← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 116

Sashe 9

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi? Ni?" D'an murmushi ta yi cike da shashanci tace "A'a haba, ina nufin sai mu samu yar aiki." Iska ya feso a bakinshi yana jin wani b'acin rai na hauhawa masa, to shi bai san wane irin aure ne za su yi da Sharhasila ba, dan tana tak'amar ita yar mai kud'i ce, kuma ita ta nunashi ta ce tana so, sai ya zama zai zaunata mulkeshi ne? Abubuwa na hauka da kidahumanci ta ke kawo masa fa, wannan wane irin abu ne? Kallon kyakyawar fuskarta ya yi wacce ta fad'a masa wuni ta yi wajen gyaran jiki da kwalliya wai dan za su had'u wurin cin abincin nan kawai wanda shi a wajenshi bai da wani anfani, cikin tausasa murya yace "To me yasa ke ba za ki dafa ba?" Turo baki ta yi irin shagwab'ar nan cikin harshen faransanci tace "Amma Bebe ai kasan ni aiki nake zuwa ko? Yaushe zan maka girki sannan na yi aikina? Ba zan iya ba gaskiya." Shi ma a harshen faransancin yace "To ai macece ke, kuma ba'a yi auren ba, zaunawa za ki yi kafin lokacin ki tsarawa kan ki rayuwarki, kar ki maida hankali kan abinda ba zai anfani lahirarki ba, Sharhasila wannan aiki da kike moriyarki da shi iya duniya ne kawai, idan ki ka fi k'arfin shed'an ne za ki nemi lahirarki da aikin, dan haka a ganina tun ba'a d'aura aurenmu ba ki tsarawa kanki komai ta yanda za ki ba wa komai lokacinshi yanda ya kamata." K'ank'ance ido yayi sosai ya na ci gaba da kallonta yace" Kin san wani abu? Mutum ne ni mai matuk'ar son kulawa, hakan yasa mahaifiyata ke fad'a min wai wasu lokuta kishi nake da k'annaina..." Yar dariya ya yi ya d'ora da" Gaskiya ne, sai na ji idan ina magana da ita bana so kowa ya mana kutse bare a tilasta mata raba hankalinta gida biyu, sannan ina da matuk'ar son abincin gida, ma'ana ina son abinci irin su tuwo, d'an wake, faten doya, biski, dambu...da sauransu." Tsareta ya yi da ido yace" Da fatan dai duk kin iya wannan? Idan ma ba ki iya ba ina fata za ki koya saboda ni." Tunda ya fara magana ta zuba masa ido ta na kallo, dogon bayanin nan da ya zauna ya na mata sai ta ji kanta ma ya fara ciwo, to ita kam ta rasa hadisi na nawa ya karanta mata, a gaskiya ba ta ma gama fahimtar zancen shi ba, dan haka ta na buk'atar k'arin bayani. D'an gyara zama ta yi tana kallonshi tace "Bebe ban gane ba, ka min dalla-dalla mana, ka na nufin ni ma sai na koyi iya tuk'a tuwo kenan?" Murmushi ya mata yace "B za ki iya ba kenan?" Kawar da kai ta yi tana nazari na wasu dakik'u, a gaskiya duk yanda take so da k'aunarshi ba za ta iya wannan wahalar ba, amma kuma sanin waye Huzeifa ya sa ta d'an yi wata shawarar, tunda dama ba shi ya fara cewa ya na son ta ba, ita ce ta ji ta na k'aunarshi saboda kyawawan halayenshi har ta masa tayin soyayyarta, da fari kam ya nuna baya ra'ayi saboda kasancewarta 'yar mai kud'in unguwarsu, amma da ta dage ya kuma shawarci mahaifiyarshi sai ya amince har yanzu suke shirin zama mata da miji nan da kwanakin da ba zasu gaza goma sha biyar ba. Dan haka ta kalleshi da murmushi a fuskarta tace "Bebe, ai kasan soyayya ta sa na ce ina sonka, dan haka ba abinda ba zan iya yi maka ba." Fad'ad'a Murmushin shi ya yi yace "Nagode sosai, ai na d'auka ba za ki yi ba." Da irin zolaya tace "Ni na isa? Idan fa ka fasa aurena?" Dariya ya yi cikin tattausar muryarshi yace "Ba zan fasa aurenki ba, sai dai na miki kishiya bayan auren." Zaro ido ta yi ta dafe k'irjinta cike da tashin hankalin da ya ziyarceta lokaci d'aya tace "Bebe, dan Allah ka daina min irin wasar nan bana so..." Tsal! Ta taso daga kan kujerarta ta dawo kusa da shi sai dai dake babu wata kujerar sai ta durk'usa k'asa ta rik'o hannunshi, da sauri ya d'an jaye hannunshi saboda gudun matsala, dan baya son ya sake shiga halin da ya shiga d'azu daga kallon wata. Sake rik'o hannun na shi tayi ta rik'e gam tana kallon idonshi da na ta idon da sukayi jajir suka tara ruwa alamar kuka, cikin rikitacciyar murya ta dinga mitsika hannunshi ta na fad'in "Ka na ji ko B ? Dan Allah ka daina irin haka bana so, ka ga ba zan iya kishi da wata a kan ka ba, dan Allah ka min alk'awarin ba za ka tab'a min kishiya ba?" Da mad'aukakin mamaki ya kalleta sosai ya na nazartarta, daga bisani numfashi ya sauke yana ci gaba da kallonta yace" Tashi ki zauna, kina ga fa kallonmu a ke." "Ni ban damu ba su kallemu, ka min alk'awari ka ji mijina." Ta fad'a da alamar fashewa da kuka, jinjina kai ya yi yasake nuna mata