← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 116

Sashe 26

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na anfanar ar mutane kamar wata matarka, yanzu ka addara kai ne mijinta ka sameta a haka, ya za ka ji?" e baki yayi ya yatsina fuska cike da sha iyanci yace "Sam, ki ma daina kwatanta azamar can da zamowa matata, kuma abin da ya faru ai biyanta na ke, ba dole na mata ba." Cike da takaici Saleema ta mi e tsaye tana ri e wayar hannunta da kyau wacce ta ji shigowar sa o tana kallonshi tace "Ka sani al awarin Allah ba ya tashi, wallahi kai ba ka isa ka lalata rayuwar an mata ba son ranka, sannan idan ka tashi aure kace kamila nutsatsiya ka ke bu ata, dole ka girbi abin da ka shuka, arnar da ka fara kuma kai ne za ka arasata." Sama da asa ta dalla masa harara ta juya za ta bar wurin, cak ta tsaya saboda idanu da suka ha a da Mu'az na tsaye a bayansu, ganinshi tsaye ya sa Mu'awwaz shiga taitayinshi ya fara sadda kai asa yana kame-kame da sosa eya. e fuska ta sake yi ta aga afa da niyyar wucewa ta barsu, sai kuma Mu'az da fuskarshi ta nuna alamar tashin hankali ya fara takowa da sauri yana nufota, irin yanda yake tahowa gaba aya sai take ganin kar dai ya rumgumeta, baya ta fara ja a hankali amma ya na ci gaba da nufota, ba tare da sani ba ta kai wa Mu'awwaz karo a bayanta da sauri ta juya ta kalleshi, sai kuma ta juyo a hassale inda Mu'az yake cike da acin rai tace "Mu'az wai me ye haka? Ka na l..." Nuna mata Mu'awwaz ya yi fuskarshi auke da fushi yace "Me ye tsakaninki da wannan yaron?" Da mamakin tambayarshi ta wara idanunta ka an a saman fuskarshi tace "Kamar ya me ye tsakaninmu? Me ka gan..." Tsawar da ya daka mata ta hanyar nunata da yatsa yace "Ke!!!" Ya sa ta ruf da bakinta ta rintse ido, sai kuma ya sha o wuyan rigar Mu'awwaz ya fincikoshi gabanshi yana kallonshi yace "Me ye tsakaninka da matata?" Turnu e fuska Mu'awwaz ya yi yana son watar kansa yace "Ni ba komai tsakanina da ita, magana kawai muke." "A kan me kuke maganar?" Ya fa a a tsawace, Saleema da ta koma gefe tana kallonsu ce tace "Amma ai bai shafeka ba." Gam-gam! Ya sake matse wuyan rigar Mu'awwaz bayan ya kalleta sannan ya kalleshi yace "Me ka ke fa a mata?" Cikin jin haushi Mu'awwaz yace "Wai me ye haka? Na fa a maka ba komai, me zan mata ne a tunaninka?" Cikin acin rai yace "Saboda na san halinka, na san duk iskancin da ka ke a garin nan, zuba maka idanu na yi kayi saboda rayuwarka, amma ka ga wannan?" Ya nuna masa Saleema dake gefe sannan ya ci gaba da cewa "Matata ce, wannan ta fi arfin ka mata iskanci Mu'awwaz, wallahi idan ka kwatanta yin haka sai na fizge abin da ka ke ta ama da shi a jikinka wajen fa awa an mutane." Hanka ashi ya yi da arfi har saida ya fa a kan kujera, har zai juya sai kuma ya sake juyowa da arfi ya sake fincikoshi ya mi ar da shi tsaye, ta e masa baki ya yi ya an matsa fuskarshi sosai kusanshi ya shinshina bakinshi har zuwa wuyanshi, Mu'awwaz na ganin ya fara shinshinarshi ya fara sissine kai a tsorace, da ma aukakin mamaki Mu'az ya kalleshi sosai yace "Mu'awwaz sigari ka fara sha?" Da sauri ya girgiza kai yace "A'a wallahi." Sakin wuyan rigarshi ya yi tare da fara cajeshi yana laluba duka aljijunanshi daga na gefe-gefe har na baya, ai kam sai ga kwalin sigari da ma yasta, cirosu ya yi ya shiga are masa kallo yace "Mu'awwaz bayan neman matan yanzu kula shaye-shaye za ka fara? Wai me ka ke neman maida rayuwarka ne? Ka kuwa san illar haka?" Saleema dake gefe tana kallonsu kiran da Mamanta ta mata dan ta tambayeta ko ta ga lambar ne ya sa ta juyawa da niyyar barinsu nan su ci kansu idan suna so. Mu'az da dama ya ke son kora mata kashedi a kan tayi nesa da anin na shi a zafafe ya gusa daga wajen Mu'awwaz tare gabanta yana kai hannu kamar zai ri e hijabinta, kallon da ta aika mishi yasa shi dakatawa ya sunkuyar da kai yana aga hannu alamar saranda yace "Shikenan na gane, kinga ni na miki al awarin zan kiyaye ta aki har sai bayan aure." Sai kuma ya kalli fuskarta yana sauke numfashi kamar wanda ya yi gudu ya nunamata inda Mu'awwaz yake da idanu yace "Kinga wannan?" Wayam! Ba Mu'awwaz har ya bar wurin, ba tare da ta auke kanta ba ta ci gaba da kallonshi da mamakin shashe ar da yake, orawa ya yi da "Saleema dan Allah ki kiyaye shi, wallahi bai da mutumci ko ka an, kinga idan kina tsayawa tare