Sashe 98
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
galla masa sama da asa tace "Hmmm! Kar ka so nin mana, dama ni na san ba kyakyawa bace kuma ba wayayya ba, amma ka sani ni ba shashasha bace..." Saida ta matsa daf da shi ta ora yatsarta kan irjinshi tace "Ina da hankali ai, ba za ka rainamin wayo ba Abdul." Hanyar akin ta tunkara zata fice sai kuma ta juyo ta kalleshi tace "Na fa a kar ka so nin, nima bana sonka." Kama ofar tayi ta bu e tana daf da fita Abdus-samad da gaba aya lamarinta ya mishi na kama da masu son kasheshi ya zuba mata idanu kawai yayi sauri aga bakinshi da yar yace "Ki jirani, zamu je gidanku ne." Da sauri ta dakata tare da juyowa ta kalleshi, ranar farko da ya bata izinin zuwa gidan sumbatar da ta mishi ta fi ashirin a fuska kawai, ya auka zai ga wannan farin cikin ne da irin kalmar da ta fa a masa a ranar cewa " *Ka fi kowa sarkina, ina alfahari da kai.*" Amma yanzu sai ta yatsina fuska kawai ta juya ta ficewarta ta barshi tamkar wani gaula. Mantawa yayi da shayin da sauri ya nufo gadon dan aukar hularshi da rawani da kuma sandar nan, saida ya bigi kofin ya zubar mishi a afa ya ji zafi sannan ya ankara da me ya yi, ba ma wannan ne ya aga mishi hankali ba kamar aramar ihun da yayi ya yarfe hannu wanda shi yasa tashin hankalin da yarinyar can ta kunna masa ne ya sa shi feso abun a suffar ihu. Ca Da sauri ya ora hular a kanshi haka ma rawanin ya laulayashi dai ne amma shi kanshi yasna baiyi ba, saidai bai da lokacin tsayawa gyarawa, ita yake so ya bi ya ri e damtsenta da kyau ya zazzare mata idanu dan kar ta sake kwatanta masa haukan nan irin na yay, haka kawai ta aga masa hankali, akan me? Sai ka ce wata mai son aukar fansa. Da an sauri ya fita a akin sai dai kuma saurin nashi ya ragu ne lokacin da ya ganta zaune a kan aya daga cikin kujerun royal in dake falon ta wani ora afa aya kan aya sai cika take tana batsewa. A hankali ya shiga takawa saidai hata takalmin dake afarshi afa ciki sauti suke bayarwa wani was was! Fuskarta da yake kallo ya ji tana razanashi haka kawai kamar ya ga dodonniya, sai ya ji zafin da ya fito da shi dan ya mata kashedi idan ma ta kama ya gaura mata mari dan gaskiya ta dagula masa lissafi sai ya ji duk ya ace, neman duburburcewa yake tun bai isa gareta ba. Gabanta ya tsaya am yace "Shine kika ya amin magana kuma kika baroni?" A hankali ta ago kanta ta zuba masa idanunta farare, sai kuma ta auke kanta tana aga gira sama irin "Ohon maka." Da wani sabon acin ran ya nunota da yatsa yace "Ke! Ke tsaya ki saurareni, kinga bana son irin haka, ban kulaki ba ki daina sakani a uku haka kawai, kuma kinga idan dai ba tsoro ba ki maim..." Irin kallon nan na gani kasheni ta watso masa, sai kuma tayi raurau da idanunta ta marairaice a sanyaye tace "Na maimaita? Marina za ka yi idan na maimaita? Saboda kawai ka tsaneni sai ka tsareni kana min ihu a kai..." Kamar an jonata kuma sai ta zabura ta mi e ta dafe ugu tana kallonshi sama da asa fuskarta a ha e zuciyarta na tafasa saboda cewa da ya yi baya sonta, ita yanzu a ganinta ai ta zama jini da tsokarshi, amma shine zai ce baya sonta sai sha uwa kawai, lallai ma! Haushinshi take ji sosai akan wannan maganar. Hawayen da suka cika mata idanu lokaci aya ta ha e tare da cewa "Wallahi ba dan kana sarki ba ko, da wani ne daban ko? Ji nake da na kabta mishi mari, amma ba komai akwai Allah." e baki yayi irin zai yi magana, sai kuma mamaki ya hanashi fa in komai ya sake gyara tsayuwa ya kalleta, ance idanu yayi ya sake kallonta da kyau, to shi dai bai san ya zaiyi da ita ba, ya cakumeta da kokawa ne? Ko gidan horo zai sa a argame mishi ita a bisa wannan zunubi da take aikatawa? Shi ma ba dan yana sarki kar a ce bashi da adalci ba, wannan abubuwa da take masa tana hassalashi ai ararta zaiyi wajen babban al ali. Da ta ga bai ce mata ala ba kuma so take ya kulata ko ta feso abinda ke ranta, sai kawai ta zura hannayenta biyu ta warware masa rawanin dake kanshi wanda ta ga ya aura ba daidai ba, fuskarta a ha e sosai amma kuma tana gyara masa na in rawanin, tsatsareta yayi da idanu sai kawai ya saki murmushi yace "Kin san dan ke ce shiyasa na yaleki ko?" Ba tare data kalleshi ba da muryarta dake nuna a hassale take tace "Ni ma dan kana kai in ne." Matse baki yayi ya ara gyara tsayuwarsa yace "Hummmm!" Ba ta kalleshi ba tace "Kai ma hmmm