Sashe 10
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shi kuma yanzu ne ma yake karatun, dan ko ya samu jarabawar nan yana da burin ci gaba da karatunshi. *Ku yi hak'uri da rashin ganin update jiya, hakan ya faru ne sakamakon wasu uzurirrika.* *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:37 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _8_ Kiran da aka mana cewa mu zo mu ci abinci ya sa Saleema fitowa daga akin bayan idar da sallah isha'i, rufe ofar akin ta yi ta fara takawa a hankali, cikin nutsuwa ta ke saukowa daga matakalar benen har ta sauko asa, za ta nufi teburin cin abincin da ta hangi mutanen gidan ta dan tsaya saboda jerawa da sukayi da Mu'az shi ma zai nufi teburin. an satar kallonshi ta yi ta gefen ido ta ta e baki, Mu'az dake kallonta ya na so ya san wacece wannan? Cikin shan- amshi da tsareta da ido yace "Sannu." Kallonshi ta yi sosai, ha en saurayi mai ilimin boko da wayewa irin ta zamani, sa kawai ta aga masa kai alamar "Kai ma sannu." Da mamakin yanda ta amsa mi shi ya bita da kallo sanda take arasawa wajen teburin, tana isa ta dan dakata tare da fa in"Ina wuninku." Alhaji Auwal ne ya fara amsawa da fara'a yace" Lafiya lau ma puce, kin sauko?" Cike da kunyar sunan da ya kirata da shi ta an jinjina kai sannan ta ja kujerar da Hajia babba ta nuna mata ta zauna. Dara-daran idonta ta aga ta kalli Mu'az da shi ma ya ja kujerar da ke fuskantarta ya zauna ya na binta da ido kamar maye, auke kai ta yi tana an gunguni ciki-ciki. Ummeeta ta kalla da suke ma ale da juna ita da Hadeeya tace "Sannu Ummee." Yatsina fuska Ummee ta yi tace "Sannu." "Abba ita ma wannan ar tonton ce?" A sanyaye sosai ta maida dubanga zuwa ga wanda ya yi maganar, wato aya she anin ne ba? Mu'awwaz ko? Ha a ido su ka yi hakan yasa ta yi saurin auke kanta, Alhaji Auwal da ke murmushi ne yace "Wai ba ka ganeta ba abokina? Mai sunan Hajia ce fa." Waro ido sosai Mu'awwaz ya yi yana kallon Saleema yace "Abba Saleema fa? Ita ce ta koma haka?" Wani mugun kallo ta aika masa cike da takaicin rashin sako hijab inta da ba ta yi ba, hakan kuma ya faru ne da tunanin doguwar riga ce jikinta kuma ban da samari ake cin abincin, murgu a masa baki tayi duba da shi kan shi fa shekara biyu zuwa uku ne ya bata, amma abu ga an hutu ya zama wani karbcece masha Allah, ka rantse ba su yi wasar asa tare ba. Hajia babba ma dake murmushi cike da dattako tace "Girman mace ai ba wuya, kai ma da ke namiji ba gashi ka ha emu wajen tsayi ba." Mu'az da ke ta kallonta yana taunar le e ne yace "Gaskiya kam, gashi ta girma...sosai." Da sauri Saleema ta kalleshi, amma sai ya dinga aiko mata da wani kallo irin na iskanci a ganinta yana kashe mata ido aya, an cire takalminshi ya yi daga afa ya zuro afar ta asan teburin ya zunguri afarta, da sauri ta jaye afar ta na waro ido ta kalleshi sosai, sake kashe mata ido ya yi hakan ya hassalata ta wurga masa harara. Hajia arama da ta mi o masa abinci amma bai kula ba ne tace "Mu'az." Da sauri ya kalleta sai kuma ya girgiza kai yace "Um um! Zan sha kayan marmarin nan kawai, kun san sun fi..." Sai kuma ya kalli Saleema yana aukar tuffa dake kusanshi sannan yace "Sun fi da i da ara lafiya ko ya ki ka ce mai sunan tsofaffi?" an bakinta tayi kamar za ta yi magana, sai kuma ta yi shiru dan bata san me yake nufi da abinda ya fa a ba. Hadeeya da kujerarta ke kusa da ta shi a angaren ce ta kalleshi tace "Yaya ka ci abinci fa, wannan ba zai ri eka ba." Kallonta yayi da fara'a a fuskarshi yace "Hadeeya ko?" Jinjina kai tayi alamar e tare da sakin murmushi, hannu ya mi a mata alamar su gaisa yana fa in "Kina lafiya?" Ba tare da tunanin komai ba ta mi a masa hannun suka gaisa, hannayen na su Saleema ta kalla sai kuma ta kalli Hadeeya, girgiza kai ta yi ta sunkuyar da kanta ta fara wasa da cokalin hannunta, babban abun takaici shine yanda ya yi haka a gaban iyayenshi amma ba wanda ya nuna ya damu. Muryar Alhaji Auwal ce ta saka ta aga kanta sanda yake fa in "Mu'awwaz idan kun kamala ka tafi da su alimentation idan akwai abunda suke da bu ata sai ku siyo." Jinjina kai Mu'awwaz yayi yace "To Abba." "Ka barshi ma ni zan kaisu." Cewar Mu'az yana ci gaba da kallon Saleema, bai san me yake ji ba a kanta ba, sai dai ya ji yana sha'awar komai na jikinta, duk da ba kyawun fuska ne da ita ba na nunawa a jarida, ba kuma jar fata gareta ba kamar an uwanta, amma dai komai na ta ya birgeshi musamman da ya fahimci ya fi sauran an uwan na ta nutsuwa da kamun kai. Wani kallo Mu'awwaz ya masa dake nuni da bai ji da in abinda Yayan na shi ya masa ba, wannan ai katse hanzari ne, ya na tunanin ya fita da an mata su shanawarsu, musamman ma Hameeda da ta fi aukar hankalinshi, sai kawai ya ce shi zai kaisu? Wallahi ba dan ya na tsoron ya yi magana ya kabta masa mari ba, da ya masa magana sai dai a yi duk wacce za'a yi. Da harara ya bi Mu'az in da ya mi e yana fa in "Ummee ina jiranku a waje." Saida ya ara matsowa kusan Saleema ya ora hannayenshi a kan teburin ya sunkuyo sosai kamar zai sumbaceta, jaye fuskarta tayi daga kallonshi tana yatsina fuska cike da kunya, duka mutanen kallonsu suke, su Hadeeya mamakin yanda ya ke ma Saleemar su ke, ko bai gane ita in ba mai aji ba ce? Yayin da amarya ta ke ta e baki da tunanin " an iska kawai, a gaban mutane ma sai ya nuna halin iskancin da tamba ewa." Hajia babba kuma murmushi take a ran ta tana ayyana "In har Saleema za ta zama alkairi gareka zan fi kowa farin ciki." Dan kuwa ta fi kowa sanin anta, ba ta ta a ganin ya wa mace haka ba, shi Alhaji Auwal kuma murmushi kawai ya ke saki a fuskarshi, ko ba komai an Alhaji Yusuf za su ji da in zama gidan. Cikin sanyin murya Mu'az yace mata" Ina jiranki, ki fito da wuri." Juyawa ya yi kawai ya fice a falon, kasa aga kanta tayi bare ta kalli mutanen wurin, sai da ta ji sun maida hankulansu kan abincin sannan ta ago ta kalli Alhaji Auwal, cikin taushin murya da ladabi tace" Am! Abba." Cike da kulawa ya kalleta yace" Na'am ata." A sanyaye tace" Ina ganin su tafi kawai, ni zan zauna a gida." Da mamaki a fuskarshi yace" Me yasa? Ke ba kya bu atar komai ne?" aga kai tayi alamar e, wata harara Hadeeya ta jefo mata cike da takaicin me yasa wau ita take da kidahumanci ne? Ku i ne fa za'a kashe musu, auke kai ta yi cike da ba in ciki, Saleema kuma da ta kula da kallon ba ta biyata ba bare ta samu damar fa a mata wata maganar marar da Hameeda a da saida ta harari Saleema cike da rashin kunya tace "Abba ka yaleta ita dama haka take, mu za mu je mu siyo abinda mu ke so." Kallon Hameeda ya yi da mamakin yanda ta ke magana akan Yayarta haka, shi fa duk bokonshi da iskancinshi ya na so ya ga arami na girmama babba, girman da ubansu ya ke bashi ne matsayinshi na wanda ke sama da shi a komai ya sa suke kamar abokai, ko Mu'awwaz da ke namiji bai yarda ya raina Mu'az ba tunda ya na gaba da shi, bare ita wannan da ba ita ke bi ma Saleema ba. auke kai kawai ya yi da tunanin idan ya ara ganin haka zai tsawatar mata, dan sam ba ya lamuntar irin haka. Shigowar wata matashiyar yarinya da ba za ta wyce tsarar Hameeda ba yasa Saleema kallon ofar, Alhaji Auwal ma cike da kulawa ya kalleta yace "Kin kai musu abincinsu?" A ladabce yarinyar da sai yanzu Saleema ta fahimci ar aiki ce tace "E Alhaji na kai musu, sun tafi masallaci ma sai da na jirasu." Jinjina kai ya yi yace "To da kyau, kin gama aikin ki ne yanzu?" Cikin ladabi tana ta rarraba ido tsakanin Alhaji Auwal in da kuma amaryar sa da ke binta da kallon yama a an tsorace ta amsa da "E na idar." "Shikenan za ki iya tafiya." Ya fa a yana ci gaba da cin abincin shi, tsaf Saleema ta kula da inda yarinyar ta kalla a matu ar tsorace, a hankali ta yallara idonta ta kalli inda idon yarinyar ke kallo. Karaf! Idonta suka sauka kan Mu'awwaz da ke ta ma yarinyar signa da ido, da sauri Saleema ta sake kallon yarinyar ta ga ta juya ta fita, ta e baki kawai ta yi da tunanin wannan shi ne abinda Mamanta ta fa a cewa Mu'awwaz ya cika tsantseni, wato shigar da ke jikin yarinyar ya ke yamata? A karo na biyu sake ta e baki ta yi ta auki cokalinta za ta ci gaba da cin abinci, Mu'awwaz ta ga ya mi e ya na fa in "Na oshi." Kallonshi amarya tayi tace "Bebe, ba ki ci sosai ba fa?" Ba tare da ya ko kalleta ba ya kama hanyar fita ya na aukar tuffa aya yace "Ya isheni." Da kallo Saleema ta bishi mamaki ya lullu e na tunanin wai su mutanen nan ba sa jin kunyar kiran kowa Bebe ne? Haka matar Babansu ma take kiran ubansu Bebe, sai ka ce wani an goye. Su