← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 215

Sashe 148

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sabrrrr" Ya samu ya fusgi kalman da qyar zuciyarsa naci gaba da bugawa. Itama kaman zai bace mata takeji daga qiftawa qwaya daya tak da zata yiwa idanunta,don haka ta motsa labbanta ba tare da amsar NA'AM din da takeson furtawa ta fita a bakinta ba. "Love is in the eyes.....eyes don't lie.....sabrrrr.....kalli idona.....me kika gani?" Ya motsa labbansa ya fada da wata irin narkakkiyar murya irin wadda soyayya ta yiwa lahani. Inda yasan yadda qwayoyin idanunsa suke narka mata bargo da bai buqaci ta kallesu har haka ba....saidai kuma kallon nasu wani abune na musamman cikin ruhi da zuciyarta. Ci gaba tayi da kallon idanun nasa.....taga abubuwa masu tarin yawa.....taga abubuwa masu yawan da sai da taji kaman zata zauce,duka ita daya?,duk ita daya muhammad fu'ad kewa wannan zazzafan son?. Hannu ya kama ya riqe kumatunta yana aza shimfidadden murmushi kan fuskarsa. "You're a thousand miles away.......but no one else is closer to my heart than you are" Ya qarasa fada yana kama fuskarta sosai gami da hade goshinsu guri daya. Musayar numfashi suka fara yi a tsakaninsu,kowanne yana shaqar numfashin da dan uwansa ya fesar,hakan na sake qara musu wani qaqqarfan alaqa tsakaninsu data tsananta bugun zuciyarsu duka su biyun. "Zan iya mutuwa.......Allah zan iya mutuwa idan ka sake matsawa daga gareni irin wannan matsawar da kayi.......zaka iya rasani......ka rasa kuma babies dinmu gaba daya" Ta qarashe maganar tana sakar masa kukan da ya koma zuwa na shagwaba kuma a wannan lokacin. "Nayi alqawari DUNIYATA.....nayi alqawari bazan qara ba,i promise" Fuskarta ta qwace ta cusata cikin qirjinsa tana shaqar wannan tattausan qamshin nasa da tayi matuqar kewa kamar zata zauce. "I pray to god that you will stay permanently in my life". "I pray too my world" Ya fada yana kissing tsakiyar kanta. Qanqameshi tayi da kyau don sake bawa kanta tabbacin reality ne bawai mafarki ba. Kalmar "wash Allah na" Daya fada ita ta sakata saurin sakinsa tana kallon fuskarta. Idanunan dai nashi ya zuba mata murmushi na fita a fuskarsa,sai ta tabe baki kaman zata saki kuka. Da sauri ya mata nuni da hannunsa,ta waiwaya a hankali zuwa sashen da yake nuna mata din. Miqewa tayi ta zauna da sauri saidai ya hanata hakan,ya jawota jikinsa ya maidata sosai yadda zaici gaba da jin qamshinta da duminta. "A nan suka harbeka?" Ta tambayeshi a sanyaye da wani irin emotion na bacin rai saman fuskarta. Girarsa kawai ya dage mata yana dubanta har yanzu fuskarsa da murmushi duk da yadda yadan fada kadan. "Allah ya isar mana....Allah ya saka mana" "Very soon duniyata......mu ajiye wannan maganar yanzun......i need you duniyata.....kaman dazu naji kince babies instead of baby right?" Ya tambaya yana tsareta da idanunsa. Tsam tayi tana dubansa,sai kuma ta saka tafukan hannayenta duka biyun ta lullube fuskarta dasu. "Yes......twins n....." Bata qarasa fada ba taji yana lalube rigarta,saidai jikin ba qwari kwata kwata da alama don haka ya ajiye hannun nasa yana maida numfashi. Koda ta kalleshi kwantaccen hawaye ta gani saman idanunsa,batasan me yasa akan duk abinda ya shafeta ba shi rago ne na gasken gaske. "Please sabrrrr......ki dagamin rigar na gani,haka Allah ke sona?" Yadda yayi maganar da gaske abun ya taba ranshi,ba zata iya hanashi ba,don haka ba musu ta miqe ta yaye abayan jikinta,tayi qasa da under wear dinta take farar fatar cikinta ta fito. Jawo