Sashe 79
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fita a gidan saleema ba ta ko ji motsin Mamanta ba bare auntynta Lubna da har lokacin tana nan ita ma. Su Hameeda ne suka taso daga inda suka dur usa ranta ace na bulalar nan da aka tsula mata, kusan Mamanta ta tsaya tace "Momma ni na tafi gida, wallahi da na san kayan takaicin da zan tarar kenan da ban zo gidan nan ba." Juyawa tayi za ta fita tace "Aikin banza kawai." Da kallo suka bita har ta fita, Hadeeya ma akin Mamansu ta nufa tana fa in "Nima dai bari na kirashi ya zo ya aukeni, banga anfanin zaman ba." Da kallo Ardiya ta bita tace "Ke shikenan abinda kika za a ma rayuwarki kenan, ciki ne fa da ke." Da sauri tace "To wai Momma ya zanyi, tunda yana son abunshi ba shikenan ba." Da mamaki ta ri e ha a tace "Kuma dan yana so shikenan sai kiyi ta biye masa? Shikenan rayuwarki ce." _______________ Sanda suka iso masarautar anyi tsakiyar sallah isha'i, hakan yasa gidan ke shiru sosai, tunda aka ce ta fito ta zuro afafunta da addu'ar shigowa gida "Bismillahi wa'lajna, wa bismillahi karajna, wa'alallahi Rabbina tawakkalna." Kamata sukayi suka shiga ta ofar sirrin da sarki ke kai kawo a cikin suka dinga kutsawa har suka isa falonta na biyu a sabon wurin da ya zama mallakinta yanzu, gimbiya Kubra ce ta kamata ta zaunar da ita tare da cewa" Zauna ko." Saida ta zauna sannan hadiman suka zauna a asa. Shigowar gimbiya Ramlat yasa hadiman suka rage yawa a falon, sam ta kasa yarda da irin wannan shigewa da gimbiya Kubra take musu, hakan yasa ta mi ewa ba tare da tayi maganar da take son yi da Saleema ba ta kalli jakadiyarta amintatta tace "Jakadiya, kinsan abinda ya dace kiyi, zamu baku wuri ki shiryata, idan kun ida sai ki jira umarnin mai gado." Cike da ladabi ta amsa da "Angama ranki shi da Kallon gimbiya Kubra tayi da bata da niyyar tashi, amma da ta kalleta da idanu ta nuna mata mu tafi, dole ta mi e tana murmushi suka fice jakadiyarta na binta a baya tana ayyana "Idan ba yau ai akwai gobe." Suna fita jakadiyar ta taso ta rufe ofar sannan ta dawo wajen Saleema, a nutse ta fara cire mata alkyabbar nan, kamata tayi ta tashi suka shiga wani aki, kan wani gado gado mai shinfi e da leda ta zaunar da ita ta juya bayanta ta cire mata zip in rigarta. Tana ji tana gani ta sake tu eta zigidir kafin a saka mata wata yar riga ba a wace aka fara yi mata darzar fatar jikinta da ita, akin wani irin umi ne yake da wanda da farko ta ringa zufa sosai sai daga baya zufar ta tsane a jikinta a lokacin da ta ke mata wata irin lindar da ta kusan fitar da ita daga hayyacinta. Sosai take bin duk wani sa o na jikinta tamkar wanda zasu canza mata fatarta daga ba a zuwa fara, ruwa mai umin gaske mai ha e da ruwan turaren nan mai tsadar gaske suka wanke mata jikinta tas, babban towel in da ta bata ta aura yasa Saleema kallonta a nutse tace "Mama, ina so zanyi sallah isha'i." Jnjina mata kai tayi tace "Shikena, kiyi alwala idan kin idar sai mu ida." Da kallon son tambayar har yanzu ba'a gama ba kenan? Ta bita kafin ta aura alwala ta fito ta bata doguwar riga ta saka sannan ta kabarta sallah. Daga yadda dattijuwar ke zaune ya nuna mata kamar ita take jira, dan haka da ta sallame ba ta samu damar arasa Azkhar in da ta saba ba ta tashi suka koma akin. Rigar ta sake kamawa za ta cire mata, kamar za ta fashe da kuka ta kalleta tace "Mama, yanzu ma cirewa za'a yi?" Murmushi dattijuwar ta mata tace "Da alama ba sai na koyar dake tausasa harshenki ba, dan alamu sun nuna kin iya magana da babba, sai dai yalla ai sarki ne, sarkinki, idan zakiyi magana da shi idanunki a asa, sannan muryarki ta fi haka kwanciya, idan zai yiwu ki dinga magana tamkar muryarki na arin kuka dan tsoro, amma fa ba kowane lokaci ba, haduwarku ce ta farko wannan, ki kula sosai wajen magana da yalla ai, ki sani wata maganar ma ba da baki zaki furta masa ba, ido kawai sun isa su sanar masa da sa onki, matar sarki kike yanzu, dole ki koyi wannan sarauniyata, musamman idan kuna tare da mutane, ya dace ki fa a masa abinda kike son fa ane da idanunki da kuma yanayin fuskarki." Zaunar da ita ta sake yi bakin gadon ta zagaya bayanta, kanta da suka kwance mata tun a gida ta shiga warwarz mata yalwatacciyar sumarta tana rabata, wani dandanan man kai ta dinga shafa mata tare da dun ule mata shi tamkar kitso, saida ta gama ta zagayo gabanta tana kallon fuskar Saleema da uta dai ta ora hannayenta ta rufe irjinta