← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 116

Sashe 88

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shiga jikinki, idan bakiyi sannu ba za'a dinga tuntu arki rayuwarki ko zamanki da mai gidanki, ta haka kuma za'a samu ofar da za'a shiga a cutar daku." Numfasawa tayi tace" Na biyu kuma shine, ba kowa ne dake miki dariya ba kema zaki yage masa baki, wani dariyarsa iya la ansa ne kawai, Saleema a cikin mutane sama da ari da zaki zauna da su, bai fi kaso talatin ba da zaki iya samun dariyar gaskiya daga garesu ba, sauran duk za'a miki ne dan kawai ba yadda zasuyi, idan kika zama mai lura da saka idanu zaki fahimci haka, amma sai kin zama mai takatsantsan da lamarin kowa a gidan nan, abu na arshe da zan fa amiki shine..." Numfashi ta ja ta sauke sannan tace" Kada ki zama mai bawa hadiman gidan nan yarda akan abinda ya shafeki da kula wanda ya shafi sarkinki, bakinki da su ya zama abinda kawai su ne zasu iya yi miki, amma in dai zaki iya da kanki to kiyi, Saleema... *kada ki yarda hadimai ne zasu gyara miki makwancinki*, bawai zan hanaki hutawa ba ko hanaki kiyi ikonki yadda ya dace a matsayinki na *matar sarki*, amma dai a nan kusa ya kamata ki zama mai kula sosai, domin kuwa nima na yi irin wannan sakacin, wanda shi ya kaini ga halin da muka samu kanmu a ciki har ya zama silar shigowarki rayuwarmu..." an tsagaitawa tayi kafin tace" Ruwan wankansa, takalmin afarsa, da ku in da suka fito daga gareshi, da su aka ha a aka masa sihirin da ya fi shekara takwas dashi a jiki..." Hawaye ne suka wanke mata fuska tasa hannu tana sharewa tana ci gaba da fa in" Ba dan iyayena masu hali bane, da mun yi bara saboda larurar *Abdus-samad* sai da na dinga siyan da kadarori dan na sama mishi lafiya, ba dan Allah ya azurtamu da ka autashi shi ka ai ba, da mun yi shirka kamar yadda wasu malaman ke nuna mana sai ta hakane zai samu lafiya, shiyasa na auki lamarinki da mahimmanci Saleema, shekarun da aka auka da ku en da aka kashe, ashe maganin na nan kusa da mu ga wata yarinyar da ba wanda ya santa...abun al'ajabi." Sake ri e hannayenta tayi sosai tace" Ki zama mai kula akan komai Saleema, dan wannan mulkin da kika gani wasu a shirye suke da su *raba mijinki da rayuwarsa* ma." A tsorace Saleema ta kalleta, ha a maganganunta sun shigeta sosai kuma ta auki aniyar kiyayewa, sai dai maganar rasa rayuwar nan yasa ta jin fa uwar gaba har ta fara hasasho idan fa hakan ta faru da gaske? Idan fa aka yi nasara a kansu kenan? Za ta zama mai *takabarsa* kenan? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Ta ambata a ranta, wane wace irin rayuwa ce? Me ye a mulkin da za'a so raba wani da ransa saboda shi? Sosai ta shiga ru ani da kuma tsoron zaman gidan, dan gaba aya ji take tamkar ko numfashinta da zai fito daga ruhinta akan idanun wasu zia sauka tsabar saka ido, tsoro matu a ta ji ya kamata har ta gagara tashi ta koma inda take, ji take ma kamar ba lallai ta kai angaren na ta ba. an rikice Saleema ta kalleta tace " *Umma*, to a ina suke cin abinci?" Da rashin fahimtar kalamanta tace "Su wai? Kowa a angarensa, sai dai wasu lokuta mu kan ha u gaba aya a ci abinci, kuma haka tun mai martaba yana raye ne, har yanzu bamu daina ba, sai dai ba wani shau i a wajen cin abincin." Saida ta ji ta dasa aya sannan tace "Su nake nufi, yalla ai mai martaba." Kallon tsanake ta mata cike da jin ta birgeta, ashe fa Abdus-samad take nufi da su, hakan ya birgeta sosai, kuma duk da ba amsar tambayarta ta bata ba, bata katse mata numfashinta ba saida ta dire maganar sannan, hakan girmamawa ne daya samo asali daga lafiyayyar tarbiya, murmushi ta mata tace "Daga aramar madafa ake fidda mana abincinmu tare da na shi." Jinjina kai Saleema tayi tace "Nagode Umma, kuma in sha Allah zan kiyaye duk abinda kika fa amin." Sakin hannayenta tayi tana fara'a tace "Nagode *sarauniyata*, za ki iya tafiya angarenki." Jinjina kai tayi ta mi e a hankali, da sauri ta mi e tsaye ita ma tana sake ri e hannayenta tace "Uhyemmm! Kuma kina ji, Saleema ana ba waliyi bane bare na ce ba zai miki ba daidai ba, saidai duk yadda ranki zai ace game da shi idan ya miki ba daidai ba, dan na ro eki kada ki bari wasu su fahimci sa aninku, zaki iya hushinki a aki dan kema ar adam ce, amma da kin fito waje ki nunawa kowa lafiya lau kuke zaune ta hanyar sakin walwalar fuskarki, dan kuwa sanin sa anin naku shi zai bada damar da wasu zasu shiga tsakani dan a farra Murmushi Saleema tayi tace" In sha Allah Umma, zan kiyaye." Da fara'a a fuskarta tace" Allah ya miki albarka." "Ameen." Ta fa a tana rusunawa sannan ta juya ta ofar da suka shigo ta nan ta bi dan ta hakane za ta iya gane na ta angaren. *Alhamdulillah.