← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 190 OF 215

Sashe 190

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"laila" Hajja harira ta sake kiranta karo na biyu. Daga kai lailan tayi wadda ke zaune qasan carpet din dakin ta kalli mahaifiyar tata.
"Na'am hajja" Ta fadi dukkanin wani lungu da saqo na zuciyarta dama gangar jikinta suna azalzalarta,tana jin kaman wuta ake hurawa sassan jikinta dama zuciyarta.
"Wacece ni?"
"Mamana ce" Ta amsa mata Kai tsaye idanuwanta kafe a kanta.
"Alhamdulillah" Hajja ta fadi tana sakin murmushi. Cikin zuciyarta cike fal da godiya ga bokan da yayi mata aikin farraqu tsakanin maamah da laila,ya gaya mata cewa wannan din qaramin aiki ne da zai iya aiwatarwa,ya mata alqawarin sai yazo duk duniya ba wanda laila taqi jini taji koda sunansa sama da hajiya mariya.
"Zaki koma wajen maamah mariya?" Hajja ta gwada tambayar laila. Shuru ta danyi na wasu sakanni,sai kuma ta girgiza kanta da qarfi.
"Bana so,bazan koma ba,ina wurin hajja na". Ta fadi bawai don tana nufin abinda ta fada din bane da gaske har zuciyarta.
Da dariya ta qyalqyale sosai,farinciki yana cikata,lallai laila dinta ta dawo,ta dawo hayyacinta.
" Na godewa Allah daya dawomin dake hayyacinki laila" Murmushin qarfin hali ta sakarwa hajjan,tanason ta sake bata tabbaci da yaqinin ta warke don ta ware mata takunkumin hana fita da sanya masu gadi su hanata fita ko nan da can. Ba abinda takeso irin taje wajen maamah,ta duqufa tayi ta mata bauta iyakar qarfinta.
"Na warke hajja in sha Allahu,kawai zaman cikin gidan nan ne hajja na gaji.....ko cikin layinnan kya barni na tattaka da qafafuna ko?" Ta fada a shagwabe kaman yadda take mata a baya.
Fuska hajja tadan bata tana dubanta.
"Aah......ba yanzu ba laila,matar nan makira ce,duk da ance tana can tana jinya amma ba Allah a ranta,kina kallon yadda take kidnapping 'ya'yan jama'a fa?" Hajja ta fadi tana nunawa laila girman ta'addancin maamah.
Wani irin tashin hankali da kuma bacin rai ne suka bijirowa lailan,ta tabbatar yau ko gobe Hajja ba zata barta ta fita ba bare ta koma wajen maamah,kenan ba amfanin rayuwarta ba tare da maamah ba?". Ta yiwa kanta wannan tambayar.
A take taji indai za'a yanke alaqarta da maamah bata da wani amfanin rayuwa,don haka ta miqe tsam.
"Bari naje kitchen nasha ruwa"
"Ki tahomin dashi" Ta fada hankalinta kwance don tasan a kitchen din dai ba wata hanyar fita daga sassan ma bare akai ga gidan.
Idanu kawai take warawa sanda ta shiga kitchen din,gaba daya kwanyarta a birkice take,neman abinda zatayi amfani dashi kawai take yi idanunta suka sauka kan gas.
Da sauri ta qarasa wajen,ta saka hannu ta kunna dukka makunnansa guda hudun da yake dasu. Fita ya fara yi sosai,kafin kace meye wannan warinsa ya mamaye kowanne sashe na part din hajjan.
Hancinta sosai hajja ta dinga budewa tanason tabbatarwa warin gas dinne?. Da wani irin sauri ta duro daga saman gadon tayi kitchen da mugun sauri. Duka masu aikinta ba kowa yau ballantana tayi tunanin wani ne a cikinsu,laila kawai tasan ta shiga kitchen din.
Cak ta tsaya daga bakin qofar falon,qafafuwanta suna rawa zuciyarta na wani irin gudu mara fasali. Laila ce tsaye a kitchen din riqe da lighter,idanuwanta fes kan hajja dake tsaye daga can bakin qofar kitchen din.
"Laila.....laila baki da hankali ne!!!" Hajja ta fadi a birkice ganin lailan tana qoqarin motsa yar robar data tare bakin lighter din wadda ita zata bata damar tashi. Wani kalar murmushi ta saki tana duban hajjan
"Kina tunanin zan iya rayuwa ba tare da umarnin maamah ba?,ko kina tunanin zan iya rayuwa a inda babu ita?.....sai watarana hajja" Laila ta fada cikin qwarin gwiwa.
