← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 167 OF 215

Sashe 167

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sake juya rubutaccen katin da yake hannunta tayi wanda akayi da zallar ruwan gold tana bin kowanne ado na jiki da kallo. Ko ba'a gaya mata ba ta sani gold ne zube a jikin katin daurin aure takarda maras daraja,ballantana zance yanata yawo anata yamadidin bikin a lungu da saqo na qasar nigeria,tsakanin maiduguri da kano kuwa dumin bikin ake ba'a cewa komai. Umar Farouq hamza kibiya zai auri fannah maisharif babaghana .
Sake buda katin tayi tana duba schedules din,duka a maiduguri ne za'a yi komai,shima abu qwaya biyu ne rakkin sai daurin aure rana ta uku,kamu da za'a hada da zaman ajo,sai bridal shower sai daurin aure,amma ita kanta tasan ace ma ba za'ayi ta'adin dukiya ba qarya ne.
"Ranar juma'a kenan fannah zata shigo ahalin hamza da ameenatu?" Ta furta ta daga kai tana duban wanda ke tsaye a kanta. Kai ya jinjina mata
"Tabbas" Ya bata tabbaci ta cikin baqaqen gilashinsa. Wani shu'umin murmushi ta aje tana ajiye katin.
"Na samu labarin kai tsaye zasu wuce da ita gidanta.....sai washegari da ameenatu zata gudanar musu da walima haka ne?". Kai ya sake gyada mata don bata tabbaci.
Wannan karon qaramar dariya ta saki.
"Hakan nima yayimin.....amma kuma dan jahannama.......bazan iya jiran washegarin ba......inaso ranar juma'ar ta zama rana mafi muni da qunci a wajensu.....inaso ranar ta juye musu daga farinciki zuwa baqinciki......inaso ta zame musu ranar tonon sililin baqincikinsu". Kai ya jinjina yanajin hannunsa yana masa qaiqayi.
"Baki da damuwa......zamu ajiye musu tarihin da zai zame musu abun lissafi da irga har qarshen kafuwar zuri'ar"
"Da kyau" Ta fadi tana cire sarqar gold din dake wuyanta. Sarqa me tsananin kyau tsada da daraja.
"A auna maka ka saida.....ko nawa ta kama kudin naka ne......bayan kudaden da zaku cajesu". Wata irin dariyar jin dadi ta qwace masa bayan ya karbi sarqar,ko a hannunsa kawai nauyinta ya isa ya bashi amsar kudade ne masu nauyi akan sarqar,baiyi wani mamaki ba ya juya ya fice yana jin dadin yadda zai rabauta da riba biyu.
_uhmmmmm,zamu gani,waye zai rabauta?,waye zai fadi?,waye zaiyi farinciki waye kuma zai shiga sasarin baqinciki?_
_Abinda ake gudu fa yana dab da faruwa.....abin boye fa yana dab da fitowa fili_
*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
_Zafafabiyar_
139
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
*_WEDDING VIBES_*
*_KANO & MAIDUGURI_*
Idan aka ambaci umar farouq kibiya,wani mutum ne me wasu irin halaye nagartattu,iya mu'amala da mutane da kuma Tarin abokai,duk da kusan kowanne aboki da zai shigo rayuwarsa yana qoqarin tantance cancantar wanzuwarka a rayuwarsa.
Bikin ya karade kafofin sadarwa masu yawa,ya kuma shiga jerin sahun bukunkunan da kowa yayi amanna zai bada wani irin salo me qayatarwa,duk da ba wani abu me yawa aka tsara za'ayi ba.
Tun lahadi ya yiwa maiduguri tsinke ta jirgin jadda wings,yayin da ya saukewa fuad saboda yanayin hannunsa. Su ahsan da sauran abokansu sune suka zame masa groomsmen.