sannan tace "Motsinki, tafiyarki, yanayin gudanar da duka lamuranki, dole a samu nutsuwa da aji a ciki, ko daga ke sai yalla ai ne, ba kowane lokaci zaki bu aci bu a bakinki ba, tambayarsa kawai zakiyi da idanu kuma ya fahimci me kike nufi, haka idan kina son ganar da shi wani abu ne dake kusa dashi, zaki iya yin fari da idanunki na sai kin ce uffan ba." A sanyaye ta sake fa in " A yanzu ke in kin zama uwar talakawa, nauyi mai girma ne ya hau kanki tare da nauyin da ya hau kan yalla ai, akwai bu atar ki zama hutunsa a cikin gida, ke ce za ki tarbeshi idan ya au zafi saboda nauyin al'umma, ke ce zaki tarbesa a duk halin da ya shigo miki, mulki babban lamari ne da idan Allah ya baka ba yana nufin ya fi sonka bane a cikin bayinsa, alamu ne na babbar jarabawa ake maka, akwai abubuwa dayawa na tashin hankali da zasu faru da shi a waje ya dinga shanyewa, amma ke matsalarki, ba lallai ne ya iya shanyeta ba, damuwarki arara za ta bayyanar da tasa damuwar har ta fara shafar mulkinsa, dan kuwa a gabanki ne zai iya fitar da acin ran da ya wuni yana sha a, a gabanki ne zai iya fitar da yanayi na tausayi, tsoro, da firgicin da yake zagaye ga talakawansa wanda hakan ke kassara nutsuwarshi da farin cikinsa, to kinga a nan dole ki zama mai nutsuwa, hankali, da sanin ta kamata, dan kuwa ke ce zaki zama mai shanye damuwarsa, akwai yiwuwar a gabanki ya zama tamkar yaron goye, idan baki lalla ashi ba sai ya aude har a kan kujerarsa ma, ki zamar masa kwanciyar hankalin cikin gida, yadda ko yana zaune a kujerarsa damuwa ta sakoshi a gaba da gajiya, ya zama ke ce kawai za ki zo masa a tunani a wannan lokacin, hakan kuma ba zai faru ba sai kin kasance mai tsafta, mai girmamashi da tausasawa a gareshi." Kasko dattijuwar ta auka tana hura huta tana ci gaba da fa a mata" Ki zama mai *ladabi* ata, idan ya ce yi, to kiyi indai bai sa a umarnin Allah ba, idan kuma ya umarceki akan wani abu ne da bai dace ba sakamakon aukar zafi irin na maza wasu lokutan, to a lokacin kada ki ce a'a ba haka ba, ki bishi da angama ranka shi da e, ki fara arin sama masa nutsuwa, idan kin tabbatar hankalinsa ya kwanta sai ki nuna masa hukuncin da ya yanke akwai tsauri a cikinsa, idan kuma ya zama mai kawo miki damuwar da ta shafeshi, kada kiyi asa a gwiwa wajen bayar da hankalinki kanshi, ki nutsu sosai ki bashi hankalinki tamkar baki ta a bawa wani abu mahimmanci ba sai lokacin, hakan zai bashi zummar fa a miki damuwarsa, idan ya fa a kuma ki kasance mai bin labarin daki-daki har ki fuskanci irin shawarar da za ki bashi game da lamarin, kinga kenan anan akwai bu atar ki zama mai hangen nesa da kuma kaifin walwa." Tana kallo ta yaye karpet in dake bayan ofar akin sai ka rame mai zurfi ya bayyana, kujerar tsugunno ta aza mata sannan ta kamota ta zaunar kan kujerar, kwa in da tayi na garin musawul ha e da turare na ruwa ta fara shafe mata jikinta da shi, sosai take murza mata shi a jiki har tana rintse idanu, bayan ta aza kaskon da sanyayyan amshi ya fara tasowa tare da haya i ka an ka an yadda ba zai cutar da ita ba, tana zaunawa ta kawo bargo mai nauyi ta rufe mata jiki dashi ruf sai iya fuskarta kawai. A ka an ta yi minti ashirin kafin ta tayar da ita suka nufi ban aki kuma har lokacin shawarwari take bata yadda zata fuskanci sabuwar rayuwarta, wani wankan ta sake yi da sabulun da aka ha a da zallan mayuka da basa saka haske sai gyara jiki ga kuma garin magarya da kuma man zeitun da sauran mayuka. Maclean da brush ta bata bayan ta ida wanka ta wanka bakinta sosai sannan ta fito. Tun ruwan jikinta basu tsane duka ba ta bata wani ha iyar farar humra da aka wa la abi da *Deeja* (akwai fa humrar nan mata, sai ki jaraba za ki gane) ta shafe jikinta har saida ta umarceta ta aga towel in ta shafe duka cinyoyinta zuwa mararta da kuma uwawunta, wata irin lallausar doguwar rigar bacci har asa ta auko mata kalar pink, pant in rigar ta fara bata ta saka sannan ta saka riga wacce ta mata as a jiki, sunkuyawa tayi ta aje mata wasu sau in silifas masu taushi sosai kalar pink ta saka, kwalli ta mi a mata tace "Shafa." a tayi ta kalli madubi ta shafa sannan ta bata farin man le e shima ta shafa, rufaffiyar alkyabba mai taushin gaske ta saka mata ta sake rufe mata kanta da rigar, zaunar da ita tayi bakin gado ta nufi aramar fridge in dake falo, tana zuwa ta bu e sanyayyar tattaciyar masarar shanu ta bata tace "Shanye duka." Da ta kar a ba dan ta shanye bane dan