← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 215

Sashe 83

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

W A S H E G A R I K'arfe hudu na yammaci dukkaninsu suna tsaye gaban motar suna qoqarin shiga,saidai gurin ya kaure da hayaniya wanda kusan qananun fada ne da musu tsakanin saddiq da amna wanda dukkaninsu bakinsu baya iya shuru. Tuni Jordan yayi zaune mazaunin driver yana jira su kammala shiga "Anni tayi warning na kaiwa dare......i think wancan hamman naku yakai qararku an fitar masa da mata har dare.....oya guys.....hurry up muje mu dawo" Ya fada yana dan buga seat din motar,abinda ya sanya musaddiq soma shiga yana cewa amna. "Yau zai gane qaramin talaka ne....... Don't argue with him.......shigo auta" Musaddiq ya shiga maganan don ya kawo qarshen fadan. Juyawa amnan tayi ta miqawa sabreen wani baqin kati da yafi kama da atm "Matar oga.....yau ina jakanki.......ga wannan anni tace na baki,naki kudin tsarabar ne da boss ya saka miki kiyi siyayya". Bin card din tayi da kallo,ita bata taba ganin card ma irinsa ba,to amma kuma ita me zatayi da kudinsa?. Ko fitarsu jiya ma ba wani abu ta siya ba,amma duk da haka saida farouq ya cikata da siyayyar da ko budewa ma batayi ba. Hannu tasa ta karba card din kawai,ta daga qafanta tana niyyar shiga motar sautin musaddiq ya sauka a kunnenta "Wow........kallemin guy dincan" Ya fada yana tabo sadiq "Tashin sense" Saddiq ya furta yana kallon fu'ad dake tahowa. Cikin wani irin taku me dan sassarfa,sanye yake da wasu lafiyayyun suspenders da suka sake bayyana ainihin zallar quruciyarsa,suka kuma sake kwashe shekarunsa suka boyesu tas......saika rantse da Allah shi din sa'ansu saddiq ne. Saman kansa homburg hat ce data fidda kyakkyawar fuskarsa da wani irin kwarjini da kwantacenn kyau da zai iya gaya maka lallai shi din ruwa biyu ne da ake kira da halfcast. Sosai kayan suka zauna masa a jikinsa,rigan na dan bayyana muscles din da jikinsa ke dashi,wannan kadai zai gaya maka qaqqarfa kuma ginannen jikin da yake dashi. "Gayennan yana wuta.....anya ba zamu koma ciki mu canza dressing ba......kada maldivians dinnan su dauka age mate dinmu ne fa" Musaddiq ya fada sounding seriously. Dariya sosai amna ta fashe dashi tana dora kanta kafadar saddiq "An gaya muku ya fu'ad wai sa'anku ne?,ku sallama kawai ku huta......idan kanajin babban kifi to shine.......kunga maza kun raina kanku ko?" Dungureta saddiq yayi yana janye jikinsa "Zakiyi dariya da kyau ai......abinda ya kamata ki fara tambaya ko ki damu dashi shine dalilin da yasa ya fito.....ku koma ciki ba zaku je ba,ko ya fito ne mu fita tare kinga yau shikenan......ba sauran sakewa" Tsit dukkansu sukayi,saboda sunsan halinsa zai aikata da gaske. Kowa ya dauke wuta a cikinsu suna fargabar hukuncinsa,har zuwa sanda ya qaraso. Da ido kawai ya yiwa Jordan inkiya ya fito daga mazaunin driver din,ya zagayo kujerar me zaman banza ta kusa da driver ya shiga yana cewa farouq "Shiga mu tafi". Da kallo farouq ya bishi,har ya shiga ya zauna,ya daga idanunsa masu cike da kwarjini ya kalleshi yana daga waje "Ko ba zaka tafi bane ka tsaya kana kallona?" Kai kawai farouq ya kada yana tunanin abinda ya sauya ma fu'ad ra'ayi ya aminta da karan kansa zai bisu. Yau fitar dadinta sai taji baikai na jiya ba tun akan hanya,duk hirarsu suna kiyayewa da hayaniya ko abinda zasu fadi. Hira suke da farouq a gaban mota duk da batajin me suke fada,a haka suka isa guri na farko. Sunyi