Sashe 51
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kinsha wahalar gidan aure ne, kin bautawa ubangiji da dukkan arfi, sannan kina bauta masa ba wai dan haka al'adarku take ba ko kuma kin ga iyayenki na yi ba, kina yi dan kinsan ha in abun ne, a ganina ki ara sanin waye shi, dan gaskiya..." Irin kallon da Saleema ke mata yasa ta an yin shiru, da ta ga ta yale kuma sai tace" Ci gaba mana." Sinne kai tayi tace" A gaskiya ina zargin kamar akwai wata ala a tsakaninshi da anwarki Hadeeya, a gabana ranar na ji suna magana akan so da kuma wani abu da ni dai ban gane ba, amma dan Allah ki ara bincike akan shi, ban fa a miki haka dan na rabaki da wanda kike so ba, sai dai zan so kiyi rayuwa a gidanki fiye da yadda mahaifiyarki take a gidan nan, duk irin matsalolin da mahaifiyarki ke fuskanta bata fuskantar matsalar wula anci da cin zarafi, a alla ki rayu fiye da ita." Tana gama fa a mata ta ci gaba da aikinta, rasa yanayin da ta shiga ta yi, a gaskiya wani yanayi take ji shi ba farin ciki ba haka kuma ba unci ba, sai kawai ta kalli mai aikin tace" Nagode miki." Ficewa tayi daga madafar dan kai masa ruwan, tana isa ne ta sameshi tare da Hadeeya ya ci kwalarta tamkar wanda zasu dambatu da junansu, sakin gorar ruwan da kofin tagaran in tayi suka fa i tare, inda kofin ya fashe tasss! A asa, da sauri ta tako garesu ganin bai yi niyyar sakin Hadeeyar ba, tabbas ta hango acin rai da tafasar zuci a tare da shi, kuma ta san koma me suka tattauna ba alkairi bane, hakan yasa ta shiga mawuyacin halin me ye ha inshi da ita da har za ta kaisu ga haka ba. Tana zuwa abinda bata ta a kwatanta yi bane ta yi, wato ta ora hannayenta biyu kan duka hannayenshi ta ri e ta kalleshi da yanayi na sanyin murya da nutsuwa tace "... *Dan Allah idan kuka ga ban amsa muku comment ba kar kuyi hushi, uzurirrika ne dayawa wallahi, ga sabgogin gabana ga kuma awainiyar gida, sannan ga burin faranta muku, idan na ce zan tsaya amsa comment ma lokaci na musamman yake bu ata, da hakan kuma zai fi a ora muku rubutun shafi na gaba, ko ya kuka gani? Amma ku sani wallahi duk wanda yayi comment inshi ina gani kuma ina karantawa, sannan shi yake sake bani arfin gwiwa, nagode muku mutane na.* *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:50 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _30_ Kallonshi tayi da yanayi na sanyin murya da nutsuwa tamkar ba abinda ke neman aga mata hankali tace "Dan Allah saketa, dan Allah?" Saida ya kalli fuskarta sannan ya jaye hannayenshi a wuyan Hadeeya, da gudu ta juya ta barsu tsaye tana fashewa da kuka, kasa fuskantarta yayi bare ya kalleta, kanshi sadde asa yana ta rarraba idanu da alamar kunyar ha a idanu yake da ita, murmushi tayi mai sautin da har saida ya jiyosa yayi saurin aga kai ya kalleta da mamaki, matsawa tayi kusanshi ta fuskanceshi da kyau tace " *Mu'az*, akwai wani tsakaninka da Hadeeya ko?" Da yanayin rashin jin da in amsar ya sake kallonta ya marairaice yace "Saleema ak..." Da sauri ta katseshi da "Dan Allah, ka fa a min gaskiya, Yaya Mu'az ban ta a so ba sai a kanka, ba wanda ya ta a ce min yana sona sai kai, ban ta a samun wanda ya nuna min soyayya ba sama da kai..." Rau-rau tayi da idanunta da suka cika da hawaye ta langa ar da kanta da muryar kuka tace" Dan Allah ka fa amin gaskiya, ka fa amin abinda idan kunnuwana suka ji zuciyata ba zata tsaya ba." Duk da kanshi fuskarta yake kallo amma idanunshi asa suke kallo, cikin rawar murya kamar sai fashe da kuka yace" Saleema laifina ne, na fa a miki komai a kaina, bansan me ya shiga kaina ba a waccen lokacin, na dinga fa awa Hadeeya ina sonta har na dinga ta a jikinta, shine yanzu take cewa ita ma tana sona, bansan ya zanyi ba Saleema." Lumshe idanunta tayi hawayen da suka taru suka ziraro mata, kallonshi tayi tace" Mu'az, ka min al awarin zaka daina fa, me yasa baka sona? Me yasa ba ka kishina?" A gigice ya ago kamar wanda ta zagi iyayensa ya ura mata idanu, da sauri ya girgiza kai yana an matsowa kusa da ita yace" Na rantse da Allah Saleema ina sonki, wallahi kishinki yasa babu abinda zan shirya a bikin nan, Saleema dan ba'a son kowa ya ganki ma ni ka ai zan shiga gidana, Saleema ni kaina wasu lokuta ina tunanin ta yadda zan rayu da ke da wannan kishin?" Murmushin ya e tayi tace" Da kana so na Mu'az da baka sake ta a kowace mace ba bayan