← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 174 OF 215

Sashe 174

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

dauke amna akayi intentionally.....wallahil azeem" Tana kaiwa nan saita rushe masa da kuka gaba daya. Rudewa yayi,gaba daya kukanta ya dauke masa nutsuwa. "Bamuyi haka dake ba sabreen.......karki cutarmin da yara please" Ya fadi yana hade hannayensa guri guda gami da sanya nata hannuwan cikin nasan "Me yasa zaka boyemin hamma?......sai idan ta mutu sannan zaka gayamin?,ina huda?" "She's safe" Ya bata tabbaci. Kai ta girgiza,sam hankalinta bai kwanta ba. "She's not safe tunda aka dauki amna.....nadra haneefa dukkansu suna cikin barazana" "Like how?" Ya fadi yana dubanta da tarin tambaya gami da zama sosai a gabanta sabanin tsugunnon dazu. Tambayarsa ta dawo da ita cikin hayyacinta. A hankali ta sassauta sautin kukan nata. Zato bai zama gaskiya ba.....zatonta kuma a yanzu baida hujja ko dalili sai qwqwaran zargi,tana gudun ta furta abinda idan yaje ya dawo zai zama ba gaskiya bane,da wanne ido zataci gaba da kallonsa?.. "Kina da wani masaniya ko hasashe ne?" Kai ta girgiza "Babu....but duk wanda ya shiga ya dauki amna....nadra dasu huda ba zasu gagareshi ba" "A tsukinnan indai ba aljani ba,banajin akwai wani dan adam daya isa ya keta tsaron da gidan yake dashi ya dauki amna.....ina kyautata zaton fita tayi.....zan binciki duk wani CCT footages na gida.....naci alwashin amna ba zata kwana uku ba cikin iyalinta ba". Wani irin abu taji yana yawo da ita,ya jima yana qoqarin daidaita mata nutsuwarta,amma kuma hakan bai hanata kwanan kuka ba,bisa sharadin itama gobe ba zata zauna a gidan ba,ya kaita gidan anni.....anni bata cancani fuskantar wannan tashin hankalin ita daya ba.
Chapter 174 · 0% Book details