← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 116

Sashe 25

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

juya ga Saleema da ke tafiya a hankali tana jin me mahaifin na ta ke fa a, ta na ganin idan aya daga cikinsu haka ta faru, shin haka zai fa a? Kiranta ya yi yace" Dawo zauna." Dawowa ta yi ta zauna yana kallonta yace" Kin ji me mahaifinki ya fa a, ke me kike tunani?" Saida ta saci kallon mahaifinta dake ta hararenta tace" Abba, mu fara tabbatar da gaskiyar maganar ta hanyar tuntu ar Mu'awwaz." Jinjina kai yayi yace" Wannan ma magana ce, amma yanzu ke mu addara an tuntu eshi kuma gaskiya ne abin da aka fa a, me ye mafitar?" ar dariya tayi ta girgiza kai tace" Abba, gaskiya a wautar kasancewata ar fari kuma mace mai rauni, idan a ra'ayina ne sai na ce mu aura masa ita, kunga kenan ko da daga baya maganar ta fito, to sai a aukeshi kawai soyayya ce irin ta masu anci, tunda dukansu sun haura shekara sha takwas, dan idan ku i mu ka bashi hakan zai iya sa wa ya dinga yaudararmu ta hanyar kar an ku i lokaci lokaci (blackmail), kunga kenan babu hutu kuma ko yaushe dai asirin zai tonu, amma idan ta zama matarshi babu mai aga maganar." Bubbuga cinya Alhaji Auwal ya yi ya washe baki yana dariya yace" Wannan yayi, wannan shawara ta yi, hakan shi ne mafita." Sai kuma ya kalli Alhaji Yusuf da mamaki ya sakashi zuba musu idanu kawai ya nuna mishi Saleema yace" Ka gani ko, abinda na ke so ka fahimta kenan, wannan ita ce *BAIWAR ARKA*." Kallonta yayi yace" Tashi ki shiga ciki Baby, amma zan fara shawara da Baba na ji me yake gani game da hakan, dan yanzu bana komai sai da shawararshi." Murmushi ta saki ta mi e kawai dan ta san ta wajen Papi ma ba za'a samu matsala ba, dan ta gama da shi tun kafin ma ta kitsawa Nafissa abin da za ta yi. *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:41 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _17_ Tunda Papi ya fara magana bayan sun fa a masa abin da ke faruwa Abban Saleema ke kallonshi kamar a tsorace, to sak shawarar da aramar arsa ta bayar shi ma yake maimaita duk da ba su fa a masa sun tattauna da kowa ba, har sai da Alhaji Auwal ya ta oshi yace "Ka gani ko, ya kamata ka saka ido akan yarinyar nan, tunda ta zo gidan nan abubuwa masu kyau ke faruwa, sannan rayuwata da ta iyalina ta fara hawa kan saiti, wallahi babbar *kadara* Allah ya baka, ka kula da ita yanda ya dace, idan Allah yasa ba ta cikin wanda za su ci moriyar boko, to ka tambayeta abin da za ta iya yi bayan wannan, za ka sha mamakin yarinyar nan idan na fa a maka watarana ni da kai za ta iya yi mana alfarmar da duk ikonmu da iliminmu ba za su sama mana ita ba." Maida dubanshi yayi ga Papi yace" Baba, tunda kai ma abin da ka gani kenan, ina ga anjima sai mu je gidansu yarinyar, ko ba komai ni a ganina ya kamata Mu'awwaz ya shiga hankalinshi, dan abin da yarinyar ta zo da shi ya tabbatar min da zargina a kan shi, Baba kamar Mu'awwaz na kamashi da kororn roba (comdom) a motarshi, amma da na yi magana ya dinga min kame-kame, yanzu kam na yarda da abin da ke faruwa a gidan nan, tunda shi ya lalata mata rayuwa, to shi ya kamata ya aureta ko ba ya so, idan ta auri wani a haka za ta iya fuskantar tsananin rayuwa da iyayya, idan mun yi sa'a auren ya yi arko to za ta rayu cikin tsangwama, amma idan shi ne da ya fara, bai da bakin aibatata dan shi ya fita lalacewa." Kallon Alhaji Yusuf ya yi dake tunani kan abin da Alhaji Auwal ya fa a masa, a ganinshi me ye ya kamata a ce kamar Saleema na so bayan karatu? Ai sai dai in soyayya take, ko kuma aure take so? A gaskiya ba ya jin zai iya taimaka mata da komai in dai ba abin da ya shafi karatu ba, to me ya fi ilimi a duniyar nan? Idan ba ka da ilimin nan na boko wani ba auye ka ke zama, aramin misali sau tari zai yi magana da yaran da harshen faransanci su mayar mi shi, amma ita ko ya yi niyyar yi mata sai ya dakata dan ya san ba za ta san me ya ce ba bare ya samu abin da yake so. Dafashi Alhaji Auwal ya yi yace "Muje ko?" an zabura ya yi sannan ya mi e yana kallon Papi yace "Baba sai an jima." Da haka suka fita farfajiyar Alhaji Yusuf na fa in "Yanzu sai yaushe za'a turo min yaran? Ina bu atarsu a gidan nan wallahi, gaba aya mun yi kewarsu." Nauyayyar ajiyar zuciya Alhaji Auwal ya sauke yace "Ka yi ari ka sama musu annai mana, ka ga fa duk sun zama an mata nan gaba ka an aurar da su za ka yi." Murmushi ya yi yana shafa wuyanshi yace "Alhaji ai... Ina ga sun isa haka, dama namiji ne muke ta fatan Allah ya bamu, kuma na fi so ya fito daga wajen mahaifiyar Saleema, amma Allah bai nufa ba har yanzu." Murmushi Alhaji Auwal ya yi yace "Da alama kai kanka ka fi yarda da tarbiyar da Safiya ta ke ba wa na ta yaran?" Sadda kanshi yayi asa bai ce komai ba, murmushi Alhaji Auwal ya sake yi yace "Shikenan ba komai, zan turosu da yamma, akwai tsarabar da nake son ha a musu ne, sannan da dare zan zo gidan na ka akwai maganar da na ke so muyi da kai a kan ita Saleema da kuma Hameeda." Da sauri ya kalleshi yace "Lafiya dai ko? Ba wani abu sukayi ba?" Girgiza kai yayi yace "Ba abin da suka aikata, idan na zo za ka ji ko menene." Jinjina kai yayi yace "Shikenan Alhaji, Allah kaimu." Musabaha sukayi ya bar gidan da tunanin wace magana kuma zai zo mishi da ita a kan Hameeda da Saleema? Da haka ya isa gida ya shaida ma Safiya Saleema ba ta samu ba kamar dai yanda tun farko ya je makarantar ya dubo musu, saida ta yi walla na rashin jin da i da fatan Allah ya nuna mata ilimin da ke cikin hakan. Idar da sallah azahar inta kenan ta samu Hajia babba tace "Mama, dan Allah wayarku za ku ara min na kira Mamana." Da fara'a ta nuna mata wayar da ke kan gado tace "Gata nan, idan kin ida kuma sai ki fa awa su Hadeeya su shirya, Alhaji ya ce zaku fita tare siyayya." "To Mama." Ta fa a a ladabce tana aukar wayar, fitowa tayi daga akin tana ora wayar a kunne, jim ka an Mamanta ta auka suka gaisa a tsanake, orawa tayi da "Mama lambar Khairat za ki duba min a wayarki, ina so zan yi magana da ita." Numfashi Safiya ta sauke har tana jin sautinshi kafin tace "Shikenan, amma me zai hana ki bari har ki dawo, tunda anjima za ku zo." A shagwa e tace "Mama, magana ce ta gaggawa, kwana hu u ya rage saukar makaranta, ina so na tambayeta wani abu ne." "Shikenan." Ta fa a tana cewa "Bari na duba na gani." Har za ta kashe wayar Saleema ta yi saurin cewa "Mama." Dakatawa tayi tace "Ina jinki." Cikin ladabi tace "Abba bai miki fa a ba a kan rashin samun jarabawata?" Murmushi Safiya tayi tace "Bai yi ba Hajia, dake tun jiya ma kwance na ke ban da lafiya, amma yanzu da sau Hankali tashe Saleema tace "Ayya! Mama baki da lafiya, ki yi ha uri jiya ban kiraki ba, ya jikin na ki?" A tausashe tace "Da sau i sosai Saleema, kuma har da rashinki a kusa dani, amma yau na ji arfi sosai da aka ce za ku dawo." Cike da tausayin mahaifiyar ta ta tace "Zan zo Mama, shiyasa nake ta miki addu'a Allah ya sa ki min ane, ko hakan zai sa ki sassauta soyayyarki a kaina." Muryarta auke da sautin jimami da rawar murya tace "To ya na iya Saleema, ke ka ai Allah ya bani, dole na tattara duka soyayyata na ora a kan ki, idan so samuna ne Saleema mahaifinki ya miki aure tun yanzu, ta hakane zan saka ran ganin jikoki daga gareki." Kunya ce ta kamata kamar tana gabanta, rufe fuska tayi da tafin hannunta ay tace "Kai Mama, dan Allah ki daina ni bana so." Safiya ma murmushi tayi daga inda take tace "To shikenan na daina, amma idan kika zo zamuyi maganar dan ki tabbatar ina bu atar hakan daga gareki." an matse bakinta tayi tace "To Mama, karki manta lambar." "To." Ta fa a tana kashe wayar dan turo mata lambar, arasawa tayi ga kujera ta zauna tana jiran shigowar sa o, kamar an ce aga kanki kalli ofa sai kal suka ha a idanu ita da Mu'awwaz dake shigowa falon da sauri kuma da alamar aci rai da tashin hankali. Kai tsaye ita ya nufo da mugun sauri, sai da ya zo gabanta ya tsaya, juyawa ya yi dama da hauni ya ga ba kowa sai ita ka ai, maida dubnshi yayi gareta yace "Ke, me kika fa awa Abbana?" Wani kallo da take jifanshi da shi asa da sama kamar ta ga abun yama, arshe ma auke kai tayi ta ta e baki tace "Me ya ce masa na fa a mi shi?" Sunkuyowa ya yi kamar zai yi ruku'u yace "Na tabbata akwai abin da kika fa a masa, yanzu yake tambayata wai me ye tsakanina da Nafissa." Kallonshi tayi ta ora afa aya kan aya tace "In tambayeka mana? Me yasa ka min arya a waccen ranar?" Rarraba idanu yayi yace " arya kuma? Yaushe na miki arya?" Nunashi tayi da yatsa tace "Ranar ka fa a min shi ne farko, ashe wata uku kenan ka
Chapter 25 · 0% Book details