Sashe 197
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
na jiraran design daban daban suke welcoming naka. Kana shiga gurin zakasan guri ne bana wasa ba.....guri ne da akayi barin dukiya,irin barin da zai gaya maka ba'asan zafin kudin ba,don an nemesu a sanda ya dace an kuma tarasu. Komai a tsare yake,don guri na musamman aka tanada saboda ajjiye yaran. Kowa xai qarasa ya gansu,me buqatar basu gift ko wani abu makamancin hakan amna da huda suna kusa,don sune iyayen yaran gaba daya. Cikin tsari aka soma gudanar da taron,sabreena maman yaran wadda ta koma hajiya sabreen,tayi wani irin razanannen kyau cikin wani dan banzan lace da aka warewa milliyoyin kudi aka bada order saqashi a india. Ba iya lace din jikinta kawai ba......hatta da lace da atamfofi da manyan luxury warmers da aka raba a gurin duka container guda akayi musu. Tun kana lissafa adadin kayan ciye ciye da shaye shaye da aka tanada a wajen zaka gaji ne kawai,don kuwa tsarin serve yourself kawai akayi,debi da kanka,kaje ka zaba ka zuba koka aika a debo maka,ko ka kira daya daga cikin ma'aikatan dake wajen ka bashi order din abinda kake da buqatar ci. Guri na musamman aka tanadarwa jama'ar DUNIYATA,don a idanun sabreen mutane ne masu kima mutunci da daraja,wadanda suka taimaka qwarai wajen bawa dangantaka dama soyayyarsu gudunmawa. A gurinne fannah ta gabatar da kyautar da BB ya yiwa takwaranshi,wato kyautar sabon company dinsa na sarrafa auduga da fiddashi qasashen waje.....daukan nauyin duka wani abu da ya shafi rayuwarsa,tun daga karatu lafiya sutura da sauransu,yace kawai abbanshi ya zuba masa idanu,don shi aka haifawa umar din. Bama umar duka ba.....dukkanninsu yana jinsu a zuciyarsa,saidai yace bazaiyi qarya ba umar din na dabanne a wajensa. Abba baiyi qasa a gwiwa ba shima ya aiko da nashi saqon ta hannun amna,estate guda ne me dauke da gidaje dari ya mallakawa nasa takwaran. Ihu aka dinga yi a wajen,saboda yadda abun ya qawatar da mahalatta taron,wato dai gasa ce ta gasken gaske tsakanin kowa da takwaranshi. A sannan fu'ad din yana daga can gidan hutawarsa,yana kallon yadda taron yake gudana kamar a gabanshi,ta hanyar cameras da ya saka aka zuba sosai a wajen,aka kuma miqa ragamar monitoring dinsu a hannun qwararrun security dinsa. Saidai duk da haka yaji yana sha'awar zama,yayita kallon duniyarsa da yanzun ta rarrabu da wasu hadakar qananun duniyoyin har guda uku. Murmushi ya saki yana gyada kai,shi za'a yiwa wariyar launin fata kenan a ware masa abbansa?,kawai sai ya dauki waya ya kira musaddiq da nashi saqon. Sanda musaddiq ke sanar da bada kyautar JADDA WINGS ga almustapha kusan kowa sai da yaji shock,kafin daga bisani gurin ya kaure da tafi. "Sannan nima ina gabatar da tawa qaramar kyautar motar" Ya fadi yana fiddo maqullin motar daga aljihunsa ya dagashi sama ya kuma isa gaban abban nashi almustapha ya ajiye. Motace me bala'in tsada new model,wadda har yanzun ko cikin masu kudi ba kowa bane ya samu nasarar mallakarta ba. Tabbas abban abba ne,kusan yafi kowa a cikinsu tashi da gwaggwabar kyauta. Kafin abar gurin fu'ad ya sanya qaramar musabaqa ga yara masu haddan qur'ani a wajen,daga shekara goma sha biyu zuwa qasa,koda izu uku ke gareka kuwa. An gwabza musabaqa me kyau,abinda ya sake janye hankalin sabreen taji a duniya bata da burin daya wuce yaran nata su zama mahaddatan alqur'ani. Sai da aka kammala komai sannan anni itama ta gabatar da nata kyautan. Motoci ne