Sashe 95
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wa'azantarwa kowa ke sauraro kuma suna aukar abinda yake tunatar da su in. Saida ya zo rufewa yana addu'a ne kowa ya gane lallai shi in sarki ne ba irin sauran ba, sarki ne da ya san akwai na gaba da shi, domin kuwa addu'a yake daga zuciyarsa muryarsa na rawan dake nuna kowane lokaci zai iya fashewa da kuka gaban mahaliccinsa sarkin sarakuna, kafin daga bisani a are aka tayar da sallah. *A minti ashirin* aka gama sallah bayan ya juyo wa anda ke bayanshi suna an gaisheshi, ido hu un da yayi da malaminsa dattijon arzi i yana zaune ya jingina a bango da alama ba yanzu zai fita a masallacin ba yasa shi mi ewa a nutse, da sauri dogarai suka mi e suka rufa masa baya suna baza manyan rigunansu, wani kallo ya aiko musu daya nuna baya bu atar rakiyarsu, hakan yasa suka zube asa dan cikin masallaci suke ba filin fada ba. arasawa yayi gabanshi tare da neman guri ya zauna sukayi musabiha, sosai suka gaisa da dattijon mai dattako yana tambayarsa al'umaran rayuwa, ta aiciyar nasiha ya masa da "Ka ji tsoron Allah, ka tuna akwai iyama, wuta gaskiya ce haka ma aljanna gaskiya ce, Allah ya tayaka ri o da hannayenka, Allah ya oraka akan ma iyanka." "Ameen, nagode sosai." Ya fa a yana sadda kanshi asa kafin ya fara tattara alkyabbarsa zai tashi, a nutse ya mi e gaba ayansa ya shiga takawa a lokacin da mutane ke ta fita a masallacin. Kafin ya isa ga dogarai dake jiranshi wani arfan matashin da zai wuce shekara talatin da biyar ya tunkaro tamkar za su yi sa ani, sai dai suna daf da juna kuma babu wanda ya hanashi tunkararshi dan akin Allah suke kuma mutane na ta fita ne ta ofofi ukun dake cikin masallacin bayan ta shigowar sarki. aramar wu ar da suka ha ata da mummunar gubar da tana ta a mutum sai dai idan Allah ya tsare kawai ya zaro daga aljihun rigar yadinshi ya cireta a cikin gidanta ya nufi soka masa ita a ciki duk da an bashi tabbaci ko ya yane ya tabbatar dai ta yanki jikinshi, da zarar gubar ta shiga jininshi to an gama. Tuni Abdus-samad ya ankara da wannan balagaggen namiji, da salo irin kwarewa ya yi saurin ra e jikinshi hakan yasa hannun mutumin wucewa a banza ya soki iska, kafin ya ankara da ina ya soka wu ar Abdus-samad ya ri i wuyan hannunshi da mugun arfin da ya saka shi sakin wu ar lokaci aya ya nemi dur ushewa har ya saki wani gunjin ara yace "Ahhj! Hannuna..." Da gudu dogarai sukayo kansu aya dogarin dake bakin ofa tsaye ya rigasu fita da gudu shima ya shigo yana zaro labceciyar wu arshi daga gidanta yana fa in "... *Alhamdulillah.* 26/06/2022 22:54 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _51_ Da gudu shima ya shigo yana zaro labceciyar wu arshi daga gidanta yana fa in "Kai aramin mugu, hattara dai maza bisa kanka." Da sauri Abdus-samad ya aga masa hannu alamar ya dakata tare da urawa mutumin idanu wanda tuni dogaran nan suka mishi wata matsa da hannayenshi suka mur e sosai sun hanashi damar ko da numfasawa yadda yake so, sauran mutanen da basu gama fita bane suka dawo suna kallon ikon Allah ana ta salallami, dogarai hu u ne suka zagaye gabanshida bayanshi da kuma gefenshi dama da hauni aya daga ciki na fa in "Ranka shi da e muje ciki, a barmu da shi zai gane kurensa." Takawa Abdus-samad ya fara yi sai kuma ya sake kallon mutumin, girgiza kai yayi a ranshi yana mamakin yadda ma mutane zasuyi wannan rashin hankalin, to an fa a musu haka kawai mutum ke haye kujerar ya shiga baccin asara? Ko kuma an fa a musu suma kamar su in malamai da bokaye suke bibiya ne? Lallai idan haka suke tunani sun yi kuskure, dan kuwa yau zai nuna musu banbancinshi da su na nesa ne ba kusa ba, yau za'a yi ta ta are a gidan nan ya nunawa kow ya fa san zaman da yake da mutune, ai ba mahaukaci bane shi da zai rasa gane mai kamalta sonsa dan Allah, kamar yadda shi ba makaho bane yana gane dariyar da ta fito daga zuciya aya da kuma wacce ta fito dan a nuna masa kawai an yi. Zai iya cewa ya jima bai yi saurin da yayi a yanzun ba da yake hanyar shigewa fadarsa tun da aka na a masa rawanin nan idan ka cire gudu da yake yi a filin dawakin da ke bayan gidan shi ma ba kullum ba, tunda suka shiga fadar ta hargitse ana ta surutai asa asa kowa na fa in albarkacin bakinshi. Daga waje kuma mutane ne ke ta cika aikinsu ta hanyar bayar da ba'asin abinda ya faru, wasu sun gani kuma suna fa a yadda ya kasance, yayin