Sashe 22
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba" Abinda zuciyarta ta dinga nanata mata kenan. Akan idanunta biyu ta buga uku tazo ta shude aka doshi hudu. Bata dako niyyar shirin komai bare akai ga batun zuwa walima. Komai nasu baya burgeta......bata da buqatar kuma ta cudanya dasu sam sam. Daidai lokacin da yake samanshi bayan dawowarsa daga sallar la'asar. Yaga kira daga security din dake waje sun shaida masa yana da baqi gasu zasu shigo ciki. Tunda yaji haka yasan 'yan gida ne.....inda baqin fuska ne lallai saisun nema izini an basu kafin su barsu su shigo,sai ya qarasa shiryawa cikin shaddar daya dauko,don already wandon yana jikinsa kafin yayi receiving call din. Wagambari ce a jikinsa,asalin tsadajjiyar wagambari sky blue da aka yiwa wani irin dinki na alfarma dake nuna zallar zamani da kuma sanin darajar ado da dinki. Ba wani mutum da zaiga sutura a jikinsa ya sake ganinta ya maimaitata,kusan sakawa daya yakewa kaya ya gama dasu,shi yasa duk sati cikin fidda suturunsa ake. Gaban madubi ya tsaya yana karya hular da zai sanya,shi gaba daya a takure yake,ire iren wadannan sabgogin bai saba dasu ba kwata kwata,wani harkar taro na biki,idan kanason ganin karsashinsa kazo sashen maganar kasuwanci. Kayan jikinsa kansu nauyi sukeyi masa,baisan ma me yasa a kayansa na wannan watan aka hada masa da dinkin manyan riguna ba,amna daya tuna farouq sai ya tabbatar shirinsa ne kawai. Halfcover ya sakawa qafarsa dan qasar italy da akayi cinikinsa da dollars masu yawa. Ya sanya hular saman kansa take wani irin mutum.....lafiyayyen half cast ya fito me matuqar daukan hankali da kwantaccen kwarjini daka iya wucewa da zuciyar kowacce d'iya mace. Waya daya ya dauka kawai sannan ya soma barin dakin. Yana sauka ne cikin takunsa dake bayyanar da nutsuwarsa jin kansa da kuma kamun kansa irin na cikakken namijin daya hada abubuwa da dama. "Wow summa wow.....hammana" Muryar amna ta fara sauka a kunnensa sanda yake fitowa zuwa parlor din. Yadda tayi maganar ya sanya murmushi subuce masa,ta kuma tuna masa da lokutan baya da yake very free ba kaman yanzu ba. Kullum ita ke bawa kwalliyarsa mark,anni na zaune a gefe tana musu dariya,saddiq na tsokanarta wani lokaci harsu sanyata kuka,shike tare mata shine ke hanasu. "Hamma ka sake zama ango sak......don Allah BB farouq,kalli ta nan gefen" Sai datayi maganar ya lura da farouq dake zaune kujerar qarshe riqe da wayarsa yana dannawa. Kadan ya daga kai ya kalleshi ya maida ga wayarsa "Yayi kyau mana amna.....amma kubarni nima soyayyata nake qoqarin gyarawa......Allah bazan qara wata uku a qasa ba.....guy dinnan daga jiya zuwa yau kalleshi ya sake canzawa?". "Stop it farouq......" Fuad yayi saurin fadi yana duban amna kafin ya maida kallonsa ga farouq din. Ya fahimci sarai abinda yake nufi,akwai amna a wajen "Hamma........am eager to see my aunty wallahi.....where's she?" Ta furta alamunta na nuna da gaske sabreen takeson gani,tana jin qaunarta sosai har cikin zuciyarta saboda hammanta. "Jeki fito da ita" Ya fada yana yiwa amna nuni da hanyar. Bata ko tsaya sauraren komai ba ta wuce wajen da sauri saurinta. Qarasa takowa yayi wajen da farouq ke zaune bayan wucewar amna din,aje wayar farouq din yayi yana dubansa. "Mutumina......akwai labari kenan" Ya qarashe zancan yana kashe masa ido. Harara ya gasa masa "Gidan jarida na bude daga jiya zuwa yau baka sani ba?" Dariya sosai farouq