← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 116

Sashe 55

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bacci aka saka masa bayan kwalliyar da aka she a, lallausan gashin nata daya kwanta a gadon bayanta yake kallo, aramar sar ar zinariyar data cire a wuyanta ta aje gefen gadon sannan ta zauna bakin gadon, suna ha a idanu ta saki murmushi ganin kallon da yake mata kamar na ban yarda dake ba, kamar kallo irin na fa i abinda kike son fa a kawai ( kalaman nan ko? Wasu ma da suka ce i luv u cewa aka na fa siyo sa , kai maza mutanenmu, yadda muka san motsinsu haka suma suke gane namu). Shi kanshi murmushin yayi yace "Amarya kenan, me kike son fa a ne?" Cike da kunyar ganin har ya ranfota tace "Kai Alaji, wai har ka gane akwai magana a bakina?" Girgiza kai yayi yana sake sakin murmushin yace "Amaryata, tun fa kina ar shekara sha bakwai kike hannuna, har yanzu da kika aurar da a, ta ya ne ba zan gane motsinki ba?" ar dariya tayi ta shiga rarrafowa kan gadon har saida ta zo daf da shi, hannunshi aya ta ri o inda aya hannunta ta shiga shafa kanshi da farin gashi ya fara cikawa cike da kissa ta fara fa in "Abban Mu'az, dama wata shawara ce na ke so na baka, sai dai ban san ko za ta yi anfani ba, tunda ka ga wanda na haifa ma ban isa da shi ba, bare wannan da ba ni na haifa ba, kuma ba lallai na samu darajar da dukanku zaku amince ba, amma zan fa a ko da ba zaku so in bab, ni dai na sauke ha innku daya rataya wuyana na fa a muku gaskiya." Irin kallon fahimta ya shiga binta da shi kafin yace" Uhm! Ina jinki ci gaba." ara narkewa tayi a jikinshi tace" Abban Mu'az, dama Mu'az ne yake bani tausayi wallahi tunda abun nan ya faru, kuma ka ga Mu'az ba yaro bane yana da bu atar yin aure, tunda aurenshi da Saleema Allah bai nufa ba, me zai hana a ha ashi aure da ar uwarta Hadeeya? Ka ga zumuncin da aka so ha awa a baya bai yi ba yanzu sai a sake ha awa ta nan." Tsaf ya gama fahimtar zantukanta kafin ya nisa yace "Gaskiya kin kawo shawara, kuma abinda nake so ki sani shine, ke ma fa uwa ce ga Mu'az, za ki iya zartar da kowane irin hukunci a kanshi, saidai abinda nake so ki fahimta, kinga Yayarta fa aka fasa aurenta da shi, kuma matsalar daga garemu ne, yau da a ce Saleema ce ta ce bata sonshi, ko kuma mutuwa mai raba tsakani ta auketa, ina ga zamu fi kowa murna da hakan, amma yanzu daya zama Mu'az ne ya ce ya fasa, ina ga kamar akwai nauyi mu kuma nema masa auren anwarta." Numfasawa ya sake yi yace" Amma ki bar min komai a hannuna, zanyi bincike akan lamarin, idan na fahimci zasu iya fahimtar junansu sai a bashi, amma ina ganin da kamar wuya, dan shi uzurinshi akan duk wacce za ta zamo iyalinshi ne, duk da dai na san soyayyar da yake ma Saleema ce ta kawo rugujewar auren." Da sauri ta tari numfashinshi tace" Ai Alhaji ni na lura kamar Hadeeya tana sonshi, dan na ga hakan a tare da ita, da nayi arin tambayarta kuma saboda kunya sai ba ta yarda na san komai ba, shiyasa ma ka ji nayi maganar nan." Jinjina kai yayi yace "Duk da haka, ki bar komai a hannuna zan bincika, idan dukansu sun amince sai a aura musu aure, amma ko da hakan ta kasance da gaggawa za'ayi saboda gudun matsala." A sanyaye ta jinjina kai ba dan haka ranta ya so ba tace "Shikenan, Allah ya tabbatar da alkairi." "Ameen." Ya fa a yana gyara zamanshi, shiru akin yayi na wasu shu in mintuna, Alhaji Auwal yana tunanin ta ya ma haka zata faru? A gaskiya ya so Saleema ta zama surukarshi, duk da ba wai yana in Hadeeya bane, sai dai ya fi ganin nagartar Saleema fiye da Hadeeya, dan a bayyane yake tarbiyarsu da nutsuwarsu ba aya ba ce, ko an zaman da sukayi nan bai ga wani abu a tare da Hadeeyar ba da zai zamar masa shaidar ta isa ta zama surukarshi kuma yayi farin ciki. Kwana biyu kenan da yin maganar amma Alhaji Auwal ba wani yun uri da yayi, dama ya fa a mata ne kawai dan ta shafa masa lafiya. Mu'az kuma har yanzu Hadeeya ba ta daina addabar rayuwarsa ba, ya shiryu ya koma ga Allah, babu abinda yake sai istigfari da sadaka tare da kusanta kanshi ga Allah ta hanyar yawaita sallolin nafila, amma Hadeeya tana yawan shiga rayuwarsa ta hanyar kira da turo masa hotunanta na shirme da hauka, sam yanzu kallon fuskar mata ma ya daina burgeshi, a yanzun da ya kusanci mahaliccinsa ya kuma aurin niyyar gyara halayensa, sai yake jin kamar ba bashi da sha'awa, tabbas ya yarda sallah maganin duk wata alfasha ce. Yanzu