Sashe 110
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_______________ Yadda duk suka zama awaye yasa Nafissa fitowa cikin ha iyar atamfarta da ta sha inki a hannun Saleema wacce anko ce sukayi duka awayen Khairat din har da Fareeda, kallo aya Agaishat ta mata tare da aukewa, sai dai da sauri ta sake maido dubanta gareta, a wula ance tace mata "Ke zo nan." an waigawa Nafissa tayi ta kalli Mu'awwaz dake ri e da hannun yaronsu sai kuma ta tafi amsa kiran, bin bayanta yayi suka tsaya a gabanta, kayan jikinta ta sake arewa kallo sannan tace "Wannan ba ita ce ankon Khairat ba?" A ladabce tace "E Mama, ita ce." Kallon Mu'awwaz tayi da ya tsareta da idanu yana jira ya ji me za ta ce, cikin hushi tace "Ka ce min aramar atamfa ce jaka takwas ka siyo mata?" "E, hakane." Ya fa a yana gyara tsayuwarsa, da yanayin acin rai tace " arya kake, wannan atamfar ko makaho ya gani ya san babba ce, gashi nan kuma an mata babban inki." Da sauri Nafissa ta marairaice tace "Wallahi Mama jaka takwas ne turmi aya, ki tambayi kowa ma ki ji zasu fa a miki, kuma inkin nan ni kyauta ma Saleema ta min, kuma shima shaida ne..." Ta fa a tana juyowa ta kalleshi tace "Ko?" Cike da tabbatarwa yace "E, bata amshi komai ba, ni na je na amso kayan ma jiya." Girgiza kai tayi tana ta e baki ita dai sam bata yarda ba, irin inkin nan ne lafiyayye mai shigewa a jikin abunda aka inka, inki ne mai duwatsun nan manya da suke mayar da abu babba sai ka ga tamkar mai tsadar gaske ne saboda duwatsun manya ne, da hannu ta mata alamar ta tafi kawai tare da ora afarta kan aya tana sake aikawa drebansu kira dan ya zo ya kaita wajen bikin, kawai ba ta son tafiya tare da Nafissae ne da ta ce Mu'awwaz in ya kaita. *Gidan Biki* Wani sahihin murmushi ta sake saki ta aga kanta sama cike da kuri da hura hanci ta fara jijjiga afarta, Agaishat ma dake sake duban Ardiyar ha e fuska tayi ta kawar da kanta a ranta tana ayyana "Na tabbata tijara kika wa Yusuf kafin ya iya siya miki shaddar nan, idan kuma ke kika siya to nasan tanadin aikinki ne na gaba aya rayuwarki." Hajia Rabi dake mamakin yadda Ardiya ke ta wani afafa ita ta sako kayan da babu mai irinsu a wurin hatta da Iklima ma, ita kayan data saka ba sune a gabanta ba kamar kwalliyar da ta ca awa fuskarta kamar wata aramar yarinya, Iklima ma daga an nesa take kallonta tana yatsina fuska, a ganinta me ya sa Ardiya za ta auki wannan shirin a bikin kishiyarta? Gashi irin wankan da ta auka da kayan jikinta ka rantse da Allah ita ce matar gwamnan ba su ba, dan ko uwar bikin sai ta yi. aya daga cikin matan da suka zagayeta ne ta sake buga tagumi tana kallon Ardiyar tace "Gaskiya Hajia ba arya wankanki ya wanku, kuma fa shaddar naga kamar babbar ce ko?" Wani yatsina fuska Ardiya tayi tace "Kama ce ma kika gani? A ganinki zan saka aramar ne?" Murmushi tayi tace "Ba haka nake nufi ba, gaskiya Hajia kin kashe masu gidan rana a wurin nan, irin wannan wula anci da kika koro ai ko matar gwamnan ta baki waje." Wani murmushi tayi na jin da i tare da an kawar da dubanta wajen Iklima a sanyaye tace "Anfanin nema kenan, da baka da abun yi ne sai a ce ka mallake miji." Sai kuma ta gyara zamanta tana ha e fuska tace "Ko da yake, ko aikinmu bai siya mana ba ai muna da surukai da aka sansu a gar..." Tsaf! Ta ha iye maganarta sakamakon ido hu u da sukayi da Safiya da ta shigo falon dake cike da hamsha en mata suna ta raharsu, tabbas saida gabanta ya fa i ganin Safiya a wurin dan ita dai ta san ta barota gida ta ce bata jin da in jikinta, hakan ya ara mata arfin gwiwar tahowa da kayan nan tayi birgimarta yadda ta so. Ba wai ganin Safiyar ka ai ba sai ya zamana sanye take da leshen nen wanda Saleema ta musu iri aya, matsalar ita ce ranar sallah shi ta saka kuma ta ora kanta a statu, dayawa awayenta sun dinga ta in leshen saboda kyawunshi da inkin da ya samu ga kuma tsadarsa, a yadda ta ce musu shine mahaifiyar Kabil ta ba sautu ta kawo mata shi daga Dubai. Tuni ta gyara zamanta tana sadda kanta asa kamar mai son oye kanta daga ganin Safiyar, ita kuma bata damu ba sai ma arasawa da tayi suka dinga gaisawa da wa anda ta sani kafin t kawo inda suke ta kalli Ardiyar tace "Kin ganni na zo ko? Gidan ne ya min shiru ba kowa kuma na ji dama dama shiyasa kawai na taho." Murmushin ya e tayi tace "Ohooo! Ai dake nima ban jima da zuwa ba na ce musu ba kya jin da Murmushi kawai Safiya tayi ta