← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 215

Sashe 151

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Wani zazzafan mari ya saukewa fuskarta,yana dubanta da wani mahaukacin fushi da bata taba gani kan fuskarsa ba
"How dare you zaki hari mutum kaman muhammad jadda?,have you lost your mind?" Ya qarashe maganar jijiyoyin kansa suna tashi,yana jin kaman zaiyi qaramin hauka.
Da zallar mamaki ta dora hannunta saman fuskarta tana duban mahaifin nata,karo na farko daya taba dora yatsunsa biyar saman fuskarta kenan da sunan mari bada sunan soyayya da lallabawa ba,wani abu da bai taba shiga tarihin rayuwarta ba sai yau.....yau ita mahaifinta ya daka saboda fu'ad?.
"Abba?.....maman naka ka daka saboda wani?" Ta tambayeshi tana nuna qirjinta da yatsanta cikin jinta cikin zallar tozarci dumu dumu
"Wani?,wani fa kika ce?,shi wannan din da kike kira wani kinsan wayeshi?,nace kinsan wayeshi?,kinsan rufin asirin da ya yiwa.mahaifinki?,kinsan cewa banda shi da baki isa ki tsaya a inda kike tsaye ba a yanzu?,kinsan waye boss na mahaifinki?,to MUHAMMAD FU'AD JADDA NE!". Shock taji sosai irin wanda bata taba ji ba,ta cire hannunta daga kan fuskarta tana dubansa idanunta dukka a warwaje.
"Kinsan tsakanina da talauci a yanzu takun taqi kadanne zan afka cikinsa!......kinsan anyi freezing duk wani account nawa....anyi banning all my properties?,duba nan...." Ya fada a hargitse yana cilla mata wata takarda.
"Takardar sanya hannu ne na dukkanin wanda keda ruwa da tsaki na saukeni daga muqamina.....duk a silarki fareeda!!!,ki gayamin meye ya rage mana yanzu?!" Ya tambayeta a tsawace yana watsa mata jajayen idanunsa.
Wani irin tashin hankali taji yana sauko mata,kalar tashin hankalin da bata taba jin makamancinsa ba,ta koma da baya ta zauna tana jin ta fara gani.bibbiyu.
Anyi banning duka properties na abbanta,harda motarta suturunta,gidansu da suke taqama da alfahari dashi.....anyi freezing accounts dinsa yana nufin harda nata daukacin accounts din......an sallameshi daga muqaminsa yana nufin daga yanzu an cire mata tittle na diyar AMBASSADOR KHALED MUSTAPHA?".
"This is insane.....unbelievable" Ta fada tana girgiza kai da qarfi don kwanyarta ba zata iya daukan wadannan abubuwan duka lokaci guda ba.
"Ba zaki gane insane bane sai lokacin da arrest warrant ya iso cikin gidannan da zummar kamaki a mazaunin masheqiya.....don tabbas!.....ina me Tabbatar miki jadda baya shurun banza......all these yayi ne tauna tsakuwa kawai don aya taji tsoro.....ina me Tabbatar miki bazai raga miki ba......kinyi yunqurin yin kisan kai......kuma bazan goya miki baya ko na hana a hukuntaki ba". Kowanne halitta na cikinta sai data kada tsananin tsoro
"Dad......na dauka ko meye na dauko kai me tsayamin ne?,abba yau da kanka kake wannan maganar?". Wani banzan kallo ya watsa mata,ya matso gabanta yana dubanta sosai.
" Ki taba kowa....ki tsokano kowa amma banda muhammad jadda.....mayunwacin zaki ne......damisar da tafi qarfin wasa......fareeda!!!!!.....wai mema kika sha?,still kina shaye shayenki da alama har yanzu ko?,magana ake miki na talauci yana bakin qofa yana qwanqwasa mana qofa fa!" Ya sake fada a gigice kuka na dab da qwace masa.
"I can't take it......bazan iya jura ba......rasaki da hukuncin duk da jadda zai dauka a kanki yafimin sauqi akan rasa dukiyata". Sai ya jawo wayarsa yana lalubar number muhammad jadda yana fatan samunsa ya nemawa kansa gafara da sassauci.
Zata iya cewa kaf tsahon rayuwarta bata taba jin wani abu daya gigita hankalinta irin wannan maganar ba,duban dad din nata takeyi ta koma kaman gunki,kowanne sashe na zuciyarta ya cika da tsoro da nadama da tashin hankali,ta yaya zata tunkari wannan babbar musibar dake tunkarota?.
Chapter 151 · 0% Book details