← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 116

Sashe 8

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da mutumta junansu. A tsanake mamanta ta kalleta tace "Saleema, lafiya ki ke ta had'e fuska?" K'ara turo baki ta yi gaba ta na k'ok'arin saka rigarta duk da sanye take da hijab saboda kunyar Maman da ta ke ji ba za ta iya tub'ewa a gabanta ba tace "Ni wallahi Mama ba na son zuwa gidan nan, dan kar Abba ya ce na rainashi zan tafi kawai." Murmushi Safiya ta yi da mamakin wai Saleema ba za ta iya saka riga a gabanta ba dan kar ta lafiyayyen k'irjin da ya cika mata gaba tace "To wai me ya sa ba kya so? Can ma gidan hutu ne fiye ma da na mahaifinku." Juyowa Saleema ta yi ta kalleta tace "Mama, ba wannan ne matsalar ba, kin san ko k'auye zan iya rayuwa, kawai dai yaran nan na sa ne ni wallahi ba su kwanta min a rai ba." Da mamaki Maman tace "Su wa kenan?" Cike da yatsina fuska tace "Yan mazan mana, duk ba su da tarbiya wallahi." Rik'e hab'a Maman ta yi da mad'aukakin mamaki tace "Ikon Allah! Saleema yaushe ma ki ka musu sanin da ki ka gane haka? Shin *Mu'az* d'in da ko shekara bai yi da dawowa daga karatu ba? Ko kuma *Mu'awwaz* d'in da ke da tsantseni da share mutane?" Ta na gama saka rigar ta cire hijabin ta na saka zip tace "Dukansu Mama, wallahi kura ce da fatar akuya, dukansu rainawa mutane hankali suke, ba ma kamar tuzurun nan." Dariya Maman ta sake har da k'yalk'yalawa tace "Wa ye tuzuru kuma?" Ba alamar wasa tare da ita tace "Shi Mu'az d'in mana, shekara talatin ba aure amma ya na nuna bai damu da komai da kowa ba, hmmm ! D'an rainin hankali kawai." Maman ta dai abun dariya da mamakin yanda ta hak'ik'ance ta na ta sababi take, to ita ba ta ma san yaushe ta musu wannan sanin ba haka? Tabbas sun tab'a zuwa gidan amma fa tun ba ta kai shekara goma ba a duniya, duk da ta san ta bata da mantuwa kan abin da ya shafi rayuwar duniya da karatunta na islamiyya, amma dai ba ta tunanin har yanzu ta na tune da abinda ya faru shekara *tara* da ta wuce. Haka ta gama shiryawa amma sam ba ta so haka ba saboda ita ta gama fahimtar duk wani da Abbansu ke alak'a da shi ta kusa sosai to d'an boko ne da ke da wayewa, sai dai na wani ya fi na wani kawai. Ta na gama shiryawa ta fito farfajiyar, a nan ta samu su Hadeeya har da mahaifin na su a tsaye da alama so ya ke ya ga tafiyarsu da kuma Mamansu gefe ta na amsa waya. Sanye take da doguwar riga wacce gaba d'aya gabanta yake a bud'e, ma'ana aka masa doguwar tsaga har zuwa cibiyarta, sai siket d'in atamfar da ya rufe mata cibayar inda a baya kuma yake yage da tsaga shima har idan tana tafiya kamar za ka hango gwiwoyinta, k'aramar jakarta ta rataya ta tsakiyar wuyanta da hannu, sai takalmin kalar jakar masu d'amara da rufaffiyar sama, kwalliya ce ta ban mamaki ta d'auka sai dai ko d'an kwali babu a kan ta, hasalima d'an kwalin rik'e yake a hannunta, a hakan wai shi ma wani kalan tsarin ne. Kayan sun matseta sosai yanda suka fito da kyakyawar surarta da kuma kyawun fuskarta, masha Allah kuma abun ka ga farar fata sannan mai kaurin jiki, hakan yasa Hadeeyar ta zama basu da maraba ita da Saleema da ta bata shekara uku da haihuwa saboda su na da kumari. Cike da rashin jin dad'in yanda ta ga yan uwanta sun shiryo ta kalli Hadeeya a tausashe tace "Haba Hadeeya, wannan wace irin shiga ce? Kina 'yar musulmai amma ki fita haka kanki babu rufi? Idan ma ba zaki saka hijab ba ko gyale ne ki saka mana." Cikin tsiwa da raini da kaud'i Hadeeya ta kalleta tace "Ke kuma malama ina ruwanki da shigata? Kina da matsala da hakane? Ka ji min mata kai, so kike na yi irin shigarki kamar wata matar aure?" Kafin kowa ya yi magana Ardayi da aka mata kiran gaggawa a wajen aiki ta k'araso da sauri kai tsaye mahaifinsu ta tunkara cikin shagwab'a tace" B , kira ne da wajen aiki ana buk'atata yanzu, zan tafi sai na dawo..." Ta yi maganar ta na fad'awa jikinshi ta sumbaci labb'anshi tare da d'agowa tace" Ba zan jima ba Bebe, sai na dawo." Saleema da tun da ta ga ta nufeshi ta d'auke kanta saboda kunya, shi kan shi yanzu da shekaru su ka k'ara ja ya kan ji nauyi idan irin haka ta faru, sai dai Ardayi ta saba kuma ba ta ganin hakan a matsayin wata matsala. Hannu kawai ya d'aga mata bai iya furta komai ba har ta k'arasa kusan su Hadeeya da ba ta san akan me suke magana ba ta rumgume su su ma musamman Hamdeeya har tana fad'a mata "Shoyerta (autata) ki kula da kan ki." "To Momma." Ta fad'a cike da farin cikin