karasa wajen Hajia Rabi suna gaisawa. Ardiya ba ta tsure ba sai da ta ga mata biyu sun shigo a tare da sauri sauri suna kula da hanyar shigowar tare da kirarin da ya tabbatar mata Saleema ce za ta shigo falon. Duk tsarguwa tayi tare da tunanin asirinta ya tonu kawai, dan a ganinta Saleema za ta nuna ai ita ta mata wannan inki da kuma siya mata kayan ma, sai dai me? Saleema tabbas ta ga kayan jikinta kuma ta san wanda ta basu tare da mahaifiyarta ne, amma kamar yadda ta gansu ga mahaifiyarta farin ciki tayi da kuma godewa Allah da ta kai matsayin da ta fara taimakawa iyayenta tun suna da ransu, haka yanzun ma da ta ga Ardiya ta ji wannan abun a ranta bayan ta gaiseshu hadiman nan na gaba tana baya tare da jakadiyarta a bayanta suka shige akin mai jegon, da mamaki Ardiya ta bi bayanta da kallo yadda ba ta ko yi alamar ta gane kayan ba. Haka abubuwa ke ci gaba da tafiya har lokacin da ta fara shirye shiryen sake shiga wata gasar, sai dai dalilin rashin lafiyar gimbiya Ramlat yasa ta dakatar da komai dan sosai ta yi jinya har saida aka fita da ita, daga arshe ba ta samu damar shiga wannan gasa ba a wannan shekara ba, hakan yasa shekara biyu kenan tana rasawa. *Yau* ma suna wayar gari Allah ya ma gimbiya Kubra rasuwa wacce jikin nata dama ba wani lafiya yake ba tun waccen faduwar da tayi, haka suka gama jimaminsu kwana uku kafin kowa ya koma rayuwarshi kamar da. Yanzu ma ta gama shirinta na komai dan tun waccen shekarar da bata samu ta shiga ba ta arasa duk abinda za ta yi ta aje, dan haka wannan lokacin arasawa ne tayi kawai tana jiran lokaci ya cika, amma sai laulayi ya sakota gaba wanda ya sa dolenta ma ta aje dan har ranar ta zo bata san ta zo ba sai Abdus-samad ne idan yana son tsokanarta yake tuna mata. *Wata shida* Ihun daya kara e gidan ne yasa Alhaji Yusuf da Safiya dake zaune falon suka tashi a tsorace suna waigawa akin Hamdeeya da suka jiyo abun, da gudu suka nufi akin suna rige-rige, dake ofar akin a bu e suka sameta turus suka ja suka tsaya suna kallon Ardiya da tayi zaman an bori akan tiles in idanunta kakkafe akan Hamdeeya. Waro idanu sukayi da matu ar firgici suka sake kallon Hadeeyar dake kwance kan gado tamkar gawa ga kuma jinin daya wanke tsakanin cinyoyinta har kan gadon yayi jagab da jini. Da mugun gudu ya arasa ga Hamdeeya data jima da somewa ba ta san inda kanta ya ke ba ya jijjigata yana kiran "Hamdeeya, ke! Ke Baby! Babyna..." A gigice ya juyo ya kalli Safiya data matsa kisanshi tana duban Hamdeeyar da yanayin firgici yace " auko min makullin mota mu kaita asibiti." "To." Ta fa a da sauri ta fita a akin da gudu, ta dauko suka ci karo ya auko Hamdeeya har farar rigarshi ta ace, hankali tashe ta kalleshi tace "Ita ma na ga kamar ta some?" Da gudu gudu ya fita da Hamdeeyar yana fa in " aukota in za ki iya?" Zaro idanu tayi sai kuma ta bi bayanshi da gudu ita ma, saida ta ga fitarsu sannan ta dawo akin ta samu Ardiya kamar yadda ya fa a, a haujace Ardiya ta kalleta bayan ta mi e tsaye tace "Ina take? Ina Hamdeeya? Me ya samu ata???" arashe fa a da arfi, nuna mata ofa tayi tace "Ya tafi ya kaita asibiti, ki kwantar da hankali ya ce mu sameshi a can..." Da sauri ta bi bayan Ardiya data fita da gudu, ta manta bata da mayafi, sam bai ma zo gabanta a lokacin, haka ta fita Safiya na kiranta ita kanta bata samu damar aiwatar da komai ba sai mai aiki ta barwa sa on ta kula da gidan suna dawowa ita ma ta bi bayan Ardiya da gyalen mai aiki da ta kar a dan ta bata ta yafa ko ya ya ne. Asibitin ku i da suka tabbatar can zai je suka nufa, da isarsu wata malamar asibitin ta nuna musu saman matakalar suka haye inda aka kwantar da Hamdeeya, suna shiga suka sameshi tsaye sai kai da kawowa yake, suna ha a idanu a tare suka jefawa junansu tambayoyi mabambamta, shi yana tambayarta "Wai me ya sameta ne?" Ita kuma tana tambayar "Ina take? Me aka ce yake damunta?" Ba wanda ya amsa ma kowa tambayar sai fitowar likita daga akin da yanayi na hanzari yana tsaresu da idanu, Alhaji Yusuf ya kalla sosai a an ki ime kuma murya a tausashe yace "Alhaji, muna bu atar jini da za'a ara mata, domin ta zubar da jini dayawa, komai zai iya faruwa idan ba'a saka mata jinin nan da gaggawa ba." A rikice Ardiya tace "Me ya samu ata likita? Me ya sameta haka da take bu atar jini? Mutuwa za ta yi kenan?" Kallonta yayi a nutse ya girgiza mata kai yace "A'a, muna dai bu atar jinin."