Duka komai dasa hannun fuad aka kammalashi da wani irin dattako da nuna tsantsar 'yan uwantaka,sunyi fuad din zai taho ranar zaman ajo sai kuma da farouq ya sanya ya masa alqawarin zaije har gurin,saboda yasan halinsa,tun asali dama shi bameson ire iren wadannan abubuwan bane.
A nutse suke takowa zuwa farfajiyan da motocin da zasu masa rakiya zuwa airport daga can su zarce Maiduguri. Hannunsa sarqafe cikin nata,kwana biyu din da zaiyi sai yake jin kamar wanda zaiyi shekara biyu ne. Ita kanta duk sai takejin kamar ta sake masa kuka,kewarsa takeji tun bai tafi ya barta ba,duk da takan ji dama dama idan ta tuna in ya tafin itama zata wuce gidan anni don shirye shiryen biki,wanda idan an dauko fannah an kawota nan din,walima za'ayi gagaruma guda daya da anni ta shirya,zasuyi yini randa za'a sauka da fannah,walimar kuma washegari ce,to amma ita din a yanzun ta zama kamar auntyn amaren gaba daya da angwayen. Tuna su huda na tare da itan yana rage mata wani kadaicin,duk kuwa da cewa ba wanda ya isa ya cike wannan gurbin nasa.
Baiko kulaa ko damu da mutane a wajen ba,ya ajiye mata tattausan kiss a goshinta bayan duka sallamar da akayi a ciki.
"Saina dawo?,ki kulamin da kanki sosai,if possible ki dawo gida ki kwana,banaso na tuna cewa baki dakinki kinji please" Kai kawai ta iya gyada masa,don idan tace zatayi magana kuka ne zai qwace mata.
Har ya fara takawa zuwa motar da Jordan ya bude masa ta jawo yatunsa,ya dawo da baya yana kallonta da narkakkun idanunsa.
"Yadai?.....ko na fasa ne?" Kai ta maqale sannan ta girgizashi.
"BB ne fa......idan banda BB dinne ba wanda zan bawa aronka....."
"Nima banda ina kishin a kallemin ke.....banda ina tattalin 'ya'yana ba abinda zai sanya na tafi na barki"
"To amma...." Ta fada tana turo baki ba tare data qarasa magana ba. Idonsa ya lumshe ya kuma budesu yana kallonta,ya mata alama daka akan ta fada.
"Banason ka kalli kowacce mace please...." Tayi maganan tana juya masa baya alamun kunyarsa takeji. Qaramar dariya ya qwace masa,yasa hannu.ya juyo da ita yana fadin.
"Say it mana.....Louder please!,with all your might" Ya furta yana mata sassauqar runguma ta baya,yadda ta nuna kishin na faranta masa kaman farincikin na neman masa yawa.
Kai tsaye ta juyo ganin abun na masa dadi,ta saka idonta cikin nasan tana dubansa.
"Your eyes belong to me,don't look at any other women please,na maka alqawari a karan kaina.....my gaze is fixed on you alone,bana ganin kowai sai jadda na" Ta fada tana rungume Hannayensa". Sulalewa yayi sai gashi saman gwiwarsa a gabanta,abinda ya sanyata zaro ido ta fara kallon mutanen dake wajen.
Dukka guards nashi sun juya bayansu,ba wani guda daya da yake kallonsu,saima kaman katanga da sukayi musu ta yadda ba wani a farfajiyan gidan da zai ganin ainihin abinda ke faruwa.
"Karki damu,My men are extremely competent" Yana kaiwa nan ya kamo yatsuntsa masu kyau da taushi. Kafin yace komai wayarsa ta dauki tsuwwa,yadan yamutsa fuska yana cirota a aljihunsa. CP ahmad nuhu ne,don haka ya daga kai tsaye ya sanya a kunnensa.
Cikin ban girma suka gaisa,kafin ya soma gabatar masa da bayanai.
"Sir dukkaninsu a yanzu sunyi taushin da kowanne bayanai muke buqatar tatsa daga wajensu zamu sameshi in sha Allah,don yanzu haka bibo da zuwaira ma mun samu dukkanin bayanan da muke da buqata,ban sani ba ko zamu iya aike maka ta email?"