ha uwarmu, anya ka ta a tuna cewa zina bashi ce?" A rikice ya sake zuba mata idanu, girgiza kai tayi a hankali ta ora da" Ba hadisi bane da aka ce duk abinda kayi shi za'ayi maka, sai dai magana ce ta magabatanmu kuma sai tayi daidai da shari'a, tabbas abinda ka yi shi za'ayi maka, zina kuma bashi ce, idan har ka ci komai daran da ewa sai ka biya, in ma kai da kanka ko kuma iyalinka, wannan iyalinka naka sun ha a da * anwarka*, *Yayarka*, *Auntynka*, *Goggonka*, *matarka* ko kuma * arka*." ura masa idanu tayi sosai tace" Mu'az, ya za ka ji a ranka idan aka ce *ni ce* zan biya wannan bashin da ka auka? Wane hali za ka shiga idan aka ce * armu* da ba ta san hawa ba bare sauka ce za ta biya kuskuren mahaifinta na baya? Dole dai zamu biyashi, inma ta da in rai ko ta fin arfi..." Fashewa tayi da kuka mai tsuma zuciya matu a ta dur ushe tare da ha e hannayenta alamar ro o tace" Dan Allah na ro eka ka dakata, ka daina kallon ar kowa da idon rashin a'a, na ji zan aureka a haka amma dan Allah ka daina." agowa tayi ta nuna kanta ta hanyar ora tafin hannunta kan irjinta tace" Na ji ni zan biya bashin, zan biya amma ba anmu, dan Allah ka dakata haka." "Ahhhhhhhh!" Ta saki arasa sakamakon ganin Mu'az ya timi a asa, a haukace ta rarrafa ta matsa kusanshi tana kallonshi kwance tamkar baya da rai, a gigice ta sake furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Abba, Abba..." Da gudu ta mi e ta nufi hanyar falon Abbansu, karo suka ci dan kiran da take masa ne ya sa shi fitowa a ru e, a gigice ta shiga nuna masa inda ta baroshi tana fa in "Abba Yaya Mu'az ne, Yaya Mu'az ya fa i, ina ga fa suma yayi." Da gudu gudu ya ra ata ya wuce yana fa in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Me ya sameshi to? Dama bashi da lafiya ne?" Da gudu ta biyo bayanshi, suna zuwa yanda ta barshi haka ta sameshi, jijjigashi ya fara yi amma shiru, walawa mai gadi kira yayi da gudu ya araso, ruwa da tunda ta auko ta saki asa ya dauko aka shafa mishi, saida aka shafa sau uku yayi wani arfan numfashi, a hankali ya fara bu a idanunshi har ya fara kallonsu aya bayan aya. Murmushin dake kan fuskarta ya ara dubawa, sai kuma ya lumshe idanu yana sauraro maganganunta a kanshi, inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!!! Da sauri ya yun ura ya tashi zaune yana sadda kanshi asa, arin mi ewa yayi Abba ya ri eshi yace "Zauna, tayiwu jiri ne ya kwasheka fa." Girgiza kai yayi a hankali yace "Abba zan je gida, bana jin da i ne." ewa yayi tsaye ya kamashi yace "Muje to, sai na ajeka da kaina." Girgiza kai yayi yace "A'a Abba da ka..." aga masa hannu yayi yace "Muje kawai." Makulin motar Mu'az in ya kar a ya nufi motar, Saleema dake binsu a baya kallon Mu'az in tayi cike da damuwa tace "Yaya Mu'az kana lafiya? Me yake maka ciwo? Ku je asibiti mana." A kunyace ya girgiza mata kai kawai amma bai yarda sun ha a ido ba, har ya shiga motar mahaifinta ya ja shi bai kalleta ba, hakan bai dameta ba a ganinta ciwon da ya sumar da shi ne, haka ta juyo ta dawo gidan ba tare da iyayensu matan sun san me ya faru na dan kowace na akinta, idan ana falo ne dama ake iya jin abinda ke faruwa waje shima idan bai yi nisa ba. Ko da suka isa gidan a galabaice ya shiga dan wani mugun ciwon kai ne ya rufeshi ga kuma ciwon da jikinshi ya auka na fa uwar da ya yi ba tare da ya shirya ba, da yar sukayi sallama da Abban Saleema ya shiga ciki, bai san ta ya ya koma na shi gidan ba dan bai jira ganin tafiyarsa ba. Kai tsaye akinshi ya wuce, Ummee da ta ga shigarshi ne ta sanarwa da Hajia Rabi. anin lokaci hankalin kowa ya dawo kan Mu'az, har Mu'awwaz da a lokacin yake aki ya balbale Nafissa da masifa kan ba zata ara ri e waya ba, dan shi sam hankalinshi baya kwantawa da duk wani motsinta, fitowa yayi shima ya shiga akin na Mu'az da kowa ke can ana ta fama yi masa sannu, sai Alhaji Auwal daya shigo bayan kiran da Alhaji Yusuf in ya masa ya fa a masa abinda ya faru a gidan. Idanunshi a rufe ya laluba yana son kama hannun mahaifiyarshi yana fa in "Mama, Mama kina ina?" Da sauri ta ri o hannayenshi tace "Gani, gani Mu'az, me kake so?" A jigace yace "Bacci, bacci nake so nayi Mama dan na farka a mummunan mafarkin nan." Cike da tausayawa da tunanin abinda ya sameshi haka tace "Mu'az ba mafarki kake yi ba, ka bu a idanunka ka fa a min me ya faru?" Alhaji Auwal ne ya dafa