ma yana tsaka da duba wani majinyaci ta kira wayarsa, yana gani amma ya share saida ya gama duba rahaton lafiyar ashin mutumin kafin ya mishi abinda ya dace ya fita, mutumin na fita ya aga wayar a matu ar sanyaye yace "Ina ji?" Cike da sangarta da shagwa a tace "Dear tun yaushe nake kiranka baka agawa? Wai me na maka ne? Me yasa kake wula antani dan ka ga ina sonka?" Dafe goshinshi yayi ba tare da ya hassala ba yaxe "Me kike so?" Cikin turo baki tace "Magana nake so muyi da kai." arfar ajiyar zuciya ya sauke yace "Shikenan, ba zan iya zuwa gidanku ba gaskiya, saboda ina kunyar mahaifinku, mu ha u wani wurin sai muyi magana." Cike da zumu i tace "Yawwa, mu ha u gidansu awata, anjima zan je can." A ta aice yace "Shikenan, ki turo min kwatancen gidan." Bai jira amsa daga gareta ba ya yanke kiran ya aje wayar yana jan tsaki da mamakin fitina ta wannan yarinya, arama da ita amma sai iya shege cike da kai. Wayar ya sake auka ya daddana, lambar ya urawa idanu da tunanin ko ya kirata ya ji ya take? Shin tana hushi da shi ko kuwa? Ta raunata kamar yadda shima yake fama da jinya har yanzu? Ajiyar zuciya ya sauke ya jingina a kujerar yana jujjuyawa, babbar yatsarshi ya kai daidai lambar yana son dannawa amma kamar ana hanashi, kamar bazata sai kuwa yatsarshi ta danna kira wa lambar, kamar wanda ya tsorata sai ya zabura ya mi e tsaye yana urawa lambar idanu yana jin yadda take kururuwa da * innn*! Ta auki sakanni tana ruri sai kuma it! Aka yanke kiran. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil!" Ya ambata tare da lumshe idanu ya koma ya zauna, sake aika kiran yayi amma aka kuma yankewa, daya aika na uku ma sai aka ce wayar a kashe take, matse bakinshi yayi guri aya yana ayyana "Na san haka za ta faru dama, Saleema mai aji ce da kuma kunya." Rufe ya rufe idanu ya jingina sosai yana juya kujerar yace "Ya Allah ka bani kamar Saleema, ita kuma ka bata wanda ya fini da komai, Ya Allah ka bata wanda farin cikinta zai fi dukiya mahimmanci a gareshi." Da kanshi kuma ya amsa da "Ameen ya Allah." *Saleema* kuma kiran farko wayar na hannun yara suna wasa, mi o mata sukayi tana ganin kiran ta yanke tare da jan tsaki ta ayyana "Me kuma zan maka? Da in baki zaka min Mu'az, na sanka fa." Har za ta mi awa yaran wayar ya sake kira, sake katsewa ta yi ta tashi ta shiga akin Aunty Lubna, na uku ma haka ta yanke tare da kashe wayar gaba aya, kan gado ta zauna ta urawa wayar idanu tana kallo, ar rayuwar da sukayi da shi take tunawa, irin so da aunar da yake nuna mata a zahiri, yanda baya hushi duk abinda za ta masa, wasu lokuta ba gaira ba dalili za ta hassala amma sai ya nuna shi fa ba komai bane, karshe ma ya ige da bata ha uri, tabbas ya koya mata sonshi, a lokacin da bata tunanin komai sai rayuwa da shi, sai kawai ya nuna mata ita ba ajinsa ba ce ba zai iya rayuwa da jahila irinta ba (wato ita abinda ta auka kenan), dan cuta kam ta yarda ya cuceta, amma kuma ba ta ri eshi ba ta yadda zata gagara yafe masa, can ya je shi da halinsa. *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:50 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _32_ Tunda ta shiga dosowa inda yake tsaye shi da Zeid yake are mata kallo, wani murmushi ya samu kansa da yi shi ka ai, ko dan Allah ya fara ganar da shi gaskiya ne? Gaba aya sai yake ganin bayyana tsiraici yanzu a matsayin auyenci da rashin kunya, sam babu wani abu da yarinyar ke yi dan ta birgeshi da yake birgeshin, yanzu haka kwalluya ce ta ban mamaki tayi, amma sai ta zama abar dariya ba da kuma mamakinta da yake, a ganinta za ta birgeshi har ya amince da wautarta, to shi wace lalacewar ce za ta sakashi auren anwar Saleema? Ai ba Hadeeya ba da ya tsaneta wacce duk ita ta zama silar komai, ko Hameeda da yake ganinta bata shiga abinda bai shafeta ba ba zai iya ba. an zungurarshi Zeid yayi yace "Abokina, idan kai baka sonta ka min hanyar aurenta mana, ni ta min a yadda ta zo in nan." Da mamaki ya kalkeshi yace "Ba ka ce ar islamiya kake so ba?" Cike da basarwa yace "Kai dai a fara da wannan in." e baki yayi ya girgiza kai ya maida dubanshi gareta sanda ta araso da fadin "Sannu." Kallo mai kama da harara ya bita da shi jin ta kallesu duk sun haifeta amma ta ce musu wai sannu, da fa Saleemarsa ce sallama za ta yi kanta a sadde, sannan ta ce "Ina wuninku." Amma dake halayen ba aya ba, numfashi kawai ya
Chapter 55 · 0% Book details