Sashe 42
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tashi, daga yadda suka fara kai da kawowa da kuma irin matan da suke taruwa a gidan da yadda ake iface-iface da shewa ya tabbatarwa Safiya kawai shiri ne na hassalata ko a ata mata rai tare da cin mutumcinta, dan kiyaye haka tunda ta shiga akinta yin sallah la'asar ba ta sake fitowa ba duba da a lokacin ne ma za'a fara taron. Kuma gaskiyarta ne dan kuwa da gayya Ardiya ta dinga gayyatar awayenta da an uwa wai dan Safiya ta gani ba irin taron da ita tayi ba sa'ilin saukar Saleema, ku in da ya bata kuma a alla saida ta zuba ninkinsu sau biyu wajen shagalin nan, dan kayan da take so Hadeeya ta saka kawai sai da ta bayar da inkinsu ga ma inkiyar da ko baka kai mata inki aka ambaci sunanta za ka santa, musamman saboda shagalin nan saida ta an ci bashin bankin da take a aiki, a ganinga za ta biya nan kusa kuma a aljihun Abbansu Hadeeya ku in za su fito. Saleema ma dai duk da ba ta yi wani tunani game da taron ba, amma dai ta san ar uwarta ce ke shagali, tunda ta fito da niyyar kama musu aiki suka canza harshe daha hausa zuwa french da buzanci, sai kawai ta ji ta tsargu ta komawarta akin Mamanta ta yi zamanta. Saida ta yi sallah la'asar ta sake aukar wayarta dan yanzu ne take ara fahimtar wayar sai kuma Mamanta tace "Ki shirya ki fita kema, kar a ce ha in bakine daga ni har ke babu wanda ya fita, yanzu za'a ce ba in ciki muke." Ba ta musa mata ba illa "To Mama." Da ta fa a ta aje wayar ta shiga ban aki, shirin na ta ba wani dogon lokaci ya auka ba, dan kuwa bayan mai da ta shafa sai turare, ko hoda ba ta shafa a fuskarta ba sai kwalli da ya zama sabo a gareta tun tana arama, doguwar rigar shadda ce ta saka kalar ruwan zuma mai yalli, aurin zara buhari ta yi sai takalminta masu tudu da ta saka, sar ar da Gwamna Naseer ya sako mata a cikin kyautar nan ta ma ala mai shegen tsada duk da ba wani aukan hankali gareta ba, ba ta auki hijabi ba duba da a cikin gidansu take, kuma ko addini bai tilasta saka hijabi a cikin gida ba, hasalima wata mazhabar na gani indai a cikin gidane ko babu an kwali ba laifi bane indai ba waje ta fita ba, a nan ne mala'iku za su tsinewa kan da yake bu Tana fita jikinta yayi sanyi ta tsaya daga nesa tana hangen mutanen dake zaune can kusa da ofar shiga angaren mahaifinsu, wurin ya ayatu sosai da kujeru da hotunan Hadeeya kala kala wanda bbabu aya inda kanta ke rufe, ga flawowi da suma suka ara fito da kyawun wurin. Kujerar da ta gani ta musamman wacce ta saka wani teburin glas tsakiya da aka sha eshi da tsadaddin lemuka da ruwan gora ha e da chacolate da su alawa da biscuit, abun ya yi kyau sosai. Ba komai ya kayar mata da gaba ba sai yadda awayen na Hadeeya da suka fara halarta ta ga kowace ta ure kwalliyarta yadda ka san gasar za en sarauniyar kyau za su je, inki iya inki, kwalliya iya kwalliya, shiri na musamman da ya fito da surar kowace, ajiyar zuciya kawai ta sauke ta ora hannayenta kan gajeruwar kagantar da ta mata shamaki da su ta tallabe ha arta kawai tana ci gaba da kallon inkin jikin kowace, ba wai dan sun birgeta ba, a'a sai dan ji ina ma a ce dayawa daga cikin inkunan ita tayi su? ara* kallon fuskar Hadeeya ta yi ganin yanda arta ta fito ka rantse balarabiya ce ko ba'india, a gaskiya dole ma arta ta auri babban waro, irin wannan kyau haka da tsaruwa? Murmushi ta saki tare da mi awa mai kwalliyar da ta gama ha a kayanta za ta tafi wacce suka yi babbar sa'a ta biyo gidansu ta mata kwalliya saboda ta riga ta fito yin kwalliyar kenan, ba dan haka ba sai dai su sameta har in da take, kar ar ku in tayi ta musu godiya su ma suka mata godiya ta fita. Hadeeya dake tsaye gaban madubi wayar da a yanzun take tutiya da ita ke ri e da ita ta kara a kunnenta fuskarta auke da damuwa, duk da idanunta suna hango mata tsantsar kyawun da ta yi, irin aurin kallabin da aka kashe mata abun ya matu ar birgeta, ga doguwar rigar dake jikinta ta wani tsadadden cotton boil, irin inkin da aka mishi ya bi jikinta sosai ta yanda mai kallo zai ga kamar a tsirararta yake ganinta, dan hatta da shatin cibiyarta an fito da ita bare su ugu da gwiwa da kuma irji, hakan ya sa irarta fitowa sak tamkar wata kwalbar cocacola. arasowa ta yi wajenta tana kallon fuskarta da ke mata haske tamkar zarah tace "Wai me ye kike yi? Ki zo ki