Sashe 118
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sallah ta sake boyewa cikin duvet. "Feel free......brush kawai zanyi na fita" Ya fada yana matsowa bayanta. Dab da ita ya tsaya,har jikinsa yana gugar nata,fuskarsa ta fito bayan tata ta cikin madubin,ya zube idanunsa fes da suka qara wani irin haske saman tata fuskar ta cikin madubin. Wani irin murmushi ne kwance a fuskarsa.....wata irin shimfidaddiyar walwala da makamanciyarta bata taba wanzuwa saman fuskar tasa ba da annuri suke fita daga fuskar tasa. Qwayar idanunta yaketa laluba yana son ya kalla amma ta hana mishi kallo,ta zura brush din kawai a bakinta tana wankewa tana kuma jin yadda yake sake shigewa jikinta da sunan brush zaiyi. Ta gefe da gefen cikinta ya zura hannuwansa ya zari brush dun,ya saka toothpaste duk a hakan yana sake shige mata,ya tura brush din bakinsa ya soma wankewa shima a hankali yana sake maida idonsa ga fuskarta data futo sosai ta madubin. Wani kallo yake mata ko qiftawa baya yi,yana fatan tayi kuskure ko sau daya ta daga kai ta kalleshi,yana son karantarta ta cikin idanunta sosai,ya sake matsawa sosai jikinta yana sansana kanta dake fidda wani irin sassanyan qamshi. Ta gama nata brush din amma tanata juyashi a hannunta,ta rasa yadda zata gaya masa.....ta kasa daga kai ta kalleshi ma bare ta samu qwarin gwiwar gaya masa. Ya karanci hakan,murmushi ya qwace masa. "Wannan kunyar daga ina?" Ya tambayi kansa da kansa daga can qasan zuciyarsa. Yana sane yaci gaba da cinye musu lokaci,yanason tayi magana amma kuma ta gaza,har zuwa sanda taji ta soma tuqewa,saita ajiye brush din,ta kuma juyo da hanzari tana fadin. "Ni na gama" Qurjinsa ta fada kai tsaye,don babu wani space da zai bata daman wucewa. Kan qirjinsa idanunta suka fada,ni'imtaccen gargasar qirjin tayi maraba,ta daga idonta a hankali tana kallon tazarar nisan tsahon dake tsakaninsu. Ya fita tsaho sosai,duk da cewa ita din ba gajeriya bace,idanunta suka sauka kan Adam's apple dinsa daya fito sosai ta maqogoronsa kaman zai fado. Wani abu guda daya tal da yake burgeta ga halittan namiji kenan......batasan meyasa yake burgeta ba,amma dai tasan yana bata mamaki,ta jima kuma tanason taji abun ya yake,tauri ne dashi?,yana musu zafi ko kuwa?,ba tare da tunanin komai ba ta miqa yatsanta a hankali zuwa wajen ta tabashi. Cikin kowanne jini dake harbawa a jikinsa yaji saukar yatsan nata,ya hadiye wani abu daya sanya Adam's apple din motsi yayi qasa ya sake dawowa saman. Kasa jurewa abinda yakeji din yayi,sai ya fincikota sosai zuwa jikinsa ya matseta a qirjinsa da kyau yana dora fuskarsa saman wuyanta. "Wannan tsokana ne ai......yanzun kuma inda zan ritsaki kona nema fansa saiki isheni da kukan banza......har a kiramin anni ma da momma ko?". Kunya ce ta kamata me tsanani,akan jiya yake tsokanarta ta sani......sannan ita kanta batasan ma'anar abinda tayin ba yanzun,taji tana sha'awar tabawa ne kawai. "Nifa wannan gaisuwar baiyimin ba......ina buqatar zuzzurfan alaqa tsakanin da iyalina......inason ki zama qawata.....aminiyata......mamana.....yayata.....qanwata....oh" Sai kuma ya tsaya yana dagota daga jikinsa gami da dan dukan goshinsa. "Ashe fa ance sai anyi shawarar za'a soni ko aah ko?" Ya fada yana ware mata idanunsa. Kauda kanta tayi gefe daya zuciyarta na bugawa,wani murmushi yana son kubce mata amma tana hana hakan,bata ankara ba taji ya dagata cak ya azata gefan sink din bandakin,hakan ya bawa santala santalan cinyoyinta daman bayyana don bathrobe