← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 179 OF 215

Sashe 179

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bibo ce ita da zuwaira,sake maida dubansa yayi ga gabansa,mashkur ne shi da dan uwan tasa ta'asar.....mashkur din da gaba daya ya fita a hayyacinsa,tsufa sosai ya kamashi,wani irin tsufa na qarfi da yaji wanda wawulonsa ya sake tsananta munin abun. Sauran duka ya bisu da kallo,amma kowannensu munin fuskar mashkur ta zarta munin da yake gani a fuskokinsu,bawai muni na fuska kawai ba.....aaah muni na zuciya. Ma'aikatan gidan jaridar ya fara nunawa. "Wadannan na gama da case dinsu......aje a hadasu da diyar ambassador......ranar shiga kotu a hadosu tare qarqashin shari'a guda daya,lawyer na zaiji da komai". "Wayyo Allah.....mun shiga uku,don Allah sir kayi mana afuwa ka yafe mana,wallahi bamusan a kanka tace a buga labarin nan ba". Wani banzan kallo yayi masa. " Okay,idan wanine bani ba kenan zaku iya tozarta masa iyali,idan wani ne bani ba kenan zaku iya wulaqantashi ku wulaqanta aurensa da shaidar zur.....CP.....bana son sake jin muryarsa a nan wajen" Ya fada yana takawa ya jawo wata kujera. Kiiiii ya ajiyeta gaban bibo wadda jikinta ketsa tsuma,ya koma ya zauna sosai yana dora qafarsa daya kan daya. "Nutsu sosai.....labari zan baki sannan na sallameki". "To....to Allah yayi albarka". " Ameenatu ahmad sabreen takai budurcinta gidan mijinta,wanda ni Muhammed fuad jadda na karbeshi da kaina....kuma mutanen dake rayuwa damu suka shaida hakan a lokacin". Dif wuta ta daukewa bibo duk yadda takeji da tsageranci sai taji maganar ta girmeta. "Ke din uwace ko?,a kamatance bai dace na gaya miki haka ba ko?,saidai kash.....nidin bana yafiya bana kuma ragayya ga duk wanda yace zai taba rayuwar duniyata.....sabreen,a inda kuma aka samu akasi shine.....tuntuni kika sanya qafa kika take wannan girman daya kamata ki samu......to ina me!miki albishir.....sabreen takai bantenta......ba wani matsiyaci ko lusarin daya samu damar tsallake wannan shingen......yadda kika dinga yada jita jitan mutuniyar banza ce......na baki dama na biyu kisan yadda zaki wanke wannan sunan daga kanta....ki maida gurbinsa da kyakkyawar shaida,idan hakan bata kasance ba kuwa,a karo na biyu idan na daukoki batar dake zanyi bat.....a bude mata ta tafi gida". Bata tsaya tunani ko waiwayen tazarar nisar tafiyar da zatayi a qasa,ba tare da abun hawa ko kudin mota ba ta fice,tunda har ta samu nasarar shaqar iskar 'yanci kuwa......bataga abinda zai hanata hada lecture din wayar da kan al'ummarta kan muhimmancin mutuncin da sabreen ke dashi ba. Idanunsa ya ware akan mutum uku.....mutum ukun da yakejin laifinsu yafi na kowa girma,ya sake aza idanunsa akan zuwaira wadda daga ita har bibo sunyi wani zuzzurmawa. Duk da ajiya ce kawai akayi musu irin ajiyar da take daidai da aljannar kare. "Kamata yayi kema a hadaki da wadancan.....sashen manyan laifuka ko?..." Kuka ta fashe dashi tana hurwa tana neman agajinsa. "Ki rufen baki,don duk yadda raina yakai ga baci bazan iya zabgawa fuskar dakeda furfura mari ba,koda furfurar ta banza ce" Gum ta koma tayi sannna ya bude idonsa yana sake dubanta. "Kina gidana kina qarqashin inuwata amma kina neman hanyar da zaa shigo a keta haddin iyalina?!.....abu guda ya rage miki ki gayamin......waye ya sanyaki boyesu a dakinki kika fiddosu da dare zuwa sassan matata!!!". Wata bahaguwar tsawa daya sauke mata sai data tattara gudawa me yawa a cikin mashkur,ya rasa wanne.ibtila'i da bala'i