← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 157 OF 215

Sashe 157

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 1 min read

qwarin daga murya ta kirashi,tana ma ganin kaman bata lokaci ne,sai kawai ta fito a toilet din da wani irin sauri. Kansa ya daga yana kallonta sanda ta fito din,sai shima ya ware idonsa yana dubanta kafin ya miqe da sauri ganin yanayinta. Sosai ya riqeta yana tambayarta "What's happening?.....relax.....gayamin" Pant dinta kawai ta daga masa,sai ya zare idanunsa waje kaman zasu fado. "Oh shit......subhanallah" Ya fadi yana jin gaba daya ya gama firgicewa. Cikin kula da takatsantsan ya maidata gadonsa ya kwantar da ita. "Lemme call a doctor" Ya fada yana fita a dakin da sauri don yana ganin tsaiwa kiransa ta landline ma bata lokaci ne. Su biyu suka shigo,shi da wata likitan mace daban,yanata masa magana akan hannunsa amma bata wannan yake ba. "Scan zamu fara yi mata don tabbatar da lafiyar babies din" Likitan ta fada tana qarasawa gaban gadon sabreen din. Maida dubansa likitan yayi a kansa. "Hannunka ya akayi yayi staining haka?" Ya tambayi fu'ad din wanda hankalinsa duka yake kan sabreen wadda dr din ta fara jawo na'urar scan wanda take a dakin permanently.
Chapter 157 · 0% Book details