ya tuntsire da ita. "Idanma hakanne Allah an maka uzuri.....da gaske ba wani abu sabo?,baka kawo kusanci tsakaninku ba?" "Kaga don Allah malam dakata" Ya fada da husky voice dinsa "Na gama gane inda ka dosa gaba daya fa.....na gaya maka ne abinda yasa na kawo ta cikin gidan nan kenan ko kuwa?,ko bunsuru ne ka aje?...." Dariya sosai ta qwacewa farouq fiye da dazu,yayi qasa qasa da muryarsa yana dubansa "Maganar gaskiya ban yarda dakai ba.....i know you kaima ka san da wannan......a hadaka da halal dinka gidan da ba kowa saikai da ita.....kuma kacemin bakayi filling distance din dake tsakaninku ba.....anya wannan kyan da naga kanayi zakacemin duka a banza yake?". Rasa me zaiyi masa ya huce yayi,sai kawai hannunsa ya fada kan remote din dake gefansa,ya shammaceshi ya wurga masa ya sauka a kafadarsa. Duk duniya farouq kadai ke masa irin haka,yana sake hararasa yana zura hannunsa a aljihu ya fiddo wayaraa Idanunta kawai ta ware daga kashingiden da take sanda taji ana knocking na qofar. Kashingidar da ta yita ne kawai tana tunanin abubuwa masu yawa tare da qoqarin cudanya abubuwan dake mata kai kawo cikin kwanya. Tunani kala kala ta dinga yi sanda taji ana knocking din.....shine ya biyota ya sake cin zarafinta ko kuwa?.....wasu ne suka sake zuwa gidan ko ko yaya?. Daga qarshe da taga bata da zabi dole ta motsa labbanta tana fadin "Waye?" "Nice adda....na shigo please?" Amna tayi tambayar cikin zaquwa. Kiran adda din da akayi sai ya sosa mata wani miki,mikin kewar 'yan uwanta wadanda su kadai ke kiranta da wannan sunan. Ambatar sunan ya sakata miqewa ta zauna sosai tana zuro da qafafunta qasa. "Shigo" Ta amsa kawai kai tsaye ba tare da tasan waye ba. "Assalamu alaikummm" Amna ta furta duka tare da shigowarta cikin dakin cikin murmushi tana riqe da handle din qofar idanunta akan fuskar sabreen yayin da fuskarta ke qunshe da wadataccen murmushi "Wa'alaikumussalam" Sabreen ta amsa mata tana mata duban rashin sani. "Ma sha Allah" Amna ta furta a sarari tana kasa dauke idanunta daga kan sabreen,murmushin saman fuskarta kuma ya kasa bacewa. Dama ta sani......ta sani tabbas hammanta ya iya zabe......tasan hammanta lallai zai zabo matar da ba irin ta kowa ba,amma bata taba tsammanin iya zabinsa yakai har kaman haka ba. "I know.....kece adda sabreen dinmu ko?" Tayi tambayar da murmushi sosai tana nunata da yatsa idanunta a kanta. Dan shuru sabreen tayi tana kallonta ba tare data iya amsa mata ba,kwanyarta na mata lissafin wacece wannan din?. Tana da surutu sosai da alama,amma kuma yanayinta kadai ya gaya mata me kirki ce. "Sunana amna hamza kibiya.....nice autarsu hamma fu'ad". Tayi mata bayani a taqaice saboda ganin yadda take mata kallon rashin sani. Ta fahimci sarai bayaninta......qanwarsa takeson cewa,kamar ta basar sai kuma wata zuciyar ta tambayeta "Meye laifinta ita?" Don bataga wani hali na daban tattare da ita ba duk da a yanzun ta fara ganinta,amma bahaushe yace alamar qarfi tana game qiba. Har amnan ta sare,sai kuma taga ta saki qaramin murmushi da yayi barazanar dauke hankalin amnan saboda yadda ya fidda kyawun innocent face dinta "Qaraso mana" Ta furta tana miqewa tsaye tare da komawa saman sofa bed". Dukka energy dinta ya dawo,ta tura qofar a nutse tana ci gaba da murmushi ta tako ciki tana samun wajen zama saman wata sofa din ta daban *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_* 08187255862 "Am