ne yake hanashi furta masa sunan.matar kowa ma ya huta?,fatansa daya wannan tsohuwar ta kira sunanta,wataqila ko kwatance da ka yayi akan shima ita ta dauki.nauyinsa duk da akwai nasa shirin. "Mmm.......maamah ce" Sunan ya saukar masa cikin ba zata. Fuska ya yamutsa yana dubanta. "Wacce kenan?" "Hajiya maamah.....mariya mahaifiyarka" Komai ya tsaya masa na wasu daqiqu,sai daya koma daidai kuma kwanyarsa ta cika da wasi wasi. "Cp.....janye matar nan,a hadata da wadancan mutanen". Kallo daya ya yiwa mummunar fuskar mashkur,wadda ta jima da tashi daga kyakkyawa zuwa asalin mummuna. "Mariya ce nima!.....maamah ake ce mata" Ya fada da sarqaqqiyar muryarsa da bata fita yanzu tartar saboda fitar haqora sha biyar daga bakinsa. Kaman ya dauki takobi ya jefeshi dashi haka yaji,duk wani jini dake jikinsa yaji yana neman daskarewa,kwanyarsa kuma tana shirin yi masa formatting da karan kanta irin na kota kwana,saidai kiran wayarsa yaso maida komai muhallinsa,ya daga kiran bawai don yana gane waye ke kiran nasa ba yana komawa kaman wani shashasha. "Jordan ne sir.......sir an jona musu na'urar fidda bayanai cikin sauqi,sun kuma yi bayanin komai...." "Me aka samu?" Ya tambaya cikin sarewa da jin komai. "Am sir.....kayi haquri.....gaskiya bayanansu na qarshe kaman na'urar ta samu matsala.....sunce zaa sake bincikawa" "Jordan please tell me.....ka gayamin ko waye ya sanyasu.....bana buqatar jinkiri a daidai wannan lokacin". "Sir....sir" Sai ya kama inda inda. "Tell me nace!" Ya fada a tsawace. "Mariya......mariya ce maamah". Iya abinda fuad yaji kenan wayar ta sulale daga hannunsa ta fadi qasa. Bai sani ba......jijiyoyin hannunsa ne suka daina aiki yadda ya kamata ko kuma qwaqwalwarsa ce?!. Tashin hankali! Allah ka rabamu dashi! Me karatu sai ince muje mu qarasa Hugumanku ce Na gode *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 149 *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX Kowacce gaba ta jikinsa sai yaji tayi wani irin sanyi,sai ya dinga jin kaman bashi da wani sauran damar ya motsa ko ya sakeyin kuzari a daidai wannan lokacin. "Mariya ce.....maaamah ce......itace" Sautukan suka dinga haduwa suna masa amsa kuwa a tsakiyar kansa. "Are you okay sir?" Muryar cp tayi kutse cikin tunaninsa,wanda yaga lokaci daya fu'ad din yanayinsa ya sauya,wuta kuma ta dauke masa. Da qyar ya iya daga idanunsa ya kalli cp saboda wani dan banzan ciwon kai daya saukar masa lokaci guda. "Yes.....am okay,akwai wadanda sukayi kidnapping 'yar alhaji hamza kibiya......za'a canzasu daga can inda suke a kawosu nan a hadesu......duk yadda ta kama ayi musu hukunci". " Ma sha Allah....sunzo.hannu kenan?" Kai ya jinjina masa kawai. Bayason doguwar magana sam sam,don shi kadai yasan yadda kansa yake masa wani irin bala'e'en ciwo,yana jin yadda zuciyarsa ke tafasa da wani irin mahaukacin fushi da yake tsoron kada ya illatashi shi a karan kansa. Da zafi zafi ya fita a gurin,ya samu abdulgaffar suna tsaye suna dakon fitowarsa. Hannu kawai ya miqa masa "Bani key" Ya fada ba tare daya dubu abdulgaffar ba. Baki ya saki yana kallon boss din nashi,baisan meye haka da zafi ya tunzurashi ba ko kuma ya sauyashi. "Sir.....muje na kaika duk inda zaka je.....like kaman baka cikin mode din da za'a barka kayi driving". "Just give me the keys abdulgaffar.......ko mutuwa zanyi a hanya kana da asara?........wanda ya kawoni duniya ma bashi da asara ballantana kai!" Ya fada da wata irin tsawa data bashi matuqar mamaki. Salin alin ya miqa masa