Sashe 115
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
bane?. Murmushi kadan ya saki,ya karanci me take daukewa kan sarai,sai ya fara takawa zuwa inda ta maida kan nata,ya saka hannu yana zuge duka curtain din da suka zama hijabi ga idanuwa,suka lullube gilasan suka hana mata kallon ruwan dake gabanta din. Maida idonta tayi ta lumshe,da alama dai taci alwashin ba zata kalleshi din ba. Kai ya jinjina,shi kadai yasan me yake saqawa a zuciyarsa......da sannu zai saita komai kan tsarin da yakeso,a nutse yabi kowanne curtain ya zugeshi,sannan ya dauki bath set dinsa ya soma dosan toilet. Kadan ta bude idanunta taga yana tafiya bandakin,tasan kuma indai ya shiga ita daya zai bari sai ruwan nan dake kada hankalinta. Zumbur ta miqe da gudu gudu ta rufa masa baya,sai ya tsaya ya waiwayo yana kallonta sanda ya sanya qafarsa a qofar toilet din. Yadda ya zuba mata idanu ya sanyata yin qasa da kanta,tasan yana neman ba'asin biyoshin da tayin,tana wasa da farcenta tace. "Tsoro nakeji" A shagwabe har batasan sanda sautin tattausar muryarta ya koma haka ba. Wani numfashi ya zuqa me zurfi yana dubanta,yana bala'in son shagwaba fiye da yadda kowa zai fahimta.......saidai ba wanda yasan da wannan dabi'ar tasa saishi kadai,don ya sanya a ransa ba shagwabar da zata burgeshi saita matarsa. Yana cikin jinsin mazan da shagwaba ke tafiya dasu,yasa hannunsa yana shafan qirjinsa dake cike da gargasa muryarsa a maqoshi yace. "Ba wani abu fa.....kina cikin aminci,na miki alqawari daga yanzu har qarshen numfashinmu.....ba iya nan kawai ba.....a dukka fadin rayuwarki ba wani abu daya isa ya sake cutar dake muddin fu'ad yana raye". Idanu ta ware tana kallon qasan curtain din,ruwan yadan kada alamun wucewar kifi. Tanason kallonsa ta tabbatar masa da tsoronta amma kuma batason kallon muscles dinnan nasa. "Still tsoron dai?" Ya tambayeta yana dage mata gira,saita daga masa kanta. "Okay.....yanzu to ya zamuyi?" Ya tambayeta yana zube mata idanunsa. Satar kallonsa tayi kadan sannan ta dauke kanta,itama bata sani ba......batasan ya zasuyi ba,kawai dai abinda ta sani ba zata yarda ta zauna ita kadai ba. Kaman yasan abinda take saqawa yace mata. "Zaki shigo ciki ki jirani na gama wankan?" Ya mata tayi yana da tabbacin ba zatayi accepting ba. Waro idanu tayi tana kallonsa kai tsaye tana mantawa da batason ganin qirar jikinsa ma. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 100 100