Sashe 13
Duniyata Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ta fada tana murmushi. Ba tare da tunanin komai ba ko kawo komai ba momma bahijja tace "Bismillah mana......haba hajiya ai diyarku ce" Daada ta fadi yadda momma din ta karbi sabreen yana burgeta. Duk da tayi gaba zuwaira ke mata jagora zuwa wani daki na daban a saman benen.....amma saita dinga jin wani irin yanayi yana bibiyar gabobinta. Kasa zama tayi,tana a tsaye sanda taji zuwaira taja musu qofar ta fice. "Zauna mana.....ki yaye wannan lullubin kan naki......don fahimtata nakeso kiyi sosai tamkar yau ne karon farko da kika fara fahimta ko haddace wani abu a rayuwarki" Tayi maganar cikin jerarrun kalmomin da kana jinsu zakasan ko meye zata fada yana da matuqar muhimmanci a wajenta. Sai data fara janye lullubin nata baya,sannan ta sulale a wajen ta zauna. Tana jin kamar babu wani sauran qwarin gwiwa daya rage mata a rayuwa,duk da yadda take kokawa da zuciyarta da qoqarin qarfafawa kanta gwiwa. "To alhamdulillah.......komai ya kammala,kuma komai yazomin da sauqi fiye da yadda nayi zato ko kuma tsammani........ina fata baki manta meye manufar aurenmu ba?" A nutse sabreen din ta daga kai sannan ta zube mata idanunta saman fuskarta. Kallonta tayi na second kusan goma sannan ta gyada kai "Da kyau.....da farko abinda zan fara gaya miki shine abinda na maimaita miki a baya.......qaidar contract dina na farko shine sirri.......inason sirri,don muddin aikin nan ya fita daga da'irar sirri zuwa wata da'ira ta daban.....to tamkar kin wargaza rayuwarki da hannunki ne......bayan taki rayuwar da kika wargaza kuma......kin wargaza ta 'yan uwanki suma...." Daga ma maamah hannu tayi da hanzari tana zare idanunta daga kanta "Ki tsaya iya kan ameenatu kawai......huda,nadra da haneefa,tabasu ko sako sunansu cikin sabgarki da ameenatu tamkar ganganci ce" "Da kyau!" Maamah ta furta tana sakin murmushi,abubuwa biyu zuwa uku suna jan hankalinta. Gyara zamanta tayi tana ci gaba da murmushi "Ashe ameenatu ce....abu yayi kyau..ameenatu ta bata,wata ameenatun zata gyara,wannan abun yayimin dadi.......qwarin gwiwarki da rashin sarewarki ya burgeni......kariyar da kike bawa qannenki tana da yawa,kuma ita dai ta isa ta bani yaqini da tabbacin ba zaki bari a samu failure ba ko don saboda su......." "Shiga maganarki kai tsaye" Sabreen ta fadi mata tana kauda kanta zuwa wani sashe na daban. Idanu maamah tadan zuba mata har yanzu tana murmushi,sai kuma ta miqa hannu ta zaro wata paper da abun rubutu ta ajiye a gabanta. "Inaso ki rubuta adadin kudaden da kike da burin mallaka a rayuwarki......ni kuma zan mallaka miki su a madadin sadakin aikinki,zan kuma qara miki kwatankwacinsu muddin komai yayi daidai". Fararen manyan idanunta ta daga ta watsawa maamah su,karon farko da idanun suka yiwa maamah din wani kwarjini da bata taba jin irinsa ba. Murmushin da ya subuce kuma a fuskar sabreen ya sanya mata kokwanto "Ki fadi magana me muhimmanci saboda mutanen dake zaman jiranki a qasa" . Maganar tata tadan daure mata kai,a nata ganin ba wata magana da zata zama me muhimmanci a wajen sabreen sama da maganar kudin aikinta,wanda take ganin shi kadai ya isa ya bata azama akan aiwatar mata da komai. To amma akance......shi yaqi dan zamba ne,don haka ta gyada kai