wurin zaman da d'aya hannunshi yace "Dan Allah ki zauna sai mu yi magana." Da sauri ta mik'e ta zauna ka kujerar ta zuba mi shi ido ta na kallo kamar wanda take son gano ta inda yake fitar da numfashi. A hankali Huzeifa ya d'an girgiza mata kai cikin sanyayyar muryar da hakan d'abi'arsa ce yace mata" Ba zan iya miki wannan alk'awarin ba *Sharha*, saboda ni d'an adam ne ban san me Allah ya tsara min a gaba ba." Jin hakan daga bakinshi ya sa ta fashewa da kuka da iya gaskiyarta kawai ta kifa kanta a kan teburin, cike da damuwa da jin tana muzantashi cikin mutane ya k'ara tausasa murya yace" Dan Allah Sharha ki daina kukan nan, kin ga tashi mu bar nan in dai kuka za ki min." Kamar ba ta san ya na yi ba haka ta dakeshi, mik'ewa ya yi ya sake maimaita" Tashi mu je na ce." Nan ma shirun ta masa, ranshi ne ya d'an fara b'aci dan haka ya zagaya kusanta ya d'auki jakarta da wayarta da makullai dake aje, bai tsaya jiran komai ba ya finciki hannunta suka fita a wajen dan shi fa duk taushinshi mutum ne kuma da baya son iskanci, sam ba zai lamunci ta mayar da shi wani lusari ba dan baya da kud'i sannan *mad'inki ne* shi, haka kawai ba za'a raina masa wayo ba, ta ya ma zai mata wannan alk'awarin? Ta san me alk'awari yake nufi a shari'ance? Ta san me zai faru da shi idan Allah bai nufeshi da cikawa ba? Ba ma duk wannan ba shi fa gaskiya *mace mai addini* ya ke da burin samu, hakan yasa ya ke tunanin ko ya aureta idan bai sameta yanda ya ke buk'ata ba to indai ya samu halin k'ara aure to zai k'ara, sai kuma ta nemi katse masa hanzarinsa da wani tunaninta irin na hayudawa haka kawai. Tuk'i kawai yake a motar ta ya na kallonta jefi-jefi, yanda ta d'aga hankalinta akan tashin d'aukar mata alk'awarin nan da irin kukan da ta yi, a ganinshi ko iyayenta aka ce sun rasu iya hakan ne kawai za ta yi, idonta sun yi jajir sosai sun kumbura abu ga jar fatar da ba ta saba da hayaniya ba. Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon gabanshi yace "Ki yi shiru Bebe, kukanki fa ya na tab'a min zuciyata sosai." "To idan ka hakane ka min alk'awarin mana." Ta fad'a kamar za ta matso daf da shi ta sumbace shi, d'an tab'e baki kawai ya ui ya girgiza kai bai ce mata komai ba, cikin tausa murya tace "Bebe me ye a ciki ne wai? Alk'awari fa kawai za ka d'auka da fatar baki." Wata nauyayyar ajiyar zuciyar ya sake saukewa yace "Sharhasila hadisin Anas d'an Malik fa ya ji daga bakin Manzon Allah (S. A. W) ya ce" Alamomin munafiki guda uku ne, idan zai yi magana sai ya yi k'arya, idan ya yi alk'awari ya sab'a, idan aka amince mi shi ya ci amana..." Kallonta yayi fuskarshi d'auke da damuwa sosai yace" Duka wannan alamomin za su tabbata a kaina idan na miki abinda kike so yanzu, na farko idan na fad'a miki ni na san k'arya na miki har cikin raina, idan kuma ban cika alk'awarin ba kin ga na sab'a, sannan na ci amanar yardar da kika min, to me ye ribar hakan? Me zai sa na jefa kaina a wannan halakar ? Alk'awari d'aya da zan iya yi miki shine, ko bayan aurenmu zan zama mai mi yi miki uzuri, sannan ko da Allah ya jarabceni da k'ara aure, to zan ci gaba da kare martaba da kimarki a idon d'ayar, ba zan tab'a bari ki zubar da hawaye ta dalilina ba kuma da sanina, sai dai abisa rashin sani, wannan alk'awarina ne gareki." Wata arniyar harara ta maka masa ta gefen ido dan ita sam abinda ya fad'a ta kunnen da ya fi kusa da shi ya shiga ko d'ya kunnen bai kai ba ya fita abunshi, ya zai tsareta da wasu zantukanshi na daban kawai da wasu tatsuniyoyi? Ba ta ce mishi k'ala ba har suka isa k'ofar gidansu. Fita duk sukayi inda ta zauna mazaunin dreba shi kuma ya kalleta yace "Ni zan idasa gida a k'afa, sai da safe." A shagwab'e tace "Ba za ka kirani ba?" Shafa sumar kanshi ya yi yace "E to...kin san fa jibi za mu fara jarabawarmu (BAC) karatu yayi zafi sosai, amma dai zan kok'arta na kiraki." Turo d'an k'aramin bakinta ta yi tace "Tom, sai na ji ka." Da haka suka rabu ita ma ta shige k'aton gidansu kowa da abinda yake ta sak'awa da warwarewa a zuciyarshi, inda Huzeifa ya fi maida hankali kan irin zaman da zaiyi da yarinyar da take ganin mahaifinta mai kud'i ne, shi kuma d'an ladanin da ya rasu ya barshi da nauyin k'annanshi da mahaifiyarsu wanda ya ke ciyar da su ta hanyar d'inkin da yake d'an samu idan ba ya karatu, yarinyar da aka ma hanya duk da takardunta ba su kai ba amma take aiki a babban reshen kamfanin shiga da fitar kud'i na *Al'izza*,
Chapter 9 · 0% Book details