din ta dage kadan. "Kinsan me?" Ya fada yana tsayawa tsakanin cinyoyinta,hucin numfashinsa dana daddadan turarensa yana sauka a fuskarta. "Karki wahalar da kanki DUNIYATA kice saikin koyawa kanki sona......" Daga kai tayi ta kalleshi abinda yakeson gani kenan dama tun dazu,saidai ita din tayi hakanne saboda mamakin maganarsa. Girarsa ya dage mata dukka biyun yana jin dadin ganin qwayar idanunta. Oily eyes daya jima yana kokwanto shin akwaisu?,sai gasu a jikin abinda yake mallakinsa gaba daya. "Yes.....iya soyayyar da nake miki ma ta ishemu mu rayu ni dake.....bake kadai bama.....har babies din da zamu haifa nan gaba" Ya fada yana dora hannunsa saman plate tummy dinta,abinda ya sanyata jan wani irin numfashi saboda tafin hannunsa guda daya daya dora saman budaddun cinyoyinta. "DUNIYATA....Kinsan yara nawa nakeso ki haifamin?" Kasa amsa masa tayi,tafi buqatar ya matsa baya kadan kada ya dagula mata lissafi,abinda ta fahimta kaman yana son sake mata wayo ne kawai yake saka kusanta kanshi da ita. "Karka zaqe da yawa.....har yanzu ban gama yanke hukunci ba" Ta fada cikin tsanani dakiya. Dariya yakeso yayi sosai amma ya dake,ya fahimci qarfin hali irin nata da zallar qi fadi dake dawainiya da ita. "Don't worry.....kedai ki tayani ji ma kawai ya wadatar dani" Yana kaiwa nan ya sunkuceta gaba daya tamkar ya dauki 'yar jaririya yana takowa zuwa bedroom din. "Ka saukeni" Ta fada a narke,saboda ta lura gaba daya ya raina dagata,ya maidata kamar wata 'yar bebin roba. "Ta yaya zakiyi nauyi kina wasa da abinci?,indai kinason mu shirya saikin koyi cin abinci irin na muhammad fu'ad" Yakai qarshen maganar yana direta saman sofa bed,sannan ya fara takawa a hankali zuwa saman dressing table yana kwaso kayan shafanshi data tabbatar yafi qarfin talaka irinta. Gabanta ya zubesu gaba daya sannan shima yabisu ya zauna a gabanta yana tankwashe qafa tamkar bawa da uban gidansa. Ya soma bude cream cream din da wasu irin abubuwa da batace ga sunansu ba ya fara tatsawa a hannunsa sannan ya kamo hannunta yana juye mata su a ciki. "Zaki iya haifamin yara dozen biyu?" Yayi maganar murya a sanyaye da wani zuzzurfan sauti yana riqe da hannunta da yake maida cream din daga hannunsa zuwa nata. Idanu tadan wara tana dubansa da kyau. "Please am serious.....ko through IVF ne.....a dinga saka miki biyar biyar.....nayi alqawari ba zaki sha wahala ba.....zan biya ko nawa ne a ciresu cikin aminci.....zan kashe miki ko nawa ne DUNIYATA.....nayi alqawari" Mamaki sake kasheta yayi ganin yadda yake maganan da dukka gaskiyarsa,hakan ya bayyana itama a idanunta,sai ya saki wani murmushi yanayin fuskarsa yana canzawa. "Kina mamaki ko?" Ya tambayeta yana sakar mata hannu don ta samu daman shafa man daya tatso mata. "Naso mu da yawa abbanmu ya haifa.....nayi wannan burin saboda gidan masu yara da yawa yana burgeni,saidai kuma mu biyu aka haifa.....inaso na tarawa abbana zuria me yawan gaske.....zuri'ar da zasu dawwama suna masa addu'a da sadaqa jariya.....bani da sha'awa ko burin auren mata biyu.....dake kadai nakeso na rayu DUNIYATA shi yasa nakeso ke din daya ki zama uwar dukka yarana" Ya qarasa fada yana dubanta. "Baga fareeda ba?" Tayi zancan da wani yanayi da ya sanya murmushi kubce masa,yadan dafa goshinsa yana cewa. "Maganan fareedan bai wuce ba?..... apologize din da nayi jiya baiyi ba?.....okay am ready to repeat it" Ya fada yana jinjina yadda abun yafi tsaya mata a rai fiye da komai. Kafadunta duka biyun ta daga tana kauda