← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 116

Sashe 69

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

murya haka? Me na yi da ya zama laifi a nan? To ka zo ka yi inkinka na fasa." Juyawa tayi za ta fita ya mi e tsaye yace "Ke zo nan? Wa ye zai arasa miki aikin?" Saida ta nunashi sannan tace "Kai mana malam alhudahuda." Murgu a baki tayi za ta sake ficewa a raunane yace "Saleemahhhhh." Sake juyowa tayi tace "Daina kiran sunana haka, kayar min da gaba kake malam." Ficewa tayi a shagon ta etara titi ta shige gidansu, dama kuma haka ke faruwa duk sanda sukayi fa a gidansu take zuwa ta ba Fareeda labari ita kuma tayi ta dariya. Yanzu ma da take fa a har Mamansu dariya take tana girgiza kai, harkokin gabansu suka shiga ita da Fareeda har sukayi sallah azahar, suna cin abinci ya shigo gidan, tabbas saboda ita ya shigo, amma da ya ora idanunshi a kan fuskarta suna ta dariya ita da Fareeda sai ya rasa me zai yi kawai ya nufi inda Fareeda ke kiyon awakinta har sun hayayyafa, ya an jima tsaye ya koma ya fita. Mamanshi na lura da shi ita dai ba ta ce komai ba, jim ka an ya sake shigowa kai tsaye wajen Mamansu ya nufa ