← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 116

Sashe 47

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mugun hassale ya tashi ya fito daga akin, bai bi ta kan wan anda ke zaune ba ya shiga motarshi ya bar wurin ranshi in yayi dubu to duka a ace yake, tu i yake na garari da rufewar idanu, ya auki minti talatin kafin ya iso dan suna nesa sosai, a hakan ma wai dan yana gudu na bala'i wanda tsaikon cunkuso ka ai ke dakatar dashi. *Ta fito* daga madafa kenan auke da kwanon miyar taushen da ta yi, bakinta har kunne tsabar farin ciki, a ganinta yau mahaifinta zai amince da burinta, dan nuna murnarta ma yasa ta sarrafa masa wainar nan ta shinkafa da hannayenta da kuma yin miyar taushe wacce mahaifiyarta ta ga tana yi kuma ta fa a mata yana sonta sosai. Tana kusa da isa teburin dan aje kwanon ba ta ji shogowar ba dan ofar ita ta bu eta gaba aya saboda tana yawan shiga da fita sanda take aikin, ofar kuma akwai an nauyi sai ka saka himma take bu ewa, hakan yasa ba ta ankara da shigowarshi ba saida ta ji tako gaf da ita ne ta an kalli aren na ta na dama dan ganin waye? Wani sardaunan mari da ya kifa mata ne yasa ta walla arar da take duk wanda ke gidan ya ji ga kuma fa uwar kwanon miyar da wajen zubawar ma na musamman tayi ya fa asa miyar ta watse, zabura tayi ta ja baya sanda miyar ta zube ta sake waigawa dan ganin me ya samu mahaifin na ta? Amma da wani irin yanayi na mugunta ua dam i dun ulallen gashinta data tumke tsakiyar kai da ribom ya nemi janta zuwa akin mahaifiyarta. A razane sosai ta dur ushe ta ri afarshi ta fashe da kuka tana fa in "Abba, Abba...ka yi ha uri Dan Allah, Abba ban maka komai ba wallahi, ka yi ha uri Abba ka yafe min." Sakin gashin na ta yayi ganin ta cije wuri aya, da aya hannunshi ya sake gaura mata mari daidai lokacin da mai aiki ta danno da gudu tare da Safiya da ta taho a hankali dan tana kiuaye jijjiga jikinta kamar yadda likita ya fa a mata, ganin Saleema dur ushe yasa ta ago afa ta shigo gaba ayanta ta nufosu, amma kafin ta araso mijin na ta ya shiga ti ar Saleema da duka hannayenshi biyu yanda kasan mai film ne ya samu gur aataccen boss in da ya kashe mishi duka dangi. Yatsina fuskarta tayi gaba aya hawaye sun cika mata idanu, daidai lokacin Hadeeya dake aki ta fito dan yau ita ka ai ke gidan, su Hameeda na gidan anwar Mamansu kuma sai ta dawo daga aiki ta biyo ta aukosu. Ganin abinda ke faruwa yasa ta ta e baki musamman da mahaifinsu ke fa in "Ni za ki zubarwa da mutumci? Ni za ki tozarta a idon jama'a? Yaushe aka haifeki Saleema?" Da sauri ta kaikaita wayarta dake hannunta ta fara aukar hoto mai motsi, Safiya da ke jin kamar za ta kifa a wurin ta fa i yasa ta sake matsowa hankali tashe tace" Dan Allah ka daina dukanta hakanan mana, me ta maka?" Bai saurareta ba bare ya yi abinda tace, yanzu kam afa ya fara gamawa da ita yana harba mata wacce jigata yasa ta ja baya har siket inta dake da roba a ugu ya fara barazanar zamewa daga jikinta, dan tuni hular dake kanta yayi fatali da ita. Kamo hannun rigarta yayi yana arin jawota dan lokacin ta shiga tsakanin aramin tebur da kujera, kuma idan ya kutso nan wurin ba zai aukesu ba, dan haka yake jawota da arfinshi, jinin da yake kwaranya ta hancinta har yana shige mata baki yasa Safiya takowa da sauri ta ri e hannunta aya ita ma ta kalleshi a matu ar hassale tace "Ka sake min yarinya, wallahi idan ka kashe min a sai na yi shari'a da kai." A haukace ya kalleta idanunshi sun yi jajir yace "Bismillah, ki kai arata Safiya, ke me yasa baki nunawa arki cewa ni ne ubanta ba ta bini sau da afa? Sai yanzu ne za ki min haukan ban..." Jan rigarta da yake yi da arfi ita kuma tana ri e da hannunta yasa rigar dake na kanti ne masu ja a jiki gaba aya rigar ta bi hannunshi, ganinta babu riga a jiki ne yasa shi ha e sauran kalaman, da sauri Saleema ta dunkule jikinta da na mahaifiyarta da ta dur usa a lokacin ta fashe da kuka tana fa in "Wallahi zan maka Allah ya isa ka ci gaba da tozarta min yarinya, mugu azzalumi." an kwalin kanta ta cire na atamfa ta rufe mata jikinta da shi, ita kuma sai ara tusa jikinta take yi ga na mahaifiyarta kukan ya auke mata tsaf sai shashe a take. ago kan da Safiya za ta yi suka ha a idanu da Hadeeya dake auka har lokaci, muguwar harara ta aika mata a razane tace "Idan na zo nan sai na ci ubanki." Da gudu Hadeeya ta juya ta shige akinsu tana ta e baki, shi