← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 116

Sashe 66

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuma tace "Amma karka damu, ko gobe ma ta fara zuwa, tunda ai shi ya ce bani ba zuwa wajen koyon inki ne, kaga sai na koya kamar yadda na yi karatuna." Kamar kuma wacce aka ragewa sauti sai ta sauke numfashi tace "Kashhh! Dan Allah ka tayani addu'a mahaifina ya fahimceni." A sanyaye sosai Huzeifa daya kasa kunne yana saurarenta cike da tausayi yace "Ana samun irin haka dama a wajen iyayenmu, sau da dama iyayenmu suna aukar burikanmu a matsayin zubar mutumcinsu ko kuma anci a garemu, da fari ki bi maganar mahaifinki, sai dai ki sani abinda kikayi na karatu yayi daidai, dan babu biyayya ga ababen halitta wajen sa awa mahalicci, a nan kuma zamuyi duba da yadda kika auki burinki, da kuma yadda ake neman tauyeki, da fari idan mukayi duba da rayuwarki ta yanzu zamu iya cewa akwai cutarwa a ciki, kiyi ha uri idan baki ji da in abinda na fa a ba, amma hanaki zuwa makarantar boko, sannan an hanaki zuwa ta islamiyya tun tsawon lokaci, burin da kike da shi ma a hanaki fuskantarsa, anya kuwa hakan ba yana nufin ci gaban rayuwarki ne ba'a so ba? Idan kuma ana ganin ana yi ne dan martabarki, ina ganin babban gatan da za'a miki shine a barki da za inki, *Saleemah*, rayuwarki taki ce, ke ya kamata ki tashi dan ingantata, idan baki mata komai da zai sa ta gyaru a yanzu ba, to fa bayan kin sake shiga hannun wani mai iko dake, ba lallai ki iya wata hwan asawa ba, dan kusan duk maza tunaninmu iri aya ne. Da wannan nake shawartarki ki daure ki fara koyon inkin nan, idan Allah ya dafa miki watarana mahaifinki alfahari zaiyi da ke, ina tabbatar miki sai ya zubar da hawayen farin cikin ganinki a inda bai yi tsammani ba, kuma ta dalilin inki kika samu hakan." A sanyaye sosai kamar mai ra a ya sake cewa" Ki warara kanki, zamanki a gida ba karatu ba aiki shine babban tazgaron da zai ruguza rayuwarki, mahaifinki bai fahimci haka bane, idan kuma ya fahimta bai auki mataki bane kamar dai yadda mafi yawan lokuta iyayenmu su suke oramu a hanyar da bata illewa da tunaninsu ita cigabanmu." an da ile yace" Kiyi shawara da mahaifiyarki, sannan kiyi tunanin rayuwarki ta gaba." Sosai maganganunshi suka ratsa Saleema, jiki a mace ta lumshe idanu tace" To, nagode sosai." Da haka sukayi sallama, ba ta kuma oyewa mahaifiyarta ba saida ta sanar da ita komai, sai dai wannan karan abinda ya fito daga bakin Maman nata shine" To, Allah yasa alkairi, amma fa ki sani babu ruwana idan ta kwa e, dan ni dai Allah na gani nayi iya arina na hanaki amma kin i fahimta, ba zan hanaki ba dan wata ila anan abincinki yake, amma idan mahaifinki ya gane ba hannuna a ciki." Daga wannan rana Saleema ta fara kar an horo a hannun Fareeda na, ta kan zo sau uku a sati, ranar litinin, alhamis da kuma juma'a, duka ranaku ne da Fareeda ba ta zuwa islamiyya da rana, dake kuma Saleema ta ware a irin haka tamkar dai yadda ta samu karatunta na boko a oye, haka yanzu ma take koyon aikinta cike da zala a da son abun a ranta sa kuma za uwa, hakan ya sa Fareeda kullum da mamaki take komawa gida, dan yadda ta na nuna lata take hardacewa, da yadda yanka abu komai wuyarsa baya mata wahala sai take jinjina lamarin har tayi tunanin ko dai tana da aljanu a kanta ne da suke sakata warewa lokaci aya. Shi kanshi Huzeifa da take zuwa yana ora mata duk ranar lahadi mamakin take bashi, har wasu lokuta ya zuba mata idanu yana kallo, idan ta zo ko awa bata yi take komawa, dan kuwa arara Huzeifa ke nuna jin haushin kasancewarta a shagon sanda ke da kwai maza a ciki, sai ya yi ta ha e rai yana harare harare, sau inta aya tana da saurin fahimta ba ta jimawa, sannan kullum da hijabinta take mai hannu wanda ko hannayenta ba sa fitowa waje. *Yau* ma kamar sauran lahadin zuba mata idanu yayi da mamakin ya zata raina masa hankali haka? Irin fa yankan da shi kanshi bai fi watanni da koya a wajen wani babban ma inki dake Kano take cewa ya koya mata, ban da rigila yaushe ta fara koyon da za ta jawo wannan babban aiki? Gyara tsayuwarsa yayi ya nunota da almakashin hannunshi yace "Kinga, idan ba koyon kika zo ba yau ki tafi gida kiyi bacci, ni ina da ayuka da dama." Ba alamar wasa tace "Wallahi koyo na zo, ka koya min malam, idan na ga da wahala saina ha ura a gaba na koya." A kausashe yace "Kinga ba zai yiwu ba, idan ata lokacin kike so muyi a shirme kinga kayan can, auki fara ha emin su, anjima