← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 215

Sashe 143

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Matsawa anni tayi da hanzari tana kiran security emergency line cikin qasa da minti daya sai gasu sun bayyana a dakin. Kiran security din ya tayar da kusan duk wani security alert na asibitin,kasancewar dakin babban daki ne,yana cikin VIP rooms da asibitin yake dasu. Cikin qanqanin lokaci qofar dakin ya cika da security da wadanda ihun security alert din ya tashesu. Kusan kowa yasan wacece a dakin a cikinsu,suna da masaniyar mahaifiyar wace a dakin,don haka fitar security alert daga dakin ya zamana kaman tashin hankali a wajen kowa. Sanda chief of security service na asibitin ya shigo dakin yana neman ba'asin abinda ya faru ya girgiza. Cikin matuqar tsoro da kuma kaduwa ya shiga bawa anni haquri. "Am sorry maaa.....muna dukkan iyawarmu wajen bawa madam tsaro,bamusan ya haka ta faru ba.....amma ni da kaina banyi minti talatin da shiga office ba bayan ba gama zagaye na tabbatar kowa yana kan aikinsa,hatta shige da fice na asibitin nan tun bayan faruwan abun muka sake saka ido akai....amma zamu duba in sha Allah,zamu kuma binciketa har sai mun tabbatar daga ina take?,meye kuma ya shigo da ita dakin......muna masu bada haquri". Kai kawai anni ke jinjinawa tana duban matar wadda tuni ta jiqe da fitsari,ainihin mummunar suffarta dukka ta fito saboda yadda tayi wurjanjan da kuka da tsananin tashin hankali. Haquri kawai take bayarwa hannuwanta a sama kaman me addu'a. A haka suka jata suka fice da ita,sabreen ta koma gefan gadonta ta zauna kawai rungume da hannayenta kanta yana cakudewa. Dr mubeena ta qaraso inda allurar da robar suka fadi ta sanya hand gloves ta daukesu,har yanxu ita kanta a tsorace take jikinta kuma rawa yake. Mamaki ne yake qara kasheta na yadda akayi amfani da kamanninta da komai nata aka shigo dakin za'a cutar da iyalin jadda. "Zanje dashi lab mu gwada muga meye ma taso zuba mata cikin drip din". Dr mubeena ta fada tana duban securities din guda biyu da suka rage a dakin. Juyawa tayi ta kalli anni da sabreen. "Ku kwantar da hankalinku,babu abinda zai faru in sha Allah,zasu dan xauna kadan daku kafin daga waje kafin security dinku na gida su iso....don anyi alerting nasu abinda yake faruwa". "Sannu Dr" Kawai anni ta iya fadi Dr mubeena ta juya ta fice da sauri Dr kamal da yake on duty yabi bayanta abun shima yana girgizashi. Case ne da makamancinsa bai taba faruwa cikin asibitin ba,sai gashi yau yana shirin faruwa akan matar mutum mafi girma da kima cikin idanunsu banda Allah ya kiyaye. Ajiyar zuciya me nauyi sabreen ta sauke tana dora hannunta saman cikinta a hankali. Wat qqqarfar soyayyar abinda take dauke dashi ya ratsa mata zuciya irin wadda bata taba ji ba,wato tako ta ina farautar rayuwarsu akeyi?,so ake a salwantar dasu gaba daya?,kowa rayuwarsu ta tsone masa idanu ta kowacce fuska?. "Nayi alqawarin baku kulawa da dukkanin qarfina da kuma iyawata.....nayi alqawarin kula daku har zuwa sanda zaku taka doron qasa......da ran mahaifinku ko babu.....da kulawarsa ko babu......zamu zame masa madubi kuma ababen alfahari in sha Allah" Tayi maganar ita daya tana sakejin kaman wata sabuwar alaqa na qulluwa tsakaninta da abinda ke cikinta da batasan meyeshi ba. Batasan hawaye takeyi ba saida muryar anni ta ratsata. "Ki rage damuwa da gaske sabreen ko don diyoyin cikin ki.....karki cutar dasu....Allah shike riqe da kowanne bawa yake bashi kariya....musamman idan ka sallama masa ka kuma miqa masa al'amarinka". Tayi maganar a tausashe tana goge mata damshin fuskarta. Ba wanda ya iy komawa bacci,abinda ya sanyata yanke shawarar yin alwala,ta daura alwalar ma'u ta shimfida mata abun sallah. Ta jima tana kaiwa Allah kokenta wanda tayi Imani shine sarki guda daya da baya maida hannun bawansa ba tare da ya amsa addu'arsa ba. Sanda ta idar tana zaune kanta a qasa,tana jin tattaunawar guards din fuad daga parlor din dakin. Kusan kowannensu zuciyarsa a kusa take,muryar abdulgafar ce ta qarshe. "Daga yau koda wasa ba wanda zai sake gigin zuwa kusa da inda take ma......daga gobe zuwa jibi ko da numfashinmu da jinin jikinmu zai qare sai mun lalubo duk inda oga yake,a cikin qasar nan ko africa ko a wacce nahiya ta duniya ma". Numfashi ta sauke a hankali,ta jawo wayarta tana lalubo number musaddiq. Dole ta fara taba mata nutsuwa kaman yadda tayi musu,dole ta taba kwanciyar hankalinta ko yaya ne,saboda itama tasan kifi na ganinka me jar koma. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 123 Cikin qasa da awa daya ta gama turawa saddiq komai da komai da take buqata,sannan ta sauka tana lalubo rubutaccen qur'ani dake kan wayarta. Ko yaya ne tanaso ta karanta ko zata samu sassaucin zugi da radadin da zuciyarta take mata,don ta dade da fahimtar babu wani abu dake bawa jiki da zuciya nutsuwa irin karatun alqur'anin.
Chapter 143 · 0% Book details