yawo sosai cikin kasuwannin da suke da kayan gargajiya na al'adun qasar Maldives.....sunyi siyayya kaman ba gobe,duk da bata taba komai daga card din da amna ta bata ba,hasalima a cikin mota ta barshi cikin handbag dinta da bata fito da ita ba. Gurare da yawa idan sunje zamansa yake cikin mota,dama shi din bai damu da shiga gurare irin wadannan ba. Koda sunyi tafiya guraren da yakanje gurare ne da suke da alaqa da kasuwancinsa,ko tarihi na kasuwanci ko kuma zai amfani kasuwancinsa,shi yasa yau din suka cika sosai da mamakin ganin yabi bayansu,duk da dukkaninsu kowa ya ta'allaqa hakan da sabreen ce sila. Guri na qarshe da suka je,suna fitowa ya miqa hannu ya karba key na motar daga hannun jordan "Zaka iya komawa gida" Yace dashi kai tsaye. Takawa yayi a hankali ya isa gaban motar,hannunsa daya zube a aljihun wandonsa,yasa hannu ya bude motar ya shige seat din driver. Junansu suka kalla tsakanin saddiq da musaddiq da amna,mamaki ya cika kowa ganin yau hamma da kansa zaiyi driving?,wani abu da suka jima basu ga yayi ba "Zaku shigo mu tafi ko na wuce abuna?" Ya leqo kansa yana magana dasu da miskilar fuskar nan tasa. Har rige rigen shiga suka dinga yi kowa mamaki kwance qasan zuciyarsa. Kaman yadda kusan komai nasa ya banbamta dana kowa haka tuqinsa,driving yakeyi cikin wata irin qwarewa da nutsuwa,gudu baiyi yawa ba......haka babu laqai laqai. "Ina muka nufa ne sir?" Farouq daya kula ya sauya hanya ya tambayeshi yana kallon fuskarsa dake a dinke tsaf. Shi kwata kwata ma guraren da sukaje kaman basu bashi walwala ba ko kadan. "Siyar daku zanyi na qara jari" Ya amsa masa a taqaice yana sake maida dubansa sosai ga titin. Dariya sosai farouq ya saki yana relaxing jikin kujerar motar "Hakan yayi ai......dadin abun bamu kadai ka debo ba ai" Yayi maganar yana turo p_cap dinsa gaba. Sarai ya gane me yake nufi,shi kuwa bazai kulashi ba,saboda neman wajen da zai dan sake samun relief kawai yakeyi. Sannu a hankali suka shiga Vaadhoo island sunan dake rubuce baro baro a allon sanarwa. Ihu amna keson saki na murna amma sanin wanda ke driving bayason magana me tsauri ko hayaniya ya sanyata danne bakinta ta dole tana duban saddiq dake zaune opposite dinta. Gira ya daga mata alamun tambaya,saita nuna masa map na inda suke ta qaramin screen din dake maqale a gefansu. "Vaadhoo.......glowing island!......sea of stars" Ta fada da wani irin farinciki daya lullbeta don sai a sannan ta lura da sun qaraso glowing island din. "Addana.......mijinki is very incredible wollah.......kinyi dace......kin dace....he's very calm,ya iya surprise,komai nashi unique ne" Ta fada farinciki yana kamata,farincikin yau zata ga inda ruwa yake haske......yashi da qasar gurin itama ke haske tamkar an watsa taurari,wannan yana gaya musu qila ya musu booking na kwana a wannan sabuwar duniya,ko kuma zasu kai dare a wajen suka yadda komai yake gudana. Murmushi kawai tabi amna dashi......babu wani abun burgewa tattare da yayan nata......itace dai bata sani ba. Amma kuma sai itama ta samu kanta da fara sallamawa al'amarin sanda suka isa adhaaran prestige,ma'aikatan wajen kuma suka iso suna maraba dasu,da alama sunsan da zuwansu wajen. Da idanu kawai take bin gurin,da gasken gaske ta zama 'yar qauye tuburan. Gidaje ko dakuna zatace saman ruwa da wani irin tsari me jan hankali. Bata da sauran abunyi illa bayansu da tabi kaman yadda taga sunbi daya daga cikin ma'aikatan saman wani shimfidadden abu daya