masu kyan gaske guda uku iri daya sak,dukkaninsu farare qal,amna kuwa wani babban box ne da ba wanda yasan ainihin meye a ciki. Fannah ma ba'a barta a baya ba,itama da nata gift din,haka dai kusan duk wanda yazo wajen da nasa alkhairin da zai gabatar, Muhammad fu'ad jadda ba qashin yarwa bane,komai arziqinka komai kuma babunka ba zaka taba cewa baka amfana dashi da komai ba,wannan ya saya ma yaranshi dama matarsa wata irin soyayya da qauna. Taro ya tashi lafiya,yara kuma sun tabbatar da sunayensu na ALMUSTAPHA MUHAMMAD JADDA(FAWAD). HAMZA MUHAMMAD JADDA(FAUZAN). da babban aboki amini kuma dan uwa UMAR MUHAMMAD JADDA(FAWWAZ). Yaran sunzo da wani irin yanayi a dangi gaba daya,yan uwa dama wadanda ba 'yan uwa ba kowa ya tafi da fawwaz fauzan da fawad a bakinsa. Kusan gaban idanunshi aka gama komai,koda ya dawo gidan wajen sha biyun dare yayi mamakin haurowarta samanshi batayi bacci ba. Daga qofa ta tsaya ta langabe kafada,ya saki murmushi yana cewa. "Qaraso ciki........kinsa yau duka kishi ya kamani......na kasa sukuni sam". Ido ta zaro,ya sakata sakin murmushin da bata shirya ba. "Hamma.....kishin me?,duka mata ne fa a wajen,yaran dake wajen under age ne fa?". Idonsa ya lumshe yana duban dukiyar fulaninta da suka tutturo kaman suna tsokanarshi ne ma,lafiyayyar farar fatarta dake samun kulawa tana sake qawata su,uwa uba kuma yanayin rigar da tayi amfani da ita V neck ne da aka shimfidawa lace. Wani abu ya hadiye a maqoshinsa kawai ya miqa mata hannu,tana mamakin maganarsa ne,don haka sam bata lura da mayataccen kallon da yake watsa mata ba. Tanata masa surutu na labarin taron suna,har sai da yayi mata wata kyakkyawar runguma sannan hankalinta ya dawo jikinta,dif surutun ya dauke,shuru ya wanzu a dakin,sai sautin bugawar zuciyoyinsu. Duk wani gaba ta jikinsa sai data amsa,ya sake cusa hancinsa cikin jikinta yana jin qamshinta yana birkitashi. "Sati uku adda na......sati uku da haihuwan su fauxan right?" Kai ta gyada masa,sai shima ya jinjina kansa yana dan zame jikinsa kadan daga nata. "Naga kaman kinyi sallah daxun da asuba ko?". Qirjinta ya buga tsoro ya saukar mata. "Hamma.....nayi sallah......amma fa three weeks....." Yadda ya zuba mata jajayen idanunshi ya hanata qarasa magana,ta maida abinda takeson cewa. "Yayi wuri?,nasan haka zakice.....amma bakisan me nakeji bane sabrrrr". " I know hamma......na sani,ba wani motsinka da zan kasa gane manufarsa.......I will always be ready to accept you.....amma yanzu hamma,dr tace ina buqatar time kafin wannan abun,yana da kyau nayi healing sosai". Zame jikinsa yayi yana lumshe idanunsa ya koma wata kujerar daban ya zauna yana dafe goshinsa. Tausayinsa taji ya kamata,ta tako a hankali zuwa gabansa ta tsugunna tana dora hannuwanta saman cinyarsa. "May I help you?.bette" Idanunsa da suka sauya launi ya bude a hankali yana kallonta,saita sake gyara tsugunonta "I will help you to feel better" Idanunsa ya ware a kanta yana dafe hannuwanta. "No.....ba abinda hakan zai qara bazai magani ba.....komai zai iya faruwa don qishirwa kawai zaki qaramin......dawo nan ki zauna muyi hira" Abinda yace kenan da ita yana ture mata pillows din da suke gefanta. Hirar kuwa tayi masa sosai,ta dinga bashi labaran abinda ya faru a wajen. Tun yana tsume har ya ware,ya soma dariyan abubuwan da take bashi labarin,qarshe dai a nan suka bingire yana rungume da ita,basu tashi farkawa ba saida kiran wayar tashin triplet ya farkar dasu.