"Good job sir.....thank you,basai ka turo ba,don yanzu haka mun fara hidimar bikin dan uwana.....but zuwa Monday dukka zamu zauna dasu,akwai yiwuwar wanda za'a sallama a cikinsu.....thank you sir"
"Okay sir.....in sha Allah" Cp din ya fada suna sallama cikin farinciki da mutuntawar yadda dukiyar FU'AD din bata sanya yana musu kallon na qasa dashi ba. Ya basu dukkan wani girmamawa da dama na gudanar da ayyukansu.
Kashe wayar yayi duka ya sanya a aljihu don kada wani ya katse masa shauqinsa,sannna ya sake riqo tausasan tafin hannunta da har yanzu yake jiyo wannan sassanyan qamshin na jiya (incense by kabo daughter+234 803 211 9803 Da gaske turarenta kwana yake a jiki,kama gida kuma da wuri yake,khumrorinta dukka na dabanne bare akai ga turarenta).
"Ni muhammad FU'AD jadda,an halicci ruhi Zuciyata dama gangar jikina gaba daya saboda ameenatu sabreen........har abada gangar jikina da zuciyata sun haramta ga wata diya mace ba ita ba......mata gaba dayansu wallahi wallahi kallon maza nake musu 'yan uwana,daga kanki an gama haifar wata diya mace har abada,amana daya ce......kuma kin sameta,bana canza magana,bana sauya alqawari" . Tasha jin ana cewa maza basu da magana daya.....ta gani da idanunta yadda maza suke zama wasu ababen tsoro game da mata,amma a yanzun saita samu kanta da amanna da maganganunsa.
Tana tsaye har dukka motocinsu suka bar harabar gidan,sai ta juya ta koma a hankali tana jin kaman ita kadai ce ta rage a duniya. Bata dauki lokaci ba itama sai kawai ta shirya,ta yiwa securities din daya bar mata magana suka shirya motoci ta fice zuwa gidan anni.
Ta samu amare sunata wani glowing kaman wadanda anni ta dauka ta jefa cikin engine aka sauyo mata da wasu,duk da dama daga amna har huda kyan fata garesu.
"Aah,mrs saddiq and musaddiq" Sabreen ta fada cikin salon tsokana. Abun mamaki wai yau ita suke kunya,kowacce sai ta sadda kai,saidai kuma yanayin amna data gani kaman ba yadda ta saba ganinta ba.
Duk da akwai surukuta sosai tsakaninta da anni,amma ta dan sake wasu abubuwan da ba zasu zamto zaqewa ba ta shiga anyi da ita. Lefen data gani wajen anni akwati ashirin da hudu na huda ashirin da hudu na amna,guda biyu arba'in da takwas kenan. Daki daban anni ta saka ta shiga tana nuna mata wasu designers akwatunan guda sha biyu samfurin shekara mai zuwa,wanda akayi lunching nasu a dubai cikin satinnan. Ita tsoro ne ma ya kamata da anni take gaya mata wai nata ne,ya ilahi ina zatakai wadannan?,kada ya jawo mata baki fa na jama'a.
A daren suna video call take jeranta masa kalaman godiya,kalaman da suka sake kashe masa jiki da zuciyarsa,yaji kaman zai narke saman sofa din da yake kwance akai.
"Sabrrrr" Ya kirayeta,wanda kiran kawai ya gaya mata yanayin da yake ciki.
"Anya ba gobe zan taho ba?,anya duniyata?". Dariya ta qyalqyale masa dashi tana tsokanarsa.
"So kake BB da fannah suce nice na hanaka?,kayi haquri please,awa arba'in da takwas ne kawai".
"Allah ka bani juriya" Ya fada yan lumshe ido,yana jin wata kewarta tako ina,tattausan skin dinta me qamshi laushi da santsi.
Chapter 167 · 0% Book details