mai su za ta zo kar Cike da rigima ta rumgume hannaye tace "Ban iya taka tela ba." Da wani kallon mamaki ya bita da tunanin yau bala'i take so su yi, kuma daidai yake da ita shi ma, banda haka taka tela fa shi dai a saninshi a wuni aya ta koya kuma ko ar gajiyar nan da wasu ke mita ma shi dai bai ji ta yi ba, kai a halin da ake ciki yanzu shi bai shakkar bata inki na aya daga cikin shahararrun matan dake kawo masa, a dai yanda zahirin ya nuna ya san yarinyar nan za ta iya, tunda yana bata yanka ta je da shi gida tayi ta kawo masa duk da masu sau i yake bata. Dade ugu yayi yace "Kinga, ina rabaki da tsokanata, dan Allah muyi abinda ke gabanmu." Wani farrr ta masa da idanu ta murgu a baki tace "Na ce fa ban iya ba, to ni baiwarka ce da zaka sani aikin nan? Bayan na ce ka koya min yanka inkin da ake yayi yanzu, sai ka ga mace ta sa riga duk tattarar tayi sama tamkar an saka mata afara gwanin sha'awa, shine zaka ce wai ba yanzu ba." Da ma aukakin mamaki ya nuna kanshi yace" Ke! Wai ni kike ma wannan kayan?" Jujjuyawa ya fara yi yana neman abun awon da zai bata su fara koyon dan ya ga iya gudun ruwanta, ta auka abun bugu yake nema da gudu ta fita a shagon ta tsallaka titi da sassarfa ta shige gidansu tana yala dariya. Ri e ha a yayi yana kallonta, sau kuma ya saki murmushi yana girgiza kai, wato ka samu macen da za ta san ita macen ce ma rahama ne, duk buhun acin ran da zai fito da shi daga gidan can inda aka ce lahadi ya zo shagon nan to an gama, dan tsaf yarinyar ke orashi ta hanyar hassalashi sannan daga arshe ta mayar da sakarai, yanzu nan na tafi kenan sai kuma ta tashi tafiya ta shigo ta masa sai anjima. Da irin haka take ci gaba da ara warexa a abinda ta saka gaba, yanzu haka ta ulla awance da wayarta saboda dabarun da Huzeifa ya sake nuna mata, kullum cikin bibiyar rayuwar ma inka take da kuma kallon sanfiri na salon inkuna daban daban, a haka har yanzu ta kan siyi atamfa dan ta inkawa kanta, kuma bata ta a nunawa Huzeifa ya ce bai yi ba saidai ya arfafa mata gwiwa, idan tana son yin mai wahala ne wanda hannunta bai gama fa awa ba sai ta zo shagon ta yanka gabanshi ya gyara mata wasu abubuwan, da haka har ranar ta matsawa Mamanta ta bata atamfarta aya a cikin wanda zatayi shigar biki ta kai shagon ta inke ta kawo mata. Tayi farin cikin ganin inki sosai da mamakin ita ta yi har da wala, dan duk da zaka iya an koyo yayi amma a lokacin da ta fara gaskiya dole a jinjina mata. Duk shagalin nan da aka yi Alhaji Yusuf bai da labari kamar sauran lokuta, dan kuwa lokacin da Fareeda ke zuwa gidan baya nan, ita kuma da take fita duk lahadi baya wani zarginta tunda satin na iya kamawa ya are bata fita ba sai lahadin kawai, wani lokacin kuma yana ma bacci za ta fita har ta dawo bai fito cikin iyalin ba bare ya san me ke faruwa, Hameeda ce hankalinshi ya fi karkata kanta dan ita ce ta fi yawan fita yawon biki da gidajen awayen, rashin yawo sosai ya taimaki Saleema daga kauda idanun mahaifinta a kanta har yanzun ta fara jiyo amshin cikar burinta. *Bayan Wata Uku* Tunda ta shigo akin asibitin take ha e fuska da yatsina baki, kallon Alhaji Yusuf take kamar ta wanwaka masa mari, da alama ma ya tare asibitin ne shima, kwanansu biyu yau a asibiti Safiya na na uda, gashi yau aka ce za'a mata tiyata da yamma dan ciro abinda ke cikinta, dan kumburi tayi sosai da yar take motsa jikinta ma, tunda suka zo asibitin ita dai sau aya ma ta ganshi gidan shi ma a gaggauce. Yanzu haka gashi nan ba kunyar mutanen d ake akin yayi wani zama gaban Safiyar kamar mai ro onta gafara sai tattausa mata afafunta yake da suka zama sumtuma sumtuma, wato duk son ta haifa masa namiji ne ya kawo haka? To sai me? Ita ma ta na son cikin nan dan dai tana duba cikas in da yake kawo mata a aikinta ne, amma ko yanzu ta ga dama za ta iya samu ita ma. Saleema da ta gama salla ne ta kalli auntyn nata tace "Aunty ina wuni." Yatsina baki tayi tace "Lafiya, ya mai jikin?" Da fara'a ta amsa da "Sau Juyawa Alhaji Yusuf yayi ya kalleta yace "Saleema zo ki zuba wa mamanki abinci." A wahalce Safiya dake ta kanta ta girgiza masa kai, bakinta ta motsa da yar tace "Um um, ba yanzu ba." Kallonta yayi yace "Na'am." yar muryar ta ta ke fita, dan haka da ta sake maimaitawa bai ji ba, agawa yayi ka an ya kai kunnenshi kusan bakinta yace "Ban ji ba." A wahalce tace "Ba yanzu ba." Da rashin jin da i ya kalleta yace "Za ki ci anjima?" aga kai kawai tayi
Chapter 66 · 0% Book details