← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 116

Sashe 20

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kirki, kin san ban auka zai gama aikin nan a an lokacin nan ba?" an murmushi kawai tayi tace "Ai ya wuce haka." "Gaskiya kam, kuma ga shi kamar dai yanda mu ka fa a masa ya mana." Kallon inkunan da hirar da suke ta awa musamman kan bikin da za'a yi jibi wanda kayan shigar bikin ne na yasa har Alhaji Auwal ya fito ba ta sameshi da maganar da ta yi niyyar zuwa su yi ba, dan ba za ta bari ta yi sanya ba, dole ta daki arfe da zafi-zafinshi. Juyawa sukayi a tare suka kalleshi yana fitowa sanye da doguwar riga, cike da kissa da kwarkwasa amarya ta shagwa e fuska tace "Baby, shi ne ka fito ba ka jirani ba? Gashi kuma ina son magana da kai." an murmusawa ya yi yace "To ai ba guduwa zan yi ba, wajen Baba zan shiga, tun jiya rabona da su." Hanyar fita ya kama ta bishi da kallo cike da jin arfin gwiwar tabbas zai amince da abin da za ta zo mi shi da shi. *Ya na* zuwa ya samu Saleema da mahaifinshi a akin suna ta hira da dariya, da mamakin irin dariyar da take ya arasa yana zama bakin gadon yace "Me ki ke ma dariya haka?" Wata dariyar ta yale da ita ta nuna tsohon tace "Wallahi Papi ne ya ke ta cika min ciki da dariya, labari suke bani." Murmusawa ya yi ya kalli mahaifin na shi yace "Baba, ya jikin na ku?" Cike da tsantsar auna da kulawa dattijon ya amsa da "Alhamdulillah Auwalu, ka na lafiya?" A tausashe ya amsa da "Lafiyata lau Baba, ka ci abinci?" Cikin sar iyar murya yace "Ban ci ba, amma kai ka ci ne?" Da alamar damuwa da tambayar mahaifin na shi yace "Baba, sai ka dinga min tambayoyi kamar wani aramin yaro, hakan ya sa wasu lokuta bana son mu ha Shiru dattijon ya yi sai kuma a sanyaye sosai yace "To ka yi ha uri, na saba ne idan ban tambayeka ba bana jin da Da sauri Saleema ta katsesu ta hanyar dafa hannun dattijon tace "Papi, na kawo ma ka abincin ne?" aga kai ya yi alamar e, mi ewa ta yi Alhaji Auwal yace "Ki ha o da maganinshi." Jinjina kai ta yi ta kama hanyar fita, ta na bu ewa Nafissa na shigowa auke da abincin, kar a ta yi ita kuma ta koma dan wasu ayyukan. Dawowa ta yi ta zauna ta zuba da kanta sannan ta ago ta mi owa Alhaji Auwal da ke shirin tashi ya tafiyarsa, kallonta ya yi da alamar jiran arin bayani yace "Uhum?" Saida ta yi takwaf-takwaf da fuskarta cike da sigar ladabi da biyayya a tausashe sosai tace "Abba, na yau kawai ka ba wa mahaifinka abinci da hannunka, a shekarun nan na shi zai yarda ka ciyar da shi ne ta hanyar bashi abinci a baki kamar yadda ya baka kana yaro, ba wai ta hanyar saka mai aiki ta dafa ba sannan ta kawo masa ya ci, na san an auki shekaru rabon da ka ji shau i na mahaifi na fizgarka, ka fizgo wannan shau in ko hakan ya sa ka tuna da mahaifinka na bu atar kulawarka, *kai ka ai kawai* ya ke da bu ata." Sadda kanta tayi asa ta saki murmushi tace" Abba, ka na damuwa saboda yawan tambayarsu gareka, ba komai ya kawo hakan ba sai *soyayyar mahaifi ga aramin ansa*, shi a wajenshi har yanzu kulawarsa ka ke bu ata, ba zai zama cikakken mahaifi ba idan har ya na nauyin baki wajen tambayar abin da ya shafi lafiyarka, harkokinka, farin cikinka da ma damuwarka, sannan abun farin ciki ne yau a rayuwa a ce kana da wanda ya damu da kai, Abba, wallahi duk soyayyar da iyalin nan na ka suke ta amar suna maka bai kai rabin soyayyar da bawan Allahn nan ya ke maka ba, hatta da an da ka haifa..." Tunda ta fara maganar alamun komai na ratsashi ne ya bayyana a tare da shi, dan jikinshi yayi sanyi kuma kanshi a asa yake sai dai wani lokaci ya kan ago ya kalli mahaifin na shi da alamar jin kunya, amma yanzu da ta ce wai har yaranshi sai yasa ya kalleta da mamaki, kamar ta san me kallon ke nufi sai kuwa ta ce "E Abba, soyayyar da yake maka ta fi wacce suke maka, sai dai idan muka kalla a zahiri shi ya na sonka ne saboda shi ya haifeka, su ma kuma suna sonka ne saboda kai ka haifesu, ba fata na ke maka ba Abba, a yanzu ba na jin akwai wata larura da za ta saka tsohon nan ya gujeka, amma yanzu Mu'az ko Mu'awwaz da za ka hanasu auren wacce suke so, to fa idan ba Allah ya shirya maka su ba, tsaf za su bijire maka a kan mace, kenan soyayyarsu ba ha i da ta wanda ya kawoka duniya." Burinta bai wuce kar ya ga za ewarta ba, ba ta