......don bataga ta inda zata bari itakam da ranta da lafiyarta ta hada jini da alhj hamza kibiya ba..... Idan fu'ad baiyi wasa ba a wannan karon,zata rufe idanunta tayi hukuncinta kan me uwa da wabi......zata mance da alaqar dake a tsakaninsu tunda har ya iya mancewa da matsayinta a wajensa. Saddiq musaddiq harma da amna sai lafazin maamah din ya sanya suka fara jin abinda ke ransu yana sassauta,wanda sam ba haka bane a qirjin anni da fu'ad. Wani duba sukaci gaba dayi mata,kowannensu yana son karanto ainihin ma'anar maganarta. Sun riga da sun sani.........banza bata kai zomo kasuwa......hakanan kowa ya tuba don wuya to tabbas babu lada.......ba haka kawai maamah zata bada amsa ga lamari me girma irin wannan ba......ba haka siddan zata miqa wuya ga al'amarin daya fado bagtatan irin wanna ba.....TABBAS AKWAI WATA A QASA. Lokacin da idanunta suka kai kan conclusions na gwajin sabreen din sai ta fara qanqance idanunta a hankali,ji tayi kaman debi yaji an watsa mata cikin idanunta kafin a hankali taji kaifin ganinta kaman yana raguwa. "Ciki?,sati uku?" Tambayar data samu daman motsa labbanta ta yiwa kanta da kanta kenan. Iskar dakin taji tana mata wahalar shaqa,kamar babu isashiyar oxygen dake wulgawa ta wajen,takai hannunta wuyanta tana janye mayafin data yafa waiko yana cikin abinda ya jawo mata qarancin iska,still sai taji ba abinda ya canza. Da gaske iska ke neman mata kadan,wannan ya sanya ta soma jan iska da qarfin gaske tana aikawa hunhunta don ta samu taci gaba da numfashi,yayin da ilahirin jikinta ya soma rawa kadan kadan. Musaddiq ne ya fara ankara da hakan,don fu'ad tuni ya soma takawa xuwa dakin da sabreen take don kaucewa kallon tuhumar da anni ke jifansa dashi. Baida matsala da duk wani tuhuma na maamah ko kuma kalar kowanne qalubale daga gareta,damuwarsa daya yadda annin dama zata karbi abun,ko ita dinma ya shirya mata,don bayajin akwai wani abu guda daya daya dace yayi sama da wannan din. "Lafiya?.....kaman numfashinta baya kaiwa" Anni data iso gurin ta fada tana duban hannunta wanda takardar gwajin da fu'ad ya bata ta sulale ta fadi a qasa. Yanayin sautin anni ya sanyashi dawowa da baya,yadan daga qafa yana qarasowa wajen,sai yayi saurin matsawa wayar dake ajiye a dakin don neman daukin likita ko nurses ya soma kira. Minti guda kacal sai ga mutum biyu tare da likita sun qaraso,saman wheelchair aka dorata sannan suka turata xuwa dakin da yake daura da wannan. Dukkaninsu suna farfajiyar dakin daga waje,suna jira suji bayanin da likitan zai fito dashi. Duk bayan sakanni sai anni ta daga idanu ta dubi fu'ad,gaba daya ya gama warware mata zaren tunaninta. Wannan wani abune nashi na daban,tsahon zamanka dashi zaku iya qareshi ba tare da ka iya fadin gundarim halayensa ba gaba daya,yakan zo da abubuwan da hankali da tunani basu kawosu ba,yana da bada mamaki irin hakan,saidai bata taba kawowa zai iya aikata qunar baqin wake irin wannan ba. shima kansa ya sani,duk wani kallo da anni take masa yana cure ne da mamakinsa,saidai ya sakawa kansa wannan dakiyar da juriyar da wani irin basarwa,don haka ko sau daya yaqi kallon anni,saidai yasan shi take kallo ta gefan idanunsa. Basu wani jima ba suka fito,suka qaraso gaban fu'ad din. "Ba wani abu bane me tsanani,kawai ta shiga shocked sosai daya sanya jininta hawa lokaci guda......irin wannan case din yana iya jawo mutuwar barin jiki ko bugawar zuciya idan yazo da akasi.....zuwa yanzu dai ita Allah ya tsallakar da ita,saidai kuma jininta yahau sosai,an mata allura ya kuma sauka alhmdlh,nan da awa daya ma zata iya tafiyarta gida.......amma fa sai tana kiyaye saka bacin rai da damuwa a ranta". "Na gode Dr" Fu'ad ya fadi yana bawa Dr hannu sukayi musabaha ya wuce. Musaddiq ya kalla sai ya taka zuwa cikin dakin saddiq ma ya bishi. Idonsa yaketa qoqarin kawarwa daga annin don kada su hada ido ya soma takawa zai shiga ya duba maamah din amma sai sautin annin ya katseshi. "Ka kyauta" Ta fada kai tsaye,abinda ya sakashi dakatawa daga tafiyar da yakeyi kenan. Shuru ya ratsa na wasu mintuna,sai kuma ya dawo da baya a nutse ya tsaya gaban annin. Hannuwanta ya riqe yana zaunar da ita daidai sanda take fadin. "Kaga irin abinda ka jawo ko?" Zame takalmin qafarsa yayi ya zauna sosai a gabanta ba tare daya damu cewa marbles bane a wajen. "Ban jawo komai ba anni.....kuma komai bai faru ba,ko ba wannan maganar irin wannan ranar irin wannan lokacin yana dab da faruwa da maamah....... Tunda muka tashi bamu san wani abu farinciki ba sai a sanadinku.......musaddiq ya rasa abubuwa masu yawa tun yana yaro......yanzun kuma a sanadinta sai a haramta masa abinda yake buri yake muradi yake kuma so?,bayan a baya ya rasa abinda yake buri da muradin kuma duka ya haqura?" Tambayar tasa tadan taba annin,saidai duk da haka sai takejin kaman bai kyauta ba abinda ya yiwa maamah,ko ba komai ita ta haifi musaddiq din ta kawoshi duniya. Ta bude baki zata sake magana yayi caraf ya riqe hannunta sosai,abinda bai taba yi ba. Idanunta ta daga tana duban nasa idanun,wadannan alamun bacin rai mai tsanani din sun bayyana sosai cikin idanunsa,alamun ranshi ya motsu sosai. "Kina tunanin ga musaddiq......zan bari amna ta auri wani a waje koda baice yana so ba?,wanin da bamu da tabbas a kanshi?,wanin da ban isa na hukuntashi ba idan ya cutatar da ita duk yadda muke sonta kuwa?.........Karki sake cewa komai anni don Allah na roqeki,bakinki kada ya sake furta komai a kansu idan ba fatan alkhairi ba......indai har yanzu kin yarda kina kuma ji a ranki ni da musaddiq 'ya'yanki ne.....amna qanwata ce halak malak kamar yadda musaddiq yake....to karki sake cewa komai sai fatan alkhairi.....ko meye zai faru.....ko menene zai taso anni na roqeki ki saka idanu.....nike da alhakin hakan kuma nine zan dauka". Gaba daya ya gama kashe mata jiki,ya kuma kashe duk wata kalma
Chapter 134 · 0% Book details