key din,saidai kuma ya yiwa sauran team nashi alama da ido,don haka fu'ad din yana tada motar yana fita suka bishi a baya cikin salon da bazai gane shi suke ba. Suna matuqar qaunarsa da kula da dukka abinda zai cutar dashi,suna matuqar jinsa a jiki irin kusa kusannan,suna jinsa tamkar wani babban yayansu da yake da ruwa da tsaki a rayuwarsu,inda suna da hali tabbas ba zasu bari ba ko quda me cutarwa ya sauka a kansa ba. Wani mahaukacin gudu yake zubawa wanda ya sake tabbatar musu da ba lafiya ba,hankalin abdulgaffar akan motar yana duban wanda ya bawa yayi driving. "Ka kula sosai,kada ka matsi bayansa da yawa kada kuma ka bari ya kufce mana" Ya fada yana gyara zaman Bluetooth din kunnensa yana magana da na motar baya. Shi kansa yasan gudun da yakeyi ya wuce qa'ida.......amma a irin zafi da bugun da tasa zuciyar takeyi sai yakejin ba wani gudu yake ba shi din. Idanunsa fes bisa kwalta amma tunaninsa yayi nesa sa gangar jikinsa. Baisan kuka yakeyi ba saida yaji iska na fifita hawayen daya silmiyo masa,karon farko tun bayan tafiyarta ta barsu.....karon farko tun bayan wasu shekaru masu yawan gaske da ya share wani abu bai sakashi kuka ba......a yau a zagaye na biyu ta sake zama silar kukanshi. Hannunsa daya ya saki dava steering din,ya shafo hawayen yana kallon su,a wannan lokaci yana jin ta gama sanyashi kuka......yayi kuka qarshe a rayuwarsa saboda ita. Tsananin kunyar anni da abba yakeji,da wanne idanu zai kallesu ya shaida musu mahaifiyarsa ce ta aikata ma diyar cikinsu autarsu haka?,da wanne bakin zai musu bayani?,wanne shine kalar sakayyar da suka cancanci su samu makwafin alkhairin da sukayi mata?. Wani birkitaccen parking yayi qofar gidan,parking din da ya tada qura,ya kuma ja hankalin malam sa'adu dake zaune daga cikin gidan a bakin qofa yana jan tasbaha. Da sassarfa yake takun nasa,kaman me gaggawar cimma wani abun. Security na farko ne ya hangoshi,ya kuma taso ya bude masa da sauri kafin yakai ga qarasowa. Kusan ba sosai yake gani ba,fatansa kawai ya cimmata......fatansa kawai ya isa gareta......ya kuma tambayeta dukka akan me?,me yasa?. Da sauri me aikinta dake saukowa daga samanta taja baya tana zubewa sanda taga shigowarsa. "Barka da warhaka yallabai?" Sam ba gaisuwarta bace damuwarsa,bai kuma damu ya amsa ba "Tana ina?" Ya tambayeta kai tsaye yana jin jikinsa ko ina yana rawa. "Tana sama" Ta amsa masa tana rabewa ganin yadda ya nufo saman da sauri bata ko dire statement dinta ba. Matakala bibbiyu ya dinga hadawa har Allah ya kaishi saman. Dab da matakalar qarshe sautin muryarta ya sauka a kunnensa. "Ta yaya akayi saken da har wani yasan inda suka boyeta.....wanne irin hauka ne wannan?,baisan muhimmancin yarinyar nan a hannuna ba?,subucewarta da kuma kamasun da akayi yasan irin asarar da zai jawomin?.....bani da haufi akan zasu iya fadar sunana......duk da boka baiyi aiki a kansu ba amma kudin dana musu alqawari da alqawarin dana musu akan koda tsautsayi ta gifta zan fiddasu....iya wannan bazai bari su fadi sunana ba" Ta furta cikin bawa kanta tabbaci da yaqini da gaibu da qaryar daka iya fidda bawa daga ainihin imaninsa. Wani abune ya fusgeshi sosai,da sassarfar data jawo hankalinta daga wayar da takeyi. Wani irin duba take masa me cike da tsoro da kokwanton ya jita ko bai jita ba?,zuciyarta gaba daya ta kasa bata nutsuwar bai jita din ba saboda wani irin kallo dake fita daga idanuwan da suka sauya launi suka jirkice,daga fararen qwayar idanuwa zuwa
Chapter 179 · 0% Book details