← Book details Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 209 OF 215

Sashe 209

Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ruwana idan ummee ta jika.....let's go,mintunan zuwanshi da dawowarsa basu da yawa" Hannun juna suka riqe suna hirarrakinsu,wanda kana kallo zakasan akwai shaquwa da qaunar juna me tsananin gaske. Ita kadai yau take zaune saman wheelchair din nata,kusan awa biyu kenan. Mutum daya take sanya ran shigowarsa kaman yadda ya saba......yaro guda dayan da take mamakin yadda yafi kowa qulafucinta a gidan da qoqarin kula da duk wani motsi nata......yaro guda dayan da ita kanta yafi shiga ranta sosai wato sauban. Jifa jifa tana jin motsin yaran,guje gujensu kasancewar weekend ce.....amma yau ko wasan kaka da jikan data jima tana nuna musu bataso ba wanda ya leqota yayi mata,duk sai ta jita ba dadi. Sabreen ce ta fado a ranta,ba yadda za'ayi duk wuya.....duk runtsi idan tana nan ta barta ta zauna shuru haka,koda kuwa bata buqatar komai zata umarci biyu ko uku cikin haihuwa yara rai goma da Allah ya bata wani yazo ya zauna kusa da ita. Wani abu ta hadiye,karon farko da taji tana dokin ta dawo daga tafiyar kwanaki ukun da tayi zuwa qasar saudiyya. Daidai nan yayi sallama,sanye da dinkin kaftan da aka yishi da wani fari qall din yadi me daraja. Dinkin babbar riga ne da 'yar ciki dinkin da aka zamanantar dashi,ya kuma sake maida fuad din kaman wani qaramin matashi. Baiyi amfani da hula ba,sai farin rawani daya nada saman farar hular kanshi,sai ya fito kaman wani basaraken malami. Duk da ya dubata dazun yanzun bai gaza wajen dawowa wajenta ba,ya tsugunna ya gaidata,ta amsa masa da sautin da ba kowa yake iya fahimtar abinda take fadi ba idan ka dauke shi da Sabreen da suke iya fahimtar kusan komai tace. Nasarar fara fitar sautin nata ma gaba daya ya samo asali ne daga Sabreen,wani umra da sukaje,ta samu daman tara roba wajen indararon ka'aba ta tari ruwan saman dake sauka ta saitin wajen,ta kumayi tofin addu'o'i sosai data samu daga wajen mallam,ta durfafi bata. Wani abu ne daya tsayewa maamah din a rai,har yau ta kasa mantawa da abun,duk da sai bayan nasarar ta samu takejin daga ina ruwan ya fito,basu gaya mata ba gudun kada taqi sha. "Yau zata dawo?,daukota zakaje kayi?" Ta tambayeshi sanda ya miqe yana soma takawa da murdadden harshenta. A mamakance ya juyo yana duban maamah din,wai yau ita ke tambayar dawowar Sabreen?,wani farinciki yana sauka a zuciyarsa ya gyada mata kai. "Eh,saura mintunan kadan jirgin ya sauka". "A dawo lafiya" Ta furta tana jin wani dadi yana mamayeta . "Allah yasa" Ya amsa wata qwalla tana cika masa idanu. Yau maamah ke masa addu'ar da alamu sun nuna kai tsaye suna fita ne daga zuciyar ta?. Sai daya tsayar da jordan cikin motar ya daidaita kansa,ya kalli fuskarsa yaga ta koma ainihin mode dinta sannan yace suje. Bayason yaje da wani sauyi ko kadan saman fuskarsa,don yasan abune da tana masa kallon farko zata karanci hakan,shi kuma duka yau din yana buqatar kyakkyawan yanayi shida duniyarshi,wadda yayi missing nata tsahon kwanaki biyar kenan. Cikin hukuncin Allah JADDA MAJESTY JET ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake abuja. Mintuna kadan kafin jirgen ya sauke matakalarsa a hankali,tsakanin wasu mintunan kuma mutanen dake da iko da jadda majesty din suka fara fitowa. Da farko wasu matane guda biyu masu baqar fata,giant dasu,sanye da baqaqen abayas da mayafinta wanda sukayi rolling,sannan kuma suka manne idanunsu da baqaqe glasses. Mata biyun dake bayansu su dinma abayanne a