zama hanya kuma abu daya da zai hanaka tafiya saman ruwan. Kai tsaye zata iya kiransa hotel ko gidan saukan baqi. Suka miqawa kowannensu wani dan card da komai da komai,sai amna ta daga kai ta kalleta bayan ta gama dubawa. "Ga inda zamu zauna can.....zamuci abincin dare a nan.......zami fita sea of stars muyi kallo harmu shiga idan da yiwuwar haka.....komai mukeso zamuje mu karba......amma adda naso kwana zamuyi......inama hamma yace mu kwana?" Amna ta fada tana duban sabreen da hankalinta yake kan ruwan dake gaban door glass din. Shimfidadden ruwa ne iya ganinka wanda yake bada kalan sky blue,abun akwai mamaki yadda mutane keta harkokinsu Kai tsaye suna kai kawo kaman cikin gidajensu suke. "Muje dakinmu adda" Amna ta fada da doki tana yin gaba,bayan ta fidda wayarta ta fara daukan hotuna da videos. Bata yiwa kanta da kanta qoro ba,idanu ta bude sosai tana kallo,yanayin iska da tsarin wajen ya banbanta da duk wani guri data taba zuwa. Gaba daya hankalinta a tashe yake,kaman yadda tunaninta yake a jagule waje daya. Iya zunzurutun dollars din data kashe don tsara komai,tun daga zuwanta Maldives da zamanta a wajen ba wani abu bane na damuwa muddin buqata zata biya. Bahaushe yace ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba. Ya zuwa yanzu da take zaune gaban glass door din tunani ne fal zuciyarta,tana jin kamar tayi wauta da take zaune tana lissafin zai wahala fu'ad din ya tsallake wannan island din ba tare daya shigoshi ba. Tayi zurfi cikin tunanin daya cika mata kwanyarta taji sn daneta daga baya gami da maqaleta da kyau. "You didn't missed your target......you hit it!" Wanda ke maqale a bayanta ta fada da murya me qarfi. A zabure ta cire hannuwanta daga wuyanta gami da waiwayowa gareta,tana jin abun kaman mafarki,idanunta dukka a waje take dubanta "Ki gayan gaskiya.....bazan iya jurewa ba idan kikacemin qarya kike" "Wallahi wallahi me jadda ya shigo......but shi da familynshi ne duka,but kaman dakuna daban daban ne" "Thank god.......ki miqawa wannan Chinese boy din wannan abun.......banason kuskure......after 30minutes zan shiga dakin,ya saka cameran daidai yadda zai nuna komai.......ya tabbatar yayi diluting tablet din a ruwa da lemonsa". "Done!......breaking news zaya fita zuwa ga Nigeria" Ta fada tana barkewa da dariya,yayin da fareeda ta tayata da qaramar dariya mata sauti. Juyawa tayi ta fita,sai ita kuma ta soma zame kayan jikinta da gagggawa tana wucewa wata siririn hanya da zai kaita toilet. Cikin qasa da minti goma ta fito,ta kuma tsaya a side din dressing ta soma balle wasu turaruka tana shafe lungu da saqo na jikinta,ta ware gashin kanta da kyau ta jiqashi da sassanyan qamshin turare,sannan ta bude wani jaka ta zazzage kayan ciki tana dagasu kafin ta fara shirya kanta a cikinsu. Wasu gantalallun riga da wando ne,very skinny,ba iya jeans din ba,har rigar data sanya. Ba wani sirri boyayye ko bayyananne da Allah ya wadatata dashi da bai fito ba walau qashi ko tsoka,me tudu ko me kwari. "Wow......wow" Taji an fada daga bayanta. Kadan ta juya tana kallonta don batasan ta shigo ba. Hannu ta watsa mata tana tambayarta alamun yayi? "Perfect.......kome kamun kan mutum ya ganki sai ya fada......ga kuma wadancan abubuwan na aikinsu yadda ya dace.......zance zaisha banban nan da nan......fatan nasara" Ta fada tana daga mata babban yatsa. Wani shu'umin murmushi ta saki tana takawa gaban madubin,ta sake juyawa sosai a
Chapter 83 · 0% Book details