za ta tafi unguwa na wasu kwanaki, suna kallo ta shiga motarta ta bar gidan. Sai lokacin Hameeda da ita ma dai wata arniyar shigar riga da siket na shadda ne jikinta tace" Kama da matar auren ma wacce ta haihu, dan wannan hijabi da ta saka sai matan aure masu 'ya'ya, dubi fa daga nan baya har k'asa yake ja mata." Kallon hijabin na ta sukayi kam mai hannaye wanda ya mata kyau sai kawai suka bushe da dariya suka tafa hannu Hadeeya na fad'in" Wa ya ga ta Allah." Murgud'a baki Hameeda tayi ta harari Saleema tace" Wai a haka za ta bi mu, ki ga fuskarta ko hoda ba ta murza ba sai k'yallin mai take, mtssss! Ni wallahi da Abba da ma ka hanata zuwa." Wani kallo Saleema ta ma Hameeda sai kuma ta kalli mahaifin na su da duk da yana jin me ke faruwa amma hankalinshi na ga waya yana latsawa tace" Abba ka a yaran nan magana mana, dubi fa shigarsu?" Wayar da ya d'ora a kunne ya sa shi nuna mata su wuce su tafi kawai dreba na jiransu, cike da takaicin halin ko in kula ta fara yin gaba ta shige motar. Tsaki Hameeda ta sake ja har suka k'arasa kusa da mota inda dreba ke jiransu suka shiga ya jasu zuwa gidan. *______________* *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:37 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _7_ Tabbas sun yarda Alhaji Auwal ya fi mahaifinsu kud'i nesa ba kusa ba, dan daga irin ginin da ya tarwatsa za ka fahimci haka, da kuma irin kayan alatun da suka k'awata gidan, ba su daina kalle kalle ba har mai aikin da ta musu jagora zuwa cikin gidan suka shigo k'aton falon. Saleema da ke baya cikin sharb'eb'en hijabinta kallo d'aya ta ma uwar gidan ta saki murmushi saboda tuna shekarun baya da su ka sameta tana cikin ganiyar k'uruciyarta mace yar gayu da wayewa, amma yanzu shekaru sun lak'ume duk wannan ji da kan da k'uruciyar, ba abinda ya rage mata face dattijuwar fuskarta mai d'auke da gilashi. Kusanta suka fara zuwa inda take zaune, Hadeeya da Hameeda daga tsaye suka gaisheta da "Ina yini?" Hamdeeya kuma kusanta ta zauna dan ta san matar ita ma tana wangale mata baki sai dai ba ta ce mata komai ba, yayin da Saleema dake gefe ta durk'usa kamar za ta yi zaune tace "Ina wuninku Mama." Da fara'a da kuma jin dad'in gaisuwar ta Saleema ta kalleta cike da kulawa tace "Lafiya lauSaleema, kina lafiya?" "Lafiya lau." Ta fad'a cike da kunya, maida hankalinsu sukayi kan wata dattijuwar da ke shigowa falon hannunta rik'e da waya, kallo d'aya suka mata ita ma suka gaisheta kasancewarta amaryar gidan. Cike da yauk'i da jan aji ta wani yatsina fuska tace "Lafiya lau, har kun iso ?" Kafin kowa ya ce wni abu Hameeda ta kalleta tace "Aunty ina *Ummeeta*?" Cike da yatsina fuska tace "Ta na ciki." Ta fad'a tana nuna mata k'ofar da ta fito, mik'ewa Hameeda ta yi ta nufi d'akin suka bi bayanta da kallo, wani d'an murmushi amaryar ta saki saboda sak ta hango Hameeda da d'anta Mu'awwaz a matsayin ma'aurata, a ganinta ba k'aramin kyau za su yi ba. Dan haka ma ta wuce inda za ta je ta na ayyana abubuwa da dama a game da ganin Hameeda, dan sam shigarta ba ta d'auketa bakin komai ba sai kawai wayewa da zamananci, sannan ta na da labarin ilimin yaran daga wajen mahaifiyarsu. Hajia *Rabi* ce ta kalli su Hadeeya tace "Ku wuce ciki kuma, kun san ana rana duka yaran su na bacci." Tab'e baki Saleema ta yi a ranta ta ayyana "Tunda an saba musu ba." Mik'ewa sukayi Hajia Rabi ta kalli mai aikin tana fad'in "Ki nuna musu inda aka gyara musu, idan su ka yi wanka sai ki kai musu abinci." Kallonta Saleema ta yi sanda suka kama hanyar d'akin tana mamakin to wankan me za su yi? Ba fa daga wani garin suke ba, tafiya ce da ba ta wuce minti ashirin ba, amma dai ba ta ce k'ala ba suka wuce cikin. *_____________* K'aramin littafin dake d'auke da kala-kalan abincin da aka mik'o masa ya girgiza kai tare d'an murmushi yace "Um-um! Nagode da wannan ma." Kyab'e fuska *Sharhasila* ta yi kamar za ta yi kuka tce "Haba dai Yallab'ai, ka zab'a mana, ni fa zan biya." D'an sunkuyar da kai ya yi kamar mai tunani sai kuma ya d'ago ya sake girgiza kai yace "Ya isa haka Baby, kin san bana son zuwa irin wuraren nan cin abinci, hasalima ni na fi jin dad'in cin abincin gida." Had'e fuska tayi tare da kawar da kai sam abinda ya fad'a bai mata ba, to ita ina za ta iya wani girki? Tabb'! Kallonshi tayi tace "Yallab'ai, amma dai ka san ba ni zan dinga girki ba idan mun yi aure ko?" Da mamaki Huzeifa ya kalleta yace "Ban gane ba? To wa zai
Chapter 8 · 0% Book details