* 20/06/2022 22:08 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _47_ Jakadiyar dake gabanta ta kalla a nutse bayan ta aje littafinta tace "Madafa nake son shiga, za ki iya yi min jagora?" Rusunawa ta sake yi tace "Yadda kike so uwargijiyata." A nutse ta mi e tsaye hakan yasa jakadiyar take mata baya, daga nan take nuna mata hanyar har suka isa madafar, ba kowa a ciki dan lokacin girkin rana bai yi ba, kula an riga da an gama na safe, hakan yasa Saleema kallonta tace" Ko zan iya ganin wa anda suke iya shigowa madafar nan?" Rusunawa tayi tace" To ranki shi da Gaban wayar tangarahon dake ajiye ta arasa, Saleema na kallonta tayi kira ta kuma fa i ta aitacc in kalmomi cewa su shigo madafa sarauniya na son ganin masu ruwa da tsaki a madafar, bayan ta aje wayar da kamar sakkani talatin mace uku namiji aya suka shigo. are musu kallo tayi ta nunasu tace "Ku ka ai ne a gidan nan ke iya shigowa nan?" aga kawunansu sukayi suka amsa da "E, ranki shi da Matse bakinta tayi ta zama irin ba wasar nan sannan tace "Ku kuke dafa abincin da gimbiyoyi ke ci kenan?" Wata babba a cikinsu ce tace "E ranki shi da e, yanzu kula hada na sarki ma." " *To ya isa.*" Saleema ta fa a tana juyar da kanta gefe, duk tsura mata idanu sukayi suna kallo, a hankali ta sake kallon inda suke tace "Daga yanzu abincin masu gidan kawai zaku dinga dafawa, amma banda na *sarkina*, ni zan dinga shigowa madafar ina girka masa da hannayena." A da ile ta furta "Kun fahimta?" Kallon juna sukayi jin wani sabon tsari, su fa shiyasa lamarin sarautar na yanzu ma ke basu haushi, kawai yara ne an boko ke mulkarsu, a sai ance suka aga kawunansu suka ce "E ranki shi da Jakadiyarta ce ta an matso kusanta ta ra a mata "Ranki shi da e, ba girmanki bane shiga madafa bayan ga mu, ki umarcemu da komai kike so a dafa za mu iya." aga mata hannu tayi tace "Ba bu ata, ni aura ba ku ba, akan me ku ne za ku kula da abincinsa?" Maida dubanta tayi ga masu girkin tace "Zan iya samun makulli nima?" Da sauri namijin nan ya laluba aljihunshi hannaye na mishi rawa ya ciro ya mi o mata, yadda hannayenshi ke rawa da ru ewar da yayi har ya mi o mata makullaye dayawa haka yasa ta kallonshi sosai in nan, da sauri ya shiga cire waya aya sannan ya mi o mata, an waiga kanta tayi ka an inda jakadiyarta take, hakan yasa ta saurin kar an makullin, a hankali ta fara takawa za su bar madafar. Saida ta kai bakin ofa ta juyo a nutse ta sake kallonshi ta nunoshi da yatsa tace "Ga bata makullayen, daga yanzu ita ce me alhakin bu ewa da rufewa." Wacce ta nuna suka kalla wato matar nan da ta fi su shekaru, ura mata idanu yayi kamar dai yana son arin bayani, hakan yasa Saleema aga girarta aya ta masa kallon "Me ye?" Da sauri ya kalli matar ya bata makullayen ya sunkuyar da kanshi asa, rusunawa matar tayi tace "Nagode ranki shi da Kallon ki shiga taitayinki ta mata tace "Ba haka kawai na dam a miki ba, sanin wanda ya shiga da wanda ya fita ne aikinki, ya zama duk wanda zai shigo nan to da saninki." Jinjina kai tayi tace "Angama uwargijiyata." Ficewa tayi a madafar ta barsu da zulumi da kuma tunanin me ye haka? Suna fita daga ciki matashin nan kai tsaye angaren gimbiya Kubra ya wuce. Ba wanda ya masa shamaki da shiga angaren har cikin falonta, dake tana waya sadda ya shigo, hakanne ya sa ta tashi ta shige aramin falon tana sauraren an-galadima da yace "Ranki shi da e, yanzu haka gani gaban malam na sake dawowa, ya ce na baki za ku yi magana." A nutse tace "Uhum!" Bakin gado ta zauna tana kallon kanta a madubi, inda malamin ke magana ta wayar yana fa in "Allah ya taimaki gimbiya, uwar marayu gatan marasa gata, ranki shi da e aiki fa ya tunkaroku." Yatsina fuska tayi ta kya e baki tace "Muje ga gundarin magana." Ci gaba yayi da fa in "Ranki shi da e tun da aka aura aure da an-galadima ya zo min da bayani nake aiki akan lamarin nan, wallahi ranki shi da e yarinyar nan *ba yadda zamuyi da ita*." Da yanayin jin haushi tace "Kamar ya? Ita ta halicci kanta ne? Aljana ce ita? Ko mala'ika?" A nutse yace "Ba ko aya ranki shi da e, sai dai *baiwar Allah ce* ta gari kamar sauran salihan bayi, gimbiya! Duk wani ulunbotona da arina akan yarinyar nan mun rasa hanyar da zamu tarwatsa
Chapter 88 · 0% Book details