da shi komai zai iya faruwa, Saleema ni na san Mu'awwaz wallahi har ta arfi zai iya yi miki abin da bana so." Wani kallo ta jefeshi da shi tace "Me ye baka so in?" Sadda kanshi yayi kamar mai jin kunyarta yace "Zai iya yi miki iskanci." "Hummm!" Ta fa a tana ra ashi tace "Nagode da kulawa." Da kallo ya bita har ta an yi nisa sai kuma ta juyo tace "Wata ila a gunka ya koya." Da wani tattausan gudu ya tare gabanta da mamakin maganarta, iska ya feso ya na tunanin wace irin jarabawa ce Ubangiji ke masa haka? Shin dan ya kasance mai ta a jikin macen da ba ta halatta gareshi? Shi ne Allah ya jarabceshi da wannan waya ayan tak? Shi bai ma ta a sanin ana son mutum lokaci aya haka ba sai yau, a kwana uku da sukayi gidansu kawai haukacewa yake neman yi, ba kuma shine farkon da ya fara saninta ba, a'a ya santa jimawa dai ake ba'a ha u ba, wannan ikon Allah ya fi gaban wasa kam, gashi sai ta mishi wauta da kato ara, amla sai ya ji ya ha e ranshi bai ace ba ko aya. Yanzun ma dai bai ji haushi ba, sai ma ance idanu da yayi cike da son ta yarda da shi yace "Wallahi Saleela ni ban ta a sanin wata a mace ba, shiyasa na fa a miki ki nemi za in Allah a kaina, idan kika ji gamsuwa a kan hakan ki fa a min, na miki al awarin sanar da ke komai da ya shafeni, kuma wallahi gaskiya kawai zan fa a miki, amma ki yarda dani Saleema ban ta a zina ba, ke ce mace ta farko da na ke so na fara sani a rayuwata bayan aurenmu." Wani irin fa uwar ne ya ziyarceta sakamakon abin da ya fa a, hakan yasa ta gyara tsayuwa ta ance idanunta tace" Mu'az, yanzu idan aka ce ba na da wannan abun da ka ke tunanin samu a tare da ni, anya kuwa za ki iya zama da ni a haka?" Tsurawa fuskarta idanu yayi yana kallo, saida ya mayar da wasa gefe cike da bata tabbaci yace" Ban san ta ya ne zan kwatanta miki yanda na ke ji ba, amma nan..." Ya fa a yana ora hannunshi na dama akan daidai zuciyarshi sannan ya ce" Gaba aya na ke jinta ta ki ce, duk wata bugawarta aya da sunanki take amsawa, walwata a yanzu ba ta tunanin komai sai ke kawai, a yanda na ke ji Saleema zan iya rayuwa da ke ko babu wannan abun da kike tunanin shi ne ka ai na ke so, ban ta a sha'awar macen da ban ga jikinta ba, amma ke jinin jikina a sanyaye yake tafiya idan na ganki, ina da sauri a kan komai, amma akan lamarinki sanya nake tamkar gajiyayyan matafiyi, Saleema, a duk duniyar nan ke ka ai ke da alhakin gajiyar da ni." Ita ba *dutse* ba ce, hakan yasa a karo farko maganganun Mu'az sukayi matu ar tasiri a zuciyarta, dan hatta da tsigar jikinta saida ta dinga tashi, sa on ya ratsata matu a, babban abun tunaninta shine, dama a haka da mahaifinta ke kusheta akwai wani namiji da zai so ta a haka? Yanzu duk kalaman nan nata ne ita ka ai? Son da yake mata har ya kai haka dama? Yadda ta ke kallonshi ne ya sa shi yasta yatsunshi biyu yace "Matata ya dai?" Da sauri ta zabura tana kallonshi, sai kuma ta kalli wayar dake hannunta ta nuna masa tace "Zan...ina zuwa, zan amsa waya." Da sauri-sauri ta ra a ta wuceshi shi kuma ya bita da kallo, saida ya ga shigewarta akinsu ka ai ya juya ya fita shi ma fatanshi aya Allah ya orashi a kan yarinyar nan dake wofantar da shi, irin yanda mata ke mararinsa suna kawo kawunansu gareshi, da yadda idan ya na wasa da mace take baje basirarta dan son ganin ya isa babbar fada, babu irin salon munafurci da kisisinar da ba'a masa ba dan ya fa a tarko, amma ya dage ya nuna a'a fa, har saida ya ta a samun kanshi yana daf da afkawa amma ya ce a jira sai ya nemo kororon roba saboda tsaro, daga ranar bai kuma ha uwa da yarinyar ba dan a ganinshi wani abun ta ke da da yasa ya kusa wuce gona da iri ranar. *Duk* abin da ke faruwa a idanun Hadeeya wacce ke sama fitowarta daga akin amarya kenan ta hangesu, la ewa ta yi tana kallonsu, irin yanda Saleema ke mishi magana kamar da gadara da isa, shi kuma yana ta wani sussunkuyar da kai, hakan sai ya sata tunanin to me ye a tsakaninsu? Ba ta iya samun amsa ba dan ba ta jin me suke fa a, saida ta ga kowa ya bar wurin sannan ta sauko ita ma da tunanin me ye wai? Soyyaya suke? Ko kuma dai wani abun ne na daban?. Lambar Khairat ta kira, bayan sun gaisa ta fa a mata ita ce, orawa tayi da cewa "Yawwa Khairat, ai nan da kwana hu u ne saukar makaranta ko?" Daga angaren Khairat ta amsa da "E, muna ta shirye shirye
Chapter 26 · 0% Book details