A gigice hajja ta bude baki tana son gaya mata cewa.
"Kada ki kunna laila.....indai mariya c na bar mata ke har abada,ki hada kayanki ki koma gareta" Saidai dukka wadannan kalaman basu samu damar fita daga bakinta ba sai hucin tsananin atsabar zafin wuta da qarar bindigar fashewar tukunyar gas din da suka cakude waje daya aka wullota waje,wanda daga nan bata sake sanin abinda yake faruwa ba.
Qarar fashewar taja hankalin sassan matan 'ya'yanta da masu gadi dake waje,kafin balbalin wutar ya tashi hankalin kowa suka nufo sashen hajja din.
Duk saurinsu turus kowa yayi,saboda wata irin muraddiyar wuta ce me azabar duhu da Zafar tana harshe ke cin kowanne sashe na hajja din. Babban sashe da yafi na kowa cikin gidan girma kyau da tsaruwa,sashen da idan ka kalleshi ka kalli na matan 'ya'yanta saika dauka su din duka sashen ma'aikatan gidanne wato boys quarters,duk kuwa da cewa mudin na mazajensu ne,dasu akayi wahalar nema da kuma samu.
Tashin hankalinsu waye da waye a ciki?,suna tsaka da son tantancewa sukaci karo da hajja yashe a qasa,wadda babban jikanta ne kawai ya iya gane itace,saboda shi dinma ya shiga dazu kai mata wankinta ya gane atamfar jikinta,fuskarta kaf da kafadunta zuwa qirjinta sun koma jazur kaman an shafeta da jar hoda saboda yadda wutar ta kwaye asalin fatarta.
"Na shiga uku......wayyo Allah na..... Wayyo laila......laila kada ki mutu ki barni......laila bansan kanki abunnan zai koma ba,wallahi laila bake nace a bawa kici ba......laila don Allah ki fito laila......naci buri a kanki,na shiga uku" Sune maganganun data dinga fada tana ihu tana kururuwa gami da zabura,azabar zuciya dana gangar jiki duka sun isheta aka wuce da ita asibiti cikin ambulance bayan anyi kiran fire service suzo su tsaida watar kada ta soma lasar sassan gidan.
Abun kamar film kamar almara,ana fita da hajjan sanda wutar ta cinye sassan sarai,surukanta dukka dake tsaye a wajen sai kowacce ta dafe kanta.
"Wayyo Allahna.....wash Allah na.... Wayyo kaina" Shine abinda suka fara fadi a jejjere,kafin kace meye wannan sai gasu duka su ukun a zube warwas a qasa sun sume.
Akwai wani malamin makarantar almajirai dake a wajen,kallo daya yayi musu yace basai an kaisu asibiti ba,babban falon gidan yasa aka ajiyesu,ya karbi ruwa yayi musu tofi sosai ya bawa mazajensu yace a yayyafa musu idan sun farka a bawa kowacce tasha.
Cikin qasa da minti biyar sai gasu a zaune,kowaccensu kuka takeyi wiwiwi
"Wallahi saika sakeni......wallahi bazan sake zaman bauta ba..... Idan ta dawo kuma me ya rage mata?,inajin sujjada zata saka mu koma yi mata" Shine abinda matan kowacce ke gayawa mijinta cikin kuka. Duka falon sai ya rikice,ga gobara a waje ga tashin hankali a cikin gidan,su kansu mazan a rude suke,don sam duka abinda matan ke iqirari akai ba wanda yasan anyi a ciki.
Gyaran murya malamin yayi ya kuma nemi su bashi hankulansu. Bayani ya musu me ratsa jiki game da lamarin,kusan abune da kaf unguwar ake magana akai yadda take bautar da uban kowa cikin gidan,kusan duk me hankali yasan aikin sihiri ne.
"Indai har zaku yarda da shawarata ku yafewa mazanku,ku sake sabon zama dasu don ba cikin hayyacinku dukka kuke ba,wataqila wannan gobarar ta qone duk wani binne binne ne shi yasa komai ya warware kansa.....sai ku bita da addu'a Allah ya bata lafiya ya sake fahimtar da ita ainihin rayuwa.....". Da wannan bayanin nasa ya kashe wannan qurar,hankula kuma suka koma kan wutar dake ci wadda an fara samun daman kasheta.
Chapter 190 · 0% Book details