in." Sai kuma ta koma gunguni tana fa in "Tunda ka san kaine mijin, me ye ma na kulaki? Dan in fa i wani abu a ce ar wuta ce ni, wallahi dan kana sarki ba zan bari ka tauyeni ba, haka kawai." Gama fa arta da daidai gama aura masa na in kawai ta kama hanyar fita tana fa in "Muje." Da kallo ya bi bayanta yadda yau ake tafiyar ba ma an legezen (elegance) nan in ji yan boko sai kawai ya girgiza kai yace "Lallai, za ki san ko ni waye." Sanin yanzu fa dogarai zasu mata caa idan ta fita suna gaisheta dan a tunaninsu shine yasa saurin ri e alkyabbar da kyau ya aga sandar gaba aya ya zuba a guje ya tare gabanta suna kallon kallo, da sandar ya nunota yace "Kinga dakata, idan fa an kike ji ki bari har mu dawo, wallahi kar ki sa na tauye ha in al'ummata saboda rikicinki." Jinjina kai yayi ya gyara jikinshi da saita nutsuwarshi sannan ya jawo hular alkyabbarta ya rufe masa fuska kafin ya ri o hannunta ya bu ofar suka fita a nutse. Suna fitowa kowa ya shiga haramar kula da abinda ke wuyanshi, dogarai biyu ne suka shiga gabansu sai hu u dake bayansu suna ta faman zabga musu kirari na takawarsu lafiya, dreban dake cikin mota zaune yana ganinsu ya fito yana rusunawa shima, aga daga cikin dogarin ne ya bu e musu ofa, cikin nutsuwa ba tare da ya saki hannunta ba ya mata alamar ta fara shiga, a sanyaye ta aga afarta ta shiga kafin ya bi bayanta ya zauna aka rufo musu ofar. Dreban ne ya shiga lokacin da Saleema ta jaye hannunta daga cikin nashi, hakan yasa shi kallonta har zaiyi magana sai kuma dreban ya shigo, matsawa yayi sosai kusanta cikin ra a yace "Har yanzu hushi kike dani?" Sadda kanta tayi tare da an karkato da kanta kusan na shi kan ita ma da sigar ra a tace "Yaushe ma muka fara fa an da har kake tunanin ya isa a ce mun gama?" "Da saura kenan?" Ya fa a yana le a fuskarta, aga masa gira tayi sai kuma ta kanne masa ido aya, hakan yasa shi sake ra a mata "Kina irin haka sai ki sa sarkinki ya kauce hanya a gaban masu girmamashi." auke kanta kawai tayi tana kallon gilmawar doguwar da ar katangar gidan, shiru motar ta auka babu sautin komai duk da su hu u ne a motar, dan bayan ita da shi da dreba akwai an-baka dake tare da dreba a gaba, motar dake gabansu ma irin wacce suke ciki ce Prado sai dai fara, amma ita ma kamar wacce suke ciki ce daga bayanta wajen rubuta lamba sai motar ke auke da rubutun sunan *sultan de Maradi* sai an hoton tutar Niger daga gefe ka Numfashi ta sauke a nutse tare da an waigowa ta kalleshi, yadda ta ga motocin nasu suna aukar hankalin mutane ba wai dan kyawunsu ko tsadarsu ba sai dan shaida wa anda ke cikin motocin, yau ita ma ta kasance aya daga cikin mata masu wani matsayi da iko a garin nan ko ma ta ce a asar, lokaci ani da ya wuce a sake take tana rayuwar ta kamar kowa, yau gashi idan tana tafiya harda jami'an tsaro a bayan motar da take ciki guda biyu baya ga dogarawa. Zafin da ta ji kan kumatunta ta tabbatar da hawaye ne take, hakan yasa ta a hankali ta sakala hannunta ga nashi hannun ta ora kanta a kafa arshi ta an ja majina, a nutse ya le a fuskarta ganin hwaye sun sauke mata yayi saurin agota yana tallabo fuskarta cike da tsantsar kulawa yace "Matanmu, me ye faru? Fa an namu ya kai hakane?" Da sauri ta girgiza kai a sanyaye tace "A'a, ba shi bane." "To me ye?" Ya fa a yana sake tsareta da idanu, ara jan majina tayi dan hancinta ke neman umewa sannan tace "Falalar ubangijina nake tunawa, yadda ya min *BAIWA* sai na ke jin tamkar ni ka ai ce a fa in duniyar, shiyasa na yi nasarar wawushe komai." Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da jawota ya ora kanta a irjinshi yana an shafawa a nutse yace "Shiii! Ki godewa Allah." Jinjina kai tayi a zuciyarta ta furta "Alhamdulillah." Haka suka ci gaba da tafiya ba da gaggawa ba har suka isa ofar gidan, motar dake gaba mai gadin ya le a suka an yi magana jim ka an ya shiga ciki ya wangale musu ofar ya koma gefe yana kallon wucewar motocin guda uku, a farfajiyar sukayi fakin inda duk suka fiffito suka taru a daidai motarsu sai wata hadima dake tare da jakadiyar Saleema a motar dake bayansu ta yi azamar nufa cikin gidan dan sanar da su shigowar mai martaba da iyalinshi. Kallonshi Saleema tayi tana jin kamar ta cijesu, to ita a ganinta gidansu ne sai an mata iso za ta shigo? Takurar banza kawai! Saida hadimar ta fito anbaka ya kama hannun motar ya bu