qugunta yayi sosai,a hankali ya aza labbansa saman mararta. Har tsakiyar kwanyarta taji wani yaarrrrr,wani abu ya tsarga mata ya saukar mata da wani irin yanayi a sassan jikinta. Lips dinsa nakan marartata ya daga idanunsa ya kalli yanayin fuskarta,kunya ta sakata runtse idanunta sai ya aje mata tattausan kiss sannan ya janye bakinsa ba tare daya saki rigar ba. Batasan me ya karanta ba,amma ya kusa mintina biyu bakinsa yana motsi kafin ya matsa kusa ya tofa mata abinda ya karanta din,ya sake kai hannunsa ya aza akai ya sake karanta wasu addu'o'in sannan ya sake mata rigar. Still hankalinta yana kan hannunsa,tayi taku biyu zuwa wajen ya sake jawota jikinsa "I really missed you......kiban koda 10minutes naji duminki......ban taba zaton zan sake rayuwa ba......dazu na tashi daga suman da nayi duniyata" Yayi maganar yana aza kansa saman kafadarta,yana jin ya samu wani peace daya dauke masa duk wani abu da yakeji a jikinsa da zuciyarsa. Idanunta sukayi rau rau da hawaye "Ko waye wannan bazan taba yafe masa ba.....ko wayeshi" Ta fada muryarta tana rawa. Ya buda baki zaiyi magana muryar farouq ta ratso dakin,yadan bude qofar kadan amma fuskarsa da idanunsa sun basu baya. "Su musaddiq kuwa zasu samu yin dubiyar nan?,ko kuma su koma kawai sa dawo?". Sassanyan numfashi ya aje kafin ya motsa labbansa. "Bansan me yasa baka da imani ba farouq....aidai ka tausayamin ko?.....na yafe dubiyar,kaima ka bisu kuje ku huta......thanks so much dude". Baki kawai farouq ya sake,ya dauka fu'ad din zai tuna dasu anni a wajen ya sakaya zancansa?. " Dama shi dan adam butulu ne ai,na maka welcome to the world ai ko?,alright.....but kasan hannunka yadda yake......yana buqatan a kula dashi.....still itama me jinyar taka ba'a dade da sallamarta daga asibiti ba.....banajin she can take good care of you". "I can BB.....i can wallahi" Sabreen ta samu kanta da fadin haka ba tare da wani kunya ko d'arr ba. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 127 *_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_* *_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_* *_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_* *_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_* *_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......G YARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_* *_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_* *_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_* *_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_* *_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_* *_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_* *_HAIHUWA KIKAYI?_* *_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_* *_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_* _Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_ 08104553105 08127084190 *_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_* *_BGAWO'S KITCHEN_* *MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU* 127 "Pay no attention to him,brush him off" Fu'ad ya fadi yana lalubenta,abinda ya dameshi kawai shine yaga abinda ya sameta don yaji farouq yace bata da cikakken lafiya. Fes farouq yaji abinda dukkaninsu suka fada,ya jijjiga kai yana mamaki "Fu'ad......farouq ne fa?,lafiyanka nake magana kana gwaleni?". Hannun sabreen ya kama ba tare daya waiwaya sashen da farouq ke tsaye ba,a yanzun baya buqatar kusanci da kowa idan ba ita ba.....idanma akace wani zaya zauna dashi a dakin ai yana ganin an gama zaluntarsa. Yasan