kuma da yake tsaye nan yana kallon jinin dake ta malalowa a hancinta, rikicewa ya fara yi hankalinshi ya fara tashi, a sanyaye ya matso zai sunkuya ya kamata ta yi saurin kallonshi tace" kada ka ta a min a malam." Saleema kuma tuni tsoro yasa ta ara yin ram da Mamanta tace" Abba na tuba, na tuba Abba ka min rai, ba zan sake sa a umarninka ba na yi al awari." Sadda kanshi yayi asa saboda hawayen tausayin yarinyar da yaji na neman wanke mishi idanu, a hankali Safiya ta shiga shafa kanta da kwantaccen gashinta da babu kitso, wato Saleema ko babu kyau da hasken fata, Allah ya mata baiwar gashi, wani irin gashi ne da ita mai wayan gaske a cika sannan mai tsayin da har ya rufe mata duka kafa unta, irin gashin nan ne mai laushi ga ba i ainun, sannan a ido ma yana da kyan kallo saboda wani zir-zir-zir gareshi tamkar gashin maza da zakaga yayi kunyya kunyya tamkar gonar da tasha gyara a lokacin damuna. Sun jima a haka har saida ya gaji ya tashi ya sake barin gidan, sannan Safiya ta taimaka mata ta tashi suka shiga akinta, bakin gado ta zaunar da ita sannan ita ma ta zauna, tallabo ha arta tayi ta ga har yanzu jinin na an fitowa ka an ka an, murya a raunane tace "Shiga ban aki ki wanke jikinki ki zo mu je asibiti." Jinjina kai tayi ta mi e da yar tana ara rufe jikinta da kallabin ta nufi ban akin jikinta duk a jigace, saida ta shiga ban akin ta kalli kanta a madubin dake ciki, wasu hawaye ne masu zafi suka ara silalo mata, a nutse ta shiga wanke jikinta sai dai a lokacin tana jin hannunta na hagu na mata zogi mai matu ar zafi, haka ta arasa ta fito a tsanake ta canza kayan jikinta, sanda take saka hijabi ne ta sake kallon kanta, ganin jinin ya daina zuba yasa ta cewa "Mama ya tsaya, kawai ba sai mun je, ga sallah nan an fara." Da tauqayawa ta kalleta tace "Kin tabbata?" aga mata kai kawai tayi dan jikinta ya fara mata tsami a lokacin, ta ko ina ra i take ji ta daure ne kawai, kusanta Safiya ta matsa tace "To jikinki baya miki ciwo ne?" A asan ma oshi ta amsa da "Um um." Sai kawai ta koma ban akin dan auro alwala. Fitowarshi kenan daga ofishin likitan ashi ya kar aukar wani hoto da yake jira ya saka hannu ya bar asibitin kenan ya ji sa o ya shigo wayar, dubawa ya yi ya ga Hadeeya ce ta na umartarshi da ya shiga manhajar sadarwa ta turo mishi sa o kasancewarshi mai sauke data wasu lokutan, saida ya ja tsaki kafin ya yi yadda ta ce dan ganin wane shirmen ne kuma? Tsaye yayi wuri aya yana ara ura idanunshi dan gasgatawa, irin kallon mamakin da yake ma hoto mai motsin tamkar wanda ya ga fatalwa, to wai me ta yi haka? Wa...meee? Sai ma ya rasa a kan me zai yi tambayar? Abunka ga babbar waya hoton ya auko iya dauka, sanda ya fizgo rigarta ta bar jikinta hannunshi ne yayi wata muguwar rawar da ya sakashi sakin wayar asa ba tare da ya sani ba. A hankali ya du a zai auki wayar hawayen da bai san da su ba suka shiga kwaranyo masa yana furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Abba me yasa za ka tozartani haka? Matata ce fa." aukar wayar ya yi da sauri ya nufi motarshi duk da a lokacin akwai marar lafiyar da yake kan dubawa, amma tashin hankalin da ya samu kanshi a ciki yasa shi mantawa da haka, tafiya yake saisa-saisa yana sambatu shi ka ai, kiran sallah da aka fara yasa shi jan birki ya lumshe idanu, a hankali zuciyarshi ta raya mishi "Ka fara gabatar da sallah kafin komai, haka Saleema ta fa a maka, sallah dan neman yardar Allah ne, amma ba dan ya zamar maka dole ba." Jinjina kai yayi kamar tana gabanshi sannan ya gyara fakin in motar ya fito, tabbas yayi sallah kuma ya kamanta nutsuwa, saidai wani lokacin she an na farmakarsa a sallar ta hanyar bijiro masa da tunani akan halin da take ciki yanzu. Yana idawa ya mi e ya dawo mota, sa on Hadeeya ya sake gani kamar haka _"A ganinka ita in saliha ce ba, to kura ce da fatar akuya, ban da zubar mana da mutumci ba abinda take yi."_ A gajarce ya maida mata da _" Ki fara yin mutumcin mana, kafin ki yi orafin an zubar."_ Sosai sa on nan na shi ya sosa ranta, me kenan yake nufi? Shi ma kuma ya tura mata ne dan ranshi a ace yake kumaya fahimci kamar atanci take so tayi ga ar uwarta, da wannan yanayin ya isa gidan kuma kai tsaye shiga ya yi har farfajiyar, mai aiki ce ta sanarma da Safiya yana magana, a lokacin ita kuma bata yanayin farin ciki ta ce kawai a ce ya shigo. Daf da zai shiga suka
Chapter 47 · 0% Book details