jikinsu,saidai tasu ruwan wine color ne. Daya janye take da wata qaramar luxury luggage,yayin da dayan ke dauke da wata kyakkyawar jaka. Kyakkyawar halittar dake takowa daga tsakiyarsu ta dushe kowacce diya mace dake tafiya tare da ita. Mistress ameenatu ahmad mrs muhammad jadda......the lady of the house itace ke takawa d'ai d'ai cikin wani yanayi da zai tabbatar maka da cikar kamala da nutsuwa gami da kammaluwar hankali da nutsuwarta waje guda. Sanye take cikin wata Turkish gown ta wani lafiyayyen material,rigar ta bude sosai daga qasa,armless ce butter color me adon gray color da wasu manyan flowers masu ban sha'awa,wadda aka yiwa top gray color me dogon hannu da kuma sarqarta a jikin rigar ta yadda basai ta buqaci wata spare sarqa ba. Tayi rolling kanta da gray color din wani exclusive veil,qafarta na sanye da wani high hill daya kasance mahadin qaramar handbag din hannunta da batafi taci qananun abubuwa ba sai tsananin tsada da jakar ke dashi. Rungume take da wata baby girl wadda ke sanye da gown armless fara qal data kasance mahadin takalmin qafarta da kuma dan crown din dake saman kan yarinyar wanda ya hana sassalkan dogon gashinta bazuwa zuwa sassan fuskarta. Wani irin kamanni ne tsakanin ta da yarinyar na sak da sak.......abinda kawai ya banbanta su shine kasancewar yarinyar 'yar kululluba da ita. Ameenatu muhammad jadda kenan IFFA......shalelen family din jadda....diya mace qwaya daya da suke da ita cikin villa din tasu. Chubby din abbee......chubby din anni......kuma chubby din triplet da twins na jadda villa. Cikin kyakkyawar nutsuwar nan tata Madame kuma duniyar muhammad jadda wato ameenatu ahmad ke sauka da takalmin ta me tsini wanda zakayi tsammanin ba zata ita tafiya dashi ba,saidai caf caf take takawa da abinta cikin sani kan ado da gayu daya ratsa jini da jikinta gaba daya. Wani fitinannen qamshi take fiddawa wanda ya huda jikinta,irin qamshin da sai kazo kusa da ita kake iya jinsa a duk wani motsi da zatayi. Dawowarta kenan daga qasar saudi Arabia,bisa gayyatarta da sukayi don su karramata da lambar yabo da kuma girmamawa ta musamman kasancewar gidan marayunta gida na farko da kaf nahiyar africa dama wasu qasashen qetaren babu koda kwatankwacinsa. Gida ne daya fara bawa yara feature me kyau......ya fara inganta musu rayuwa da inganta mafarkansu bisa jagorancin me gayya me aiki muhammad fu'ad jadda mamallakin kamfani guda daya da baida kishiya dake sarrafa gold da Diamond a qasash kusan arba'in cikin qasashen da muke dasu a duniya sama da guda dari biyu. "Karbeta najma.....tayi bacci" Sabreen ta fadi a nutse tana miqawa nanny dinta ita gami da gyara rolling dinta daya dan cukuikuye. "Sarkin rigima" Nanny din nata ta fada tana rungumeta a kafadarta "Kunfi kusa,fadanki dana iffa ko waye ya shiga ma kunya zaiji" Sabreen ta fada tana murmushi. Murmushin daya samu isa ga idanuwan Muhammad fu'ad dake zaune cikin mota,ya kuma kori Jordan ya saita madubinsa yana qarewa duniyarsa kallo abinsa. Sam bata ganshi ba,bata kuma san yana mata kallon qurillar nan tashi ba,duk da cikin jikinta tana jin kamar wani kusanci yana wanzuwa tsakanin zukatan guda biyu. "Welcome maa" Shine abinda dukka ma'aikatan da suka rako boss jadda suke fada cikin rusunawa da girmamawa,yayin da ita kuma take amsawa cikin nuna kulawa da tambayarsu aikinsu. Abun yana bawa fu'ad mamaki sosai.....gaba daya ta zama tamkar wata uwa tsakanin kowanne ruhi dake rayuwa cikin jadda's villa. Ba iya yaran gidan su huda amna dasu saddiq ba......tsakanin kowa da kowa ma,muddin kana