← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 116

Sashe 72

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yayi ya juya zai barshi yace" Nagode." shigewa yayi mota ya barshi nan tsaye tamkar baya da rai, Mamanshi ce suka araso ita da Fareeda suna tafiya kamar basa san taka asa, suna zuwa Maman ta ce" Muje ko Huzeifa, mu zamu je gida, amma kai ka je asibitin dan sanin me ke wakana." A sanyaye ya girgiza kai hawaye masu zafin gaske na kwaranya a idanunshi yace" A'a Mama, ba bu atar hakan, muje gida kawai." Da kallo suka bishi sanda ya arasa bakin titi yana son tsayar da adaidaita sahu, bayanshi suka bi da tunanin tabbas akwai abinda mahaifinta ya fa a mishi dan sun hangesu tare suna magana. *Suna* isa asibitin wasu sabin gwaje gwaje aka mata, oxygen aka saka mata da zai taimaka mata wajen numfashi ga kuma na'urar dake arin daidaita bugun zuciyarta, tuni aka kusa saka mata wasu ruwan bayan sun tabbatar a yanzu bata bu atar jini, sai allurar tetanus da suka mata saboda arfen da ya shiga jikinta. Duk da haka sai wajen 12:00 dare Safiya dake tare da ita da Alhaji Yusuf dake auke da Ahmad a kafa a suka ji na'urar na ara sosai tin! Tin! Tin! *Alhamdulillah.* 14/06/2022 12:41 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _39_ Da yardar Allah ta farfa o kuma tana kar an kulawa daga hannun manyan likitoci, kwana biyu da faruwar hakan aka mata ecographie dan tabbatar da babu wani abu a kayan cikinta da ya samu lahani, ganin komai lafiya ba wata matsala sannan hankula suka an kwanta. Saidai Saleema ta lura mahaifinta na awainiya da ita ne amma baya son ko kallon fuskarta, hakan na damunta sosai sai take ganin hushi yake da ita mai tsanani, kuma hakane tabbas hushi yake da ita, haka take jinyarta har yau da aka sallamesu zasu koma gida bayan kwana goma sha aya. Safiya dake goye da Ahmad tana tattara kayansu mai aiki na kaiwa mota dake jiransu waje, tana zaune bakin gadon wayarta a hannu tana ta tunanin dalilin da yasa Huzeifa baya aga mata kira, yanzu idan ma ta kira sai ya dawo alamar ya saka lambarta a ba in jadawalin kenan? To me ta masa? Ko kuma me ta musu? Ko aya ba wanda ta gani a asibitin da sunan ya zo dubata, duk da dai asibitin na da lokacin shiga da fita, amma dayawa da suka zo dubata ai sun ganta, duk da ana hanawa shiga sai da bibbiyu. Kallon Mamanta tayi tace "Mama, Fareeda ko Mamansu wani bai zo ba?" A hassale Safiya ta juyo ta kalleta tace "Saleema karna sake jin kin ambaci mutanen nan, mahaifinki a hassale yake game da ke, ki rufawa kanki asiri." Narai-narai tayi da idanu sun cicciko da wala, bata ha ura ba haka ta dinga kiran lambar Fareeda ma amma ita ma ba'a samu, saida suka isa gida ka ai ta aje wayar ta shiga wanka. *Komai* ya tsaya mata cak, gidan da take wuni a cikinsa babu da i, ina kwana yanzu sai ta ce wa Abbanta amma kallo bata isheshi ba, ga Mamanta kanta data lura ba wani walwala tsakaninta da mahaifinta, idan ka ga suna hira tsakaninsu to akan Ahmad ne da yanzu har aukarshi yake su fita, kuma Maman ta fa a mata duk ita ce sila. Ita ba zuwa islamiyya ita ba makarantar boko ba, tunda Hadeeya ta haihu ta shirya tare da mutane zasu tafi ya ce su suje amma ita ta zauna gida, sannan ko ofar gida bai yarda ta kuma zuwa ba saida izininshi, haka akayi hidimar bikin Hadeeya sai ranar suna ka ai ta je, shila a bayan idanunta waran kashedi ya ma Safiya wacce uta ce tsaye akan lamarin haihuwar Hadeeyar da ya shafi su iyaye cewa idan har ta yarda Saleema ta je wani wurin ko kuma ta wuce arfe shida ba'a gidan nan ba tayi kuka da kanta. Sai ga ta a wajen bikin nan a takure, musamman dangin mahaifinsu da aka dinga mata wani kallo sai ta tsargu zuciyarta ta karye ta dinga kuka. Nafissa dama ba ta samu zuwa bikin ba saboda tana kwance asibiti akayi, tana so ta je ta ga jaririya amma ba dama, hakan yasa zaman take jin shi tamkar ar kurkuku. _______________ Iko da iko, ku i da ku i ne suka ha u a shari'ar, hakan yasa da fari kowa ke gudanar da lamarin da izzar ji da kai da burin kare nashi, amma da Alhaji Auwal ya ga lamarin bun asa zaiyi sai ya shawarci Alhaji Yusuf in ya bashi ha uri, da wannan aka rufe matsalar aka sallami Sharhasila da tausayawar cikin dake jikinta ga kuma mijin da tayi dominshi ya saketa, saida ya sake jadadda musu su fita a harkar arsa kafin aka rufe wannan matsala saidai da shara in idan Sharhasilar ta sake aikata wani abu to fa ba maganar