sorry aunty.....hala nayi disturbing naki kina hutawa" Ta sake fadi tana murmushi. Maida mata martanin murmushin tayi,wanda har sai da amnan ta furta "Ya salam,wanne irin kyau ne haka?". Kai ta girgiza "Ko kadan....." "Barka da rana,kin yini lafiya?,ya baqunta?,anni na miki ban gajiya,munzo mu wuce dake wajen walima......kowa yanaso ya ganki don jiya baku samu shigowa ba saboda dare ko?" Ta jero dukka abinda ke tafe da ita da wanda ke ranta kamar ba itace anni ta jawa kunne kada tazo ta cikata da surutu ba. A iya bayananta kawai ta gane wacece ita.....diyar matar nan da cikin kalamanta kawai zaka fahimci nutsuwa gami da tarin ilimi a ciki,wannan ya sanya sabreen sake sakar mata jiki kadan,saidai ta wani bangaren tana tunanin ta inda zata zamewa zuwa walimar,don sam bata shirya sake shiga kowanne taro ba. To na meye ma zata yita nuna fuskarta wa danginsu,bayan bawai tazo bane don ta zauna?. "Amma walimar......" Sai maganar tata ta katse saboda daga mata hannu da amna tayi sakamakon shigowar kira,tayi blushing kadan sannan ta kalli sabreen "Anni fa ba zama anyi suruka.....ungo nasan kirannan naki ne". Batason katsewa amna doki da farincikin da take ciki,don haka ta miqa hannu dole ta karbi wayar "Idan ba zaki samu daman zuwa ba diyata kada kiji kin takura.....kiyi zamanki,dama taro ne na sanya albarka,sai a sallami mutanen". Ji tayi ba zata iya mata haka ba,ba zata iya watsa mata qasa a ido ba,don haka tace a hankali "Muna hanya in sha Allah" "To Allah yayi muku albarka,Allah ya kawoku lafiya" "Ameen ameen" Ta amsa tana miqawa amna wayar idanunta nabin amnan da kallo. Ta fahimci wani farinciki takeji sosai,duk da batasan na meye ba,ganin amna din sai ya tuna mata da huda dinta,duk da ta girmi huda,saidai ita kuma ta girmi amna qila sa shekara uku ma ko hudu. Dole ta miqe ta soma qoqarin rage yafen jikinta da dankwalin kanta don shiga wanka,ta lullube jikinta da qaton towel ta wuce tabar amna tana bata labarin sabreen din,abinda yaso badda bacin rai da takurar zuciyar da take ciki ta shige bayi da boyayyen murmushi a qasan fuskarta. Komai na toilet din na kayan wankan ba irin nata bane,amna tunda ta karanta sunan products din da brand dinsu tasan harka ce kawai ta girma akayi. Daga yanayin sulbi da qamshin shower gel din kadai ta sake sallamawa,wannan ya dauketa minti kusan ashirin sannan ta gama. Towel biyu kawai ta shigo dashi,ta daura dayan,dayan kuwa dole ta nade kanta dashi saboda sumarta data jiqa da ruwa,ba wanda zata yafa don suturta jikinta,don haka ta sako shower slipper din zuwa bakin qofar toilet din ta cireshi saman water proof doormats din dake sashe na biyu na toilet din ta murda handle din ta bude qofar. Daidai lokacin daya soma duba agogo ganin sun sakashi dabi'ar daba tasa ba.....dabi'ar daya tsana ya kuma ja mata kunne a dazu da kada ta soma aikatata kwata kwata. Tsaki yaja ya fara lalubar number wayar amna,saidai ya kirata kusan sau uku bata daga ba,wannan ya sakashi miqewa a fusace yayi ciki yana cewa farouq "Ina zuwa". Takawa kawai yakeyi cikin hallway din ba tare da yasan wanne ne dakinta a ciki ba?. Haka ya dinga gota bedrooms din a hankali,sai daya isa na qarshe sannan yadan tsaya cak yana kasa kunne duk yasan bazaiji motsin komai ba saboda yanayin door din,a jikinsa kawai yaji da mutum a nan,sai ya juya yana fuskantar qofar ya murdata da dan zafin nama. Opposite suke tsakanin qofar toilet din