kai "Ina ruwana nikam.....am temporary......" "Temporary?" Ya katseta cikin maimaitawa yana dubanta da kyau ba tare da ya barta ta qarasa fada ba,sai ya ajiye boyayyen numfashi "You're my world.....kece DUNIYATA sabrrrrr....na rantse da Allah.....banda ubangijin daya haliccemu ba wanda ya isa ya qwaceki a hannuna.....ke kanki baki isa ki raba kanki dani ba.......ko mutuwa ina kai qararta wajen Allah.....muddin tana da nufin rabani dake ubangiji ya hukuntamin ita". Sosai maganarsa ta ratsata,taci gaba da shafa wa hannayenta man cikin wani irin kasala ba tare data dago idanunta ta kalleshi ba. "Ya kamata muje kiyi break" Ya fada yana katse shirun hadi da miqewa. Batasan me ya matsa yayi ba sai daya miqo mata rigar saman cinyarta. Rigar jiya ce dai da bata saka ba,saita daga ido tana masa kallon Why?. Kafada ya daga yana watsa hannuwansa. "Zan iya saka miki if ba zaki iya sawa ba" Kai ta girgiza masa da sauri,don ta tuna jiyan,daga saka rigar labari yasha banban. "To ka fita sai na shirya" Ta fada a shagwabe still "Inje ina?,bayan ko na fita dinma saina dawo na taimaka miki na daure miki rigar kin manta?" Ya fada hannuwansa na goye a qirjinsa yana qare mata kallo,don hatta cikin bathrobe din ba qaramin kyau tayi masa ba. "Na rufe idona.....inkin gama sakawa ki gayamin" Ya fada yana juya mata baya gami da maida kallonsa qofa yana ganin gilmawar ruwa ta tsakanin labulayen da basu gama rufuwa ba. A gurguje ta saka rigar,tanayi tana waiwaye wai kada ya juyo ya ganta bata sani ba. Dariya yakeyi abinsa can qasan ransa,don yana ganinta tarwai ta wani glass dake gabansa ba tare da ta sani ba. "Zan iya juyowa?" Ya tambaya yana danne dariyarsa. "Eh" Ta fada tana turo baki gaba,abinda yayi matuqar burgeshi har yaji kaman ya kama lips din ya shanye. A nutse ya dinga bin igiyoyin yana daure mata,kowacce daya saiya tambaya "Tayi haka?" Kai take daga masa mafi yawa,ta koma kaman kurman qarfi da yaki,ta tabbatar kaf halittun bayanta ya gama qare musu kallo,tana jin yadda yake sakin ajiyar zuciya time to time. Yadda maroon din rigar ta zauna daga bayanta kadai ya qawatar dashi gami da tafiya da hankalinsa. Ya dora yatsunsa a hankali saman fatar wuyanta,inda wajen ya danyi jajaja. Hannunta ta dora saman nasa tana dan danne wajen,guri kusan uku duka haka sukayi,yasan kuma shine sila,zare hannun nasa yayi yana juyo da ita tana fuskantarsa. Idanunsa ya lumshe yana kuma budesu duka samanta. "You look so gorgeous" Ya motsa labbansa yana furtawa da wani irin sassanyan yanayi yana duban qirjinta da yayi redness shima guri uku. Yatsantsa yakai wajen yadan taba sannan yace "Does it hurt?" Fuska ta kwabe masa cike da shagwaba kaman zata sake masa kuka,sai ya yarfar da hannunsa yana fadin. "Ayyah.....sorry,bari na fanshi wannan ciwon" Ya fada yana ja da baya fuskarsa da murmushi. Luggage dinsa ya kwantar ya bude,ya ciro wani dan mitsitsin box ya tako gabanta. "Qaramim gift ne....for you duniyata" Ya fada yana ciro wani siririn agogo dake zuba qyalli. Koda bakasan meye ba kasan abune me matuqar daraja,kallo daya zakayi masa kasan abune me tsadar gaske,bashi da girma ko fadi amma yana daukan ido sosai. Matsowa yayi kusa da ita sosai,ya miqa mata hannunsa yana kallonta da ido. Ta fahimci me yake nufi amma saita noqe,bai wani tsaya jiranta ba yasa hannunsa ya kamo hannun nata sannan ya fara saka mata agogon. *_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_* 08187255862 _Zafafabiyar_ 103 103 "Ya subhanallah" Ya