fita mana ana jiranki." Cike da qhagwa a ta turo baki tana sake dan ara wayarta a kunne tace "Momma ni fa na yi al awarin ba zan fita ba sai tare da Mu'az ina." an zaro idanu Ardiya tayi sai kuma ta juya ta kalli awayen Hadeeya da ke saka tsarabar da za'a rabama kowa bayan gama taron, ganin hankalinsu yana kan aikin da ta sakasu yasa ta sake matsawa sosai kusan Hadeeya cike da ra a tace" Dama jiya na so muyi magana da ke, sai dai ko da na dawo dare ya yi sosai, wai da gaske Mu'az ne ya ce yana sonki?" Kallonta Hadeeya tayi da mamaki da kuma aguwa tace" Momma, to arya zan miki? Shi da kanshi ya fa a min a ranar da muka je gidansu, nima kuma na bashi amsa, kuma ba ki ga muna waya da shi ba kullum." Nauyayyar ajiyar zuciya Ardiya ta sauke ta du ar da kanta asa tace" Ina fata dai ba lalata min ke ya yi ba, sannan ya watsar da ke ya je ya auri Saleema." arfi Hadeeya ta zaro idanu ta furta" Aure kuma?" Da sauri Ardiya ta mata alamar" Shiiiiii! Sannan ta sake mata ra a cewa "Nima jiya Gaishata ke fa a min, wai maganar aurensa ake yi da Saleema." Kiran da ya sake tsinkewa wanda ta aika ne yasa ta auke wayar a kunnenta tana kallon mahaifiyarta a gigice tace "Momma Mu'az Saleema zai aura? To ni kuma fa? Ba ni ya ce yana so ba?" Sai kuma ta aga murya tace "Wallahi Momma na san ma asiri ta masa, dama na ga tana ta shigewa jikinshi da muka je gidan, wallahi Momma ba zan yarda ba." Duk da ta san ba gaskiya bane kuma ba ta yarda cewa wai asiri Saleema ta ma Mu'az ba, amma dan ta kwantar mata da hankali duba da abinda ke gabansu sai kawai ta dafata tace" Hakane mana ata, ke dai yanzu ki je ki kwantar da hankalinki, ki saki ranki ki yi shagalinki yanda ya dace, ni zan ji da wannan matsalar, Mu'az zai dawo gareki ko ba ya so." Jinjina kai tayi tace" Da gaske Momma?" Cike da warin gwiwa tace" Na ta a fa a miki zan yi kuma na kasa?" Girgiza kai tayi alamar a'a, nuna mata ofa tayi tace" Dan haka je kiyi murnarki, ni zan ji da komai." Juyawa tayi za ta fita Ardiya ta kalli awayen na ta tace" Sai ku tashi ku tafi ko." Aje aikin sukayi suka mi e, biyu a cikinsu ne suka auki gwangwanin abun fesawa mutum mai kama da flawowi yayin da yake tafiya, Hadeeya ce a gaba su kuma suna bayanta kamar yadda aka tsara, dama kayansu iri aya kusan kalar kayan Hadeeya, suma kuma duk doguwar riga ce a jikinsu, haka suka dinga fesa mata abun nan tana fita har suka kawo ar berandar da Saleema take. ewa sukayi da Saleema za ta koma ciki sakamakon aton redio da aka kunna wanda ya kara e gidan, ita kuma ta ji ba za ta iya jurar wannan ara a kunnuwanta ba, wani kallo Hadeeya ta bishi da shi kafin ta ja tsaki su wuce a ranta tana ayyana "Wallahi ba zaki rabani da shi ba, ta ! Ai ya fi arfinki yarinya." Tunda Saleema ta koma ciki bata sake fitowa ba saida tayi sallah magrib, lokacin ne ta fito saboda jin har lokacin ki a na tashi, a ganinta dai magriba tayi ya kamata a ce kowace a ta tafi gidansu, amma abun mamaki data fito sai ta samu gidan cunkus da an mata da samari wasu na rawa wasu na kallonsu da alama lokacin ne ma shagalin yake kan ganiyarsa, dan ko da yamma mutanen basu kai rabin haka ba, abun takaicin shi ne ganin anwarta Hameeda tare da wani she anin matashin da ya sha zanzaro suna ta ti ar rawa. Girgiza kai tayi a ranta tace "Allah ya shiryaku." Juyawa ta yi da nufin shiga falon Abbansu, sai kawai ta ga Ardiya na zaune tana kallon komai ita da awayenta suna ta hira da dariya, idanunta ne suka cika da hawaye na tausayin halin da an uwanta ke ciki, ta ya suna irin wannan rashin kunyar, amma kuma tana kallo ba za ta tsawata musu ba? A fusace ta juya ta shigo falon ta shiga ofar dake kusa da tv dake jikin bango, ratsawa tayi da wajen cin abincin na mahaifinsu wanda ma fi yawan lokuta a nan yake cin abincin safe sannan ta shiga ta wata ofar sai ga ta a falon na shi. Da mamaki ta kalli ofar data fita waje zuwa farfajiya wacce idan ya yi ba i suke shigowa ta nan, ko kuma shi yana shigowa ta nan musamman idan iyayensu basu nan ko ya ji an yi ba i, kwalayen lemu da robobin ruwa da sauran sharar data gani ya ara ata mata rai, tunaninta su waye dan rashin kunya suka shigo har akin mahaifinsu sannan sukayi haka? Juyawa ta yi ta dawo kusa da teburin cin abinci ta auki tsintsiya da abun kwashe shara da wurin zubawa ta koma falon,