so su ga ta cika shiga shirgin da ba na ta ba, sai dai kuma akwai kurakuren da take ganin ya kamata su gyarasu, saida ta an fa a murmushi a ladabce tace" Dan Allah Abba kar ka fahimceni ba daidai ba, na yi magana ne saboda girma da mahimmancin iyaye garemu, idan har shi ka ai ya rage maka a rayuwa, ya dace ka ata an sauran lokacin da ya rage maka wajen kula da shi, duk rayuwarsa ya ata ta ne wajen kula da kai, a yanzu da ya kawo arfi yake kuma neman tallafi, kulawarka ka ai yake bu ata, duk abin da ka ke nema da yake auke maka hankali daga nesantar mahaifinka, ba zai zama mai albarka gareka ba saboda mahaifinka ba ya farin ciki da halin da ka ke sakashi a ciki.." Sai kuma ta kalli tsohon da ya ureta da ido ya ma rasa akan me zai auna yarinyar, cikin kulawa tace" Papi, ko kana farin ciki da zaman wurin nan kai ka ai?" Da sauri Alhaji Auwal ya kalleshi da son jin amsar da zai bayar, shi ma kallonshi ya yi da tunanin ko ya masa kara? Sai kuma ya sunkuyar da kanshi asa saboda ba ya so ya sosa ranshi ko ka an, wani murmushi Saleema ta yi mai ciwo ta kalli Alhaji Auwal tace "Wani shirun ma amsa ce." A hankali ta rusuna ta aje farantin abincin sannan ta mi e tsaye tana kallon Alhaji Auwal tace "Idan har ka yi ya i she an kuma ka yi nasara, to na san za ka yi abin da ya dace kan lamarinshi, sannan za ka ci gaba da yi har sanda mai rabawa za ta rabaku kuna mai cike da alhini da aunar junanku." Idonta cike da hawaye ta matso kusa da Alhaji Auwal ta an ri e hannunshi tace" Abba, kafin kai ko shi wani ya bar duniya, ya kamata ya shaida arzi i da ikon da Allah ya baka ta sanadiyar jajircewarshi a kan ka har ka zama hakan." Juyawa ta yi ta kalli tsohon da fara sharar hawaye saboda ta o masa ciwon da ya jima yana gwaguyarsa, cike da tsokana ta marairaice ta kama kunnuwanta tace" Ayya! Papi ya na kuka saboda na ta a masa an gudaliyarsa." Da sauri ta ri e hannunshi aya tace" To a gafarceni ba zan sake ba, na barku lafiya." Ta fa a tana ficewa a akin da sauri-sauri, jiki a matu ar sanyaye tsohon ya bita da kallo yana mai saka mata albarka, ko ba'a samu canji ba a alla dai ta sauke nauyin da ya hau kanta na fa in gaskiya da gyara kayanka, Alhaji Auwal kuma kanshi na sadde ya kasa agawa saboda tsananin kunya da nadama da kuma udirin gyarawa da ya arsu a zuciyarshi yanzu yanzun nan. Tsugunno ya yi a gaban mahaifin na shi ya ri o hannayenshi kanshi a asa cikin muryar da ke auke da amon nadama yaxe "Baba ka yi ha uri ka yafe min, na tuba Baba ba z..." Da sauri yace masa "Shikenan Auwalu, ya isa haka ka ji ko, ni dama ban ta a ri eka a zuciyata ba, saboda na san illar hakan, bana so mutuwa ta riskeni ina mai hushi da kai, shiyasa duk yanda raina ya ace a game da halin ko in kula da ka ke nuna min sai na yi gaggawar yafe maka." Hannayen mahaifin na shi ya ago ya sumbata har sau uku sannan ya dur usa gwiwoyinshi ya rumgumo tsohon na shi ya sumbaci wuyanshi, shi kuma da abun ya zo masa da rashin sabo sai ya ji kunya ta kama shi, rintse ido ya yi sai dai yana jin aunar an na shi na sake narkuwa a cikin jikinshi, angare aya kuma soyayya yarinyar nan ya ji ta mamaye zuciyarshi da kuma saka mata albarka. Alhaji Auwal ma albarkar ya ke saka mata tare da ba wa kansa tabbacin wannan dole ma ta zama surukar gidanshi, wata zuciyar kuma na raya mi shi ba dan anshi ya rigashi ba ai da shi zai so samun wannan *zinariyar waliyiyar*, dan babu wanda ba ya son alkairi wa kansa? Amma a hakan ma idan har ta zama matar anshi, to shakka babu za ta ci gaba da orasu a sira in rayuwa mi iya. Bai fita a akin nan ba sai da ya ba wa mahaifinshi abinci a baki ya sha maganinshi, wani abun farin cikin kuma yanda suke hira tsohon na ta o yarinyar Alhaji Auwal wanda shi bai san ya yi ba, wani kuma ya sani amma ya manta saboda shekaru, sai ya sake yarda da abin da Saleema ta fa a cewa har yanzu shi a aramin yaro yake kallonshi tunda shi ya haifesa, to in ba haka ba har fa labarin lokacin da ya yi bayan-gari yake bashi daga makaranta, haka ya auki awa biyu suna nisha i kuma har zuciyarshi sai ya ji kamar ya sauke wani nauyi mai girman gaske da ya jima yana dakonshi a kai. A farfajiyar gidan suke zaune kowa ya na abin da ya fisheshi, motar Mu'az ce ta shigo gidan ya nufi inda
Chapter 20 · 0% Book details