da wasu ji ne sukayi daga sama su ma suke arawa a kan nasu, dan kuwa wasu har sun fara fa in sarkin nan ashe an bala'i ne kuma an tauri, an soke shi da wu a amma bai ji ba kamar a jikin arfi aka soka. Bai zauna kan kujerar ba yana tsaye su kuma dogarai da sauran mutanen fada kawunansu na asa dan ba zasu mi e tsaye ba idan ba tafiya ne zai yi ba sai dogari aya kawai dake bayanshi da bulala a hannu. Kitir! Kitir da arfi dogaran suka shigo da mutumin nan dake ta son ya waci kanshi ya tsare sai jajaye ido yake yana fa in "Ku sakeni." Basu kula da tsiyarsa ba saida suka dur usar da shi da wata gandareriyar bulala a gabanshi ta hanyar labta masa ita a bayanshi sai da ya zabura, ja baya yayi kas an yana kallon mutumin da shi ma a lokacin ya aga kai ya kalleshi, duk da fuskar Abdus-samad a rufe take amma sai ya ji kwarjini da haibarsa sun cika masa idanu, da sauri ya sadda kai yana ha e hannaye alamar ro o yace "Ranka shi da e kai min rai, ka min afuwa na tuba ba zan ara ba, ka yafe min ranka shi da Da wani kakkausan kallo ya dubeshi zuciyarshi na tunzurashi kan ya wanka masa marin da ba shi ba sake ji na har abada, amma kuma yana tausar kanshi kar yayi abinda bai dace ba tun yanzu a fara kiransa da marar adalci. aga kanshi yayi sama cike da bada umarni yace "Ku bamu waje dukanku." Duk rusunawa suka sake yi sai dogari aya da yace "Allah taimaki sarkina, sarki mai adalci da ha uri, anya kuwa zamu iya barinku kai da shi?" Da yanayin fara hassala yace "Ku tafi na ce." Jikinshi ne ya ara aukan rawa yana ja baya daga zaunen da yake yace "Allah taimaki sarki mai adalci, sarki mai ha uri da yafiya, kai min rai ranka shi da e na tuba, Allah ya huci zuciyarka." Duk ficewa sukayi har da angaladima daya fita a arshe yana waiwayen mutumin da fatan Allah ya rufa masa asiri, saida suka fice gaba ayansu suka rufo ofar sannan ya dubi mutumin da kanshi ke asa sai zufa ke ta tsatsafo masa tamkar zaiyi kwance a zaman tsabar rusuna kai. Sandar dake hannunshi wacce aka ma kwalliya da jan abu tamkar na alkyabbar dake da ratsin ja amma fara ce tas tamkar dakakkiyar shaddarsa, ajeta yayi kan kujerarshi ta zama, a nutse ya fara warware rawanin daya ma mutumin nan shamaki da ganin fuskarshi, saida ya cireshi gaba aya shi ma ya aje tare da hular, a nutse ya tattaro babbar rigarshi ita ma ya cireta ta sama ya aje gefe, a hankali ya taka gaban mutumin yayi tsugunno irin na maza yasa hannu ya tallabo ha arshi da bata da maraba da ta mace tsabar rashin gashin da zai nuna namiji ne. Har ya kalli tsakiyar idanunshi, amma sai ya ji tamkar zai mutu saboda razana da firgicin ganin sarkin a haka wanda ya tabbata ba dan yana son kasheshi ba da har ya mutu ba lallai ya san kamanninsa ba, duk da ya ara sun kuyar da kanshi kuma idanunshi sun i kallonshi, a haka da yanayin kaushi sosai yace "Wa ya turoka?" Gumtse bakinshi yayi ya rintse idanu a asan ranshi yana ta karanta "Hasbunallahu wa ni'imal wakil." Jin shiru bai amsa masa ba yasa ya saki ha arshi yana murza zoben dake hannunshi na azurfa yace "Ba niyyata bane na kashe anan, ka san me tunanina ya ke fa amin a kan ka?" Ba tare da ya bu a idanunshi ba ya girgiza kai yace "Ranka shi da e na tuba." Wani lalataccen murmushi yayi yace "So nake mu daku, mu daku ni da kai ko za ku san ni ba sa'anku bane..." Numfashi ya sauke tare da mi ewa tsaye yana an taku gefe da gefenshi yace "Sihiri gaskiya ne, kuma ya kama masoyin Allah ma fiyayyen halitta bare kuma ni, amma kuyi tunanin zaku cimmin ta wannan fagen... Sttttttta! Stttttta! Stttttta!" Ya dinga ta a harshenshi kafin a zabure ya sake yowa kanshi da kakkausan murya yace "Kai na ke sauraro kafin ka sa na canza tunanina a kan ka." ara rusunawa yayi tamkar zai fashe da kuka yace "Ka gafarceni ranka shi da e, zan fa a maka..." Rumgume hannaye yayi ya sake zuba mishi idanu alamar yana saurarenshi, cikin rawar baki da tsananin tsoron wannan bala'i daya baibayeshi gaba da baya, to fa wannan shine *gaba kura baya sayaki*, a rikice ya bu a bakinshi da yar yace" * angaladima* ne da kuma *shamaki*." Sam bai yi wani mamaki da jin haka ba, dan shi ya jima da sanin angaladima ba sonshi yake ba, shamakin ma ne dai ya an ji mamaki dan bai yi tsammanin haka daga gareshi ba, ta e baki yayi yace" Nawa suka biyaka?" A ladabce yana rera kuka yace" Yalla ai ba su bani komai ba, sun dai yi min al awarin ku i ne masu