gyara, dan ita in dama mai laifi ce dake yawan lahanta mutane, dan haka hukuma ba zata sake mata wani sassauci ba. Ai ko mahaifinta ya yarda da hakan, dan ya fara gajiya da iskancinta, ku in da ya kashe dalilin case din nan Allah ka ai ya san su, dan duk inda yaje yana neman kamun afa ku i yake saki na mamaki tunda shi ma mahaifin yarinyar da yafi su gaskiya ba aramin wallo ba. Daga zuwansu gida ta shirya ta ce ai wajen Huzeifa za ta je, mahaifiyarta kamar za ta mutu dan ba in ciki, ba sunan da bata kirata da shi ba na mayya marar zuciya, amma ta ce ta ji ta gani ai uban anta ne da yake cikinta. Ai kam ta yarda da abinda Mamanta ta nusar da ita, dan tana zuwa Mubarak yayi tsaye kan ba za ta ga Huzeifa ba wanda ke kwance akin Mama ba lafiya, da ta so yi mishi hargagi shine ya auki muciya ya rantse da Allah kan zai ci uwarta, kuma ga Mama zaune amma ba ta yi yun urin hanashi ba, uwa uba Fareeda dake ta jinjina kai alamar e ta yarda ya ci uwata, sai kawai ta fita tana sababin ai ba zasu rabata da shi ba tunda cikinshi ne jikinta, ko an i ko an so ita da Huzeifa sun zama aya. *Rayuwa*, me ye ma rayuwar? Numfashi? Yau da gobe da jibi? Lokaci ko yanayi? Duka zata auki kowace ma'anar, dan kuwa a cikin kowane fitar numfashi na Saleema yanzu tare da gunjin kuka yake fita, inda yau da gobe suke ara cinye mata lokacinta suna riska yanayi mabambamta, daga zafi zuwa sanyi, daga sanyi damuna, komai nata ya tsaya cak yayin da duniyar ta mata juyin waina. A yanzun da take fuskantar rayuwa da hushin mahaifinta, sai duniya ta sake mata zafi har idan ta ora goshinta da sunan sujada take ro on Allah ya kawo mata miji na gari tayi aure ta bar gidan, dan ko yanzu alamu nunawa suke sai Hameeda ma tayi aure ta barta a gidan saboda samarin dake gosulo a kanta kullum, ita kuma bata ma fita ba bare ta samu, dama can kuma bata da farin jinin da samari suke tsayar da ita a titi. Sannu sannu aka cinye shekaru har *uku* ba wani canji daga rayuwar Saleema, duk wani da ya shigo rayuwarta a anin lokaci ya fita ya barta da tunanin baya, a shekaru biyun nan ta samu labarin haihuwar matar Huzeifa daga bakin Fareeda data canja layi bayan aurenta ta kirata, ita kanta Fareeda yanzu haka tana goye da yaronta, haka ma Huzeifa ya sake wani auren a aramin gidanshi da ya samu ya gina, kuma har yau Sharhasila tana zawarcin ya dawo da ita gidanta amma ya i, ta yi tarko da ansu dan ya maidata amma abun shiru, ya yarda addarar yaron nan ce ta addara masa aurenta, amma bayan haka baya ko tunanin sake rayuwa da Sharhasila. Haka ma Mu'az yayi aure shekara aya kenan da wata ar uwarsa ta wajen mahaifiya, ya rumgumi addara da kuma matarshi suna zaune lafiya, sai dai zancen mance Saleema bai taso ba, dan ita kanta matar ta san da zaman Saleema kuma tana kishi da ita a oye, dan ranar da ta nuna a zahiri saida ya kusa korata gidansu, wai a kan me zata yi kishi da wacce ma ta manta da shi? Sannan Saleema ita ce silar shiryuwarsa har ya zama mutum da ta gani ya birgeta ta aura, dan haka yanzu ta daina nunawa saidai a yi wasa da dariya har ta nuna masa tunda tana nan ba ta yi aure ba ka je ka aureta mana, sai ya girgiza kai yace "Hallacinta a gareni ya fi arfin na saka mata ta hanyar tilasta mata ko zuri'arta biyan bashina." Mu'awwaz ma haka shi da Nafissa sun inke wuri aya a zahiri, yau lafiya ne gobe ba lafiya, yanzun nan suna shiri amma abu ka an sai ya nuna zarginta yake ko ita ta nuna bata yarda da shi ba, amma a zahiri musamman gaban Gaishata sai Nafissa ta yi sanyi tamkar ba ita ba, amma a ba ini tamkar zasu ci junansu anyu, a haka har ta ara samun wani cikin ta sake haihuwar mace, kuma har yau Gaishata ba ta aunarta kuma bata aunar yaran, hakanne yasa har yau wutar dake ruruwa a zuciyarta game da Saleema ba ta mutu ba, ta yi ta yi Mu'awwaz ya ara aure ya ce shi fa da uruciyarsa lalurar mata biyu ba zata kasheshi ba, dan haka duk sanda ta kalli Nafissa ko anta saita zageta sannan ta zagi wacce ta zama silar auren. A shekara ukun nan Papi ya rasu, ga haihuwar Khairat da ita ma da yar Abban Saleema ya barta ta je, yanzu haka wata uku kenan da akayi auren Hameeda wacce kammala jami'a, auren Hameeda bai ma Saleema ciwo ba, saidai ya sa ta zubar da hawaye, dan gaba da gaba dangin Abbansu suke nuna ita fa tayi nauyin afa da har yanzu ba ta yi aure ba, abinda ya sakata zubar da hawaye bai wuce ar uwar mahaifinta data
Chapter 72 · 0% Book details