← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 215

Sashe 147

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

da haske,irin iskar dake fitowa daga tsirran da aka wadata bayan dakunan dasu,wanda kana iya hangen komai tarwai ta gilasan da dakunan ke dashi daga gaba. Sam parlor din baiyi kama da asibiti ba,an saka sofas set guda,tv plasma freezer da side tables da babba guda daya,curtains da komai na parlor din fari ne qal tamkar hannu baya tabawa saboda tsananin kula da tsafta,hakanan qamshi ne me kwantar da hankali kawai yake fita. "Akwai likita a ciki a tare dashi,bibbiyu bibbiyu nake ganin ya kamata a shiga......" Farouq ya fada yana rarraba idanunshi tsananin fuskokinsu. Sulalewa tayi ta zauna saman sofa din,koda farouq yace ta fara shiga batajin zata iya hakan,gwara a cikinsu wasu su fara shiga din,yanayin fuskar kowannensu shine zai bata qwarin gwiwar shiga ko akasin hakan. Kaman anni zatayi magana sai kuma ta fasa,ita da abban sukayi gaba farouq yana musu jagora suka buda qofar suka shige. Zaman jiran fitowarsu annin ba wani abu bane me sauqi a wajenta,sai ta jita tamkar tana zaman jiran isowar layin mutuwa kanta,kanta a qasa ta saka hannuwanta dukka biyun ta dafe kanta tana jin yadda zuciyarta ke harbawa kaman zata fado qasa. Wani motsi takeji mararta tanayi,baqon abune da bata taba jinsa ba sai a ranar kamar ana d'allinta da yatsa. "Hasbiyallahu la'ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" Ta dinga maimaitawa labbanta kadai ke motsawa. Da yatsunta ta dinga irga kowanne wucewae second,tanajin kaman suna wucewa da kowanne dama na rayuwarta,tana jin kamar suna wucewa ne da farincikin rayuwarta gaba daya. Sai da su abba suka kwashe mintuna kusan goma harda doriya kafin taji fitowarsu. Duk yadda taso daga kai ta kalli reaction na fuskarsu ta gaza yin hakan,ta kasa koda motsawa,tana jin tsoron abinda zata daga ta gani tattare dasu. Saidai takum tafiyarsu su biyun bata tsinci komai a ciki ba,karsashi ko akasin hakan,wanda hakan ya sake sanyata a taraddadi me yawa da kokwanto. "Ni zan shiga" Ta fada da wani irin fusgar kalma cikin ba zata a sanda saddiq da musaddiq ke takawa zuwa qofar dakin. Miqewa tayi ta zauna sosai tana dubansu sanda suka dakata daga shigar da juyyayyun idanunta,tana jin kamar kafin su shiga su fito zata iya rasa numfashinta da rayuwarta gaba daya,koma meye gwara ta shiga ta gani ta kuma fuskanceshi da.dukkan iyawarta,da wannan qudurin ta taho,ba kuma zata iya canzashi ba. Da baya suka dawo,ba wanda ya musanta mata ko yace wani abu,saita miqe a hankali tana jin kamar qafafunta ba zasu dauketa ba ta doshi dakin. Ta kusa sakkani talatin riqe da handle din ta kasa murzawa,har sai da muryar farouq dake bayanta ta dawo da ita daidai "Are you okay?" Ya tambayeta yana leqen fuskarta. Kai ta gyada masa. "Ko na bude miki?" Ya sake tambaya cikin kulawa saita girgixa kanta ta kuma tattara gaba daya qarfin daya rage mata ta murda qofar tana shiga. Jijiyoyin jikinta ne taji tamkar suna tsinkewa,numfashinta kamar an musanya mata da wani abun daban me tauri bawai lallausan iskar da kowanne me rai yake shaqa ba. Ta dinga ganin idanunta kaman gizo suke mata,ba ainihin abinda zata gani bane take gani......gani take zolayarta kawai idanun nata sukeyi saboda abinda take kwana ta tashi da fatarsa kenan.....abinda take kwana ta tashi tana mafarki da burin ya kasance kenan. Yana zaune saman gadon da aka tallafo bayansa aka dago kan gadon sosai yadda zaiji dadin zama. Jikinsa sanye da rigar asibitin ruwan sararin samaniya me haske sosai. Lallausan blanket ne lullube da qafafunsa zuwa qugunsa. Fararen idanunsa tarr bisa fuskarta,idanun da suka dan rusuna kamar wanda bacci yake cike a idanun nasa. Kallon kallo ya wanzu a tsakaninsu,zukatan kowannensu yana bugawa da sauri da wani irin doki da zumudin ganin daya bangaren zuciyar tasa. Wasu irin abubuwa ya dinga sakar mata suna ratsa sassan jikinta......wani irin shauqi mahaukaciyar soyayya da zazzafar qauna ke kurdawa ta kowanne lungu na zuciyarta. Kewarsa me matuqar qarfi ta taso ta lullube zuciyarta ta sakata jin wani rauni na mamayarta,take idanunta suka cika da hawayen da bata da ikon tsaidasu. Hannunsa daya ya miqa mata yana ware mata su alamun marabtarta yakeyi,cikin wani irin zaquwa da dokin isowarta gareshi,batayi wata wata ba ta soma takawa da sassarfa zuwa inda yake tana jin kaman lokacin isarta inda yake ma ya mata yawa.....inama zaiyiwu ta zama walqiya cikin qiftawar idanu ta samu isa gareshi. Jikinsa ta fada gaba daya kuka yana qwace mata,tsam ya riqeta cikin jikin nasa yana mata kyakkyawan masauki zuciyarsa na tsananta bugu cike da wani bahagon so,idanunsa suka dinga lumshewa da kansu,dumin jikinta yana ratsa qashinsa bargo harda jinin dake harbawa kowanne sashe na jikinta. Hannunsa daya ya sanya ya riqo fuskarta,idanunta yake son kallo,qwayoyin idanun nan nata da yayi matuqar kewa yakeson gani. Bata hanashi ba,ta daga oily eyes dinta masu sheqi da suka jiqe da hawaye tana kallonsa. Nutsewa idanunsu sukayi cikin na juna,wani irin feeling ke ratsa kowannensu wanda yafi qarfin baki ya bayyanashi. Wani deep connection ya qullu a tsakaninsu,magana ce tsakanin zuciya da zuciya kawai wadda tafi qarfin baki ya bayyanata. Idan ya motsa labbansa sai yaji sun masa nauyi.....sai yaji kaman sunyi kadan su isar da saqon da zuciyarsa keson fadi
Chapter 147 · 0% Book details