tsiyar farouq tsaf zaice shine zai zauna dashi saboda mugunta,yadda ta gayawa farouq kai tsaye zata iya kulawa dashi ya matuqar burgeshi,don haka ya qara encouraging nata. "Take what he says with a grain of salt,dont let him get to you" Ya fadi yana sake juya hannuwanta yana dubawa. Salin alin farouq yaja qofan yana wucewa,saidai a ransa ya ayyana dashi fu'ad din yaci tuwo,zaisan kuma miya yasha "What's wrong with you my world?" Ya tambayeta yana tallafo fuskarta,yaga alamun bata fahimta ba sai ya canza salon tambayar. "Farouq.....yace baki da lafiya.....da gaske ne?" Murmushi ta sakar masa,ta miqa hannunta a nutse tana kama habarsa me cike da kwantaccen gashi. "Kana tunanin zan iya lafiyayyar rayuwa sanda ake shaidamin muffin dina yayi batan dabo cikin DUNIYARSA?" Tambayar ta sanya murmushi kubce masa shima,ya girgiza kai yana kallon zara zaran eyelashes dinta. "Wannan ciwon nayi.....amma daga yau na warke in sha Allah". Knocking na qofar da akayi shi ya katse musu wannan daddadan tattaunawar,ya kalleta yana dan hade rai da alamun gajiya da rashin jin dadi a fuskarsa. "Inda zai yiwu.....zan sanya a sauyamin dakin da babu wanda ya sanshi bare a dameni" Idanu ta waro waje tana miqewa a nutse. "Da BB yace na hure maka kunne....kuma daka cika me butulci". "Kibar ganin farouq haka duniyata....zai iyayin abinda yafi nawa" "Qarya kakemin......kunyarka tafi tawa yin qaranci" Muryar farouq din ta ratsa dakin sanda sabreen ta bude musu,itadai sai tayi baya tana boye fuskarta. Da idanu kawai ya bita yana sake ganin ta canza masa,ko takan tsiyar da farouq keyi masa da raddin da yake maida masa baibi bama sam sam. Likitansa ne ya shigo a bayan farouq din,sai fu'ad ya kimtsa yanayin fuskarsa ta hanyar rage fara'arsa yana duban sabreen. "Ki shiga toilet ki gyara lullubin kanki sosai.....banaso ko gashi daya ya fito" Ya qarasa fada yana maida dubansa ga likitan wanda dauke idanunsa kenan daga kan sabreen din. Fuska a hade fu'ad din ya kalli farouq sanda likitan ke buda qirjinsa yana auna gudun zuciyarsa. "Ka gaya masa,He should look down when she's around,matar aure ce". "Tashin hankali" Farouq ya fadi,yasan ba qaramin daru za'a sha ba.....kowa ma sai ya shiga uku muddin duniyarsa tazo......wannan ya sanya yaso ya boye har sai ya fara samun lafiya da kuma sauran dalilai na tsaro da sukeso su gama binciken duk wanda keda hannu a cikin attack din ba tare da kowa ya ankare ba. Yasan da biyu ya fadi ragowan maganan da turancin englishi,dole yasan likitan zai fahimci wani abu. Sanda ta dawo daga toilet din gyaran mayafin kujera farouq yaja mata yace "Zauna a nan" Ya fada yana ajiyeta kusa dashi. Likitan yaci gaba da duk wani dube dubensa,ya kammala yayi rubuce rubuce ya ajiye file din ya fita farouq ya bishi. Idanunta still akan hannun,har yanxu tana jin ciwon kaman cikin jikinta,yanzu kenan ida harbin ya subuce ya sameshi a inda ba'aso yanzun da wani zancan daban kenan akeyi?. "Subhanallah" Ta samu kanta da furtawa tana dauke idanunta sai caraf suka fada cikin nasa. Abinda bata sani ba kallonta yakeyi da duk wani motsi nata. Ya miqa mata hannu yana daga kwance rigingine. Kafadarta ta noqe tana dubansa a shagwabe. "Kasan wadanne irin wahalallun kwanaki na dinga yi cikin duniya kuwa?" Idanunta suna tara hawaye har batason tuna wannan kwanakin. "Inda nine inajin da tuni fargaba ya kasheni.......kinsan adadin son da nake miki kuwa?" Kallonsa take har bata qiftawa,tanason gwada ma'aunin sonsa a zuciyarta
Chapter 148 · 0% Book details