kwana kana tashi a jadda's villa. "Wannan tsadajjen murmushin rabonshi da akeyi ya isa haka please" Ta tsinci lallausan sautin nan nasa cikin kunnuwanta a sanda ya fito daga motar yana bude mata murfin motar yana kuma gyara babbar rigarsa da daya hannun. "Wow" Ta fada da wani boyayyen sautin da labbanta ne kawai zasu gaya maka abinda ta fada,tana fidda idanunta waje dukka a kansa. "Muffin......ka koma exactly ranar da ka zama angon ameenatu sabreen.......sak irin shigar". " Har yau har gobe har kullum ma cikin taya kaina murna nakeyi da mallakar mace irinki......ki taimakeni ki sakayamin kanki cikin motar nan kafin mazan dake airport dinnan kaf su qarasa kallemin ke" Kai ta girgiza tana dariya sanda ta fara takowa cikin jan aji. "Hammana yaushe xai canza ne?baya kallon madubi yaga yadda ya fara zama babban mutum?,babban mutum din daya ajiye yaran da sati me zuwa zasu kammala secondary school dinsu?" "Fu'ad bazai taba canzawa ba.....kishinsa da soyayyarsa game da Sabreen suna nan kaman yau aka ginasu" Ya amsa mata yana rufe motar,ya zagaya ya shiga nasa side din. _wacce addua kuka yimin littafinnan yaqi kammaluwa a yau?_ *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 *_NACE BA......._* *_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._* *_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_* *_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_* *_Da yardar Allah saikin godemin_* *_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_* Golden oud Hawi Sandal balls Sandal flakes Cotton bakhoor Kabbasine mix Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk) Deep crush (luxury khumra). Signature oil Kuleccham Kabbasine spray *_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_* *_PRIME SCENTS(the scents of royalty_* *KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI* *SUNA NAN A* *_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_* *BA'A KANO KIKE BA?* *_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_* *DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE* wa.me/+2348103155915 KO KI KIRATA TA NAN 08103155915 _Zafafabiyar_ 173 *_HUGUMA CLOSET ON TIKTOK_* *follow us diaries* https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1 Wani ajiyar zuciyar numfashi ya sauke yana lumshe ido gami da sauke nannauyan ajiyan zuciya. "Sai yanzu zuciyata zata koma aiki daidai......welcome home your royal highness" Ya fadi cikin salo na girmamawa yana hada hannuwansa guri guda. Murmushi tayi tana girgiza kai,kullum sabuwa ce a wajensa kaman yadda yake sabo a wajenta. "Giya nake roohi......hayaty kulliha" Ido ya fidda waje yana tashin motar tasa. "Wannan ranks din nifa bana gane musu sosai yanzu.......jira n ake naga nan gurin ya tasa" Ya fada yana taba lafaffen cikinta kaman bata taba daukan ciki ba. Itama waro idon tayi tana kallonsa. Mamaki yake bata yadda har yanzu 'ya'ya basu isheshi ba,yara goma cas tara dukkaninsu maza mace daya?,me kuma yake da buqata?. "Muffin......fauzan fawwaz da fawad ba graduation dinsu next week immediately ana gama bikin nadra da haneefa?". Dubanta kadan yayi sannan ya tada motar hankalinsa kwance. "What's that supposed to mean? And what's the point?......kin daina haihuwa?". Ganin yadda yayi maganan yana nuna da gaske yake fadi,saita karya wuyanta tana narke masa. "Hamma......yanka sau hudu fa?...." "Yanka hudun yana nufin kin gama?" Ya sake tambaya yana tsume fuska. Sosai tayi calming down kanta tana saukar da kanta. "Ni na isa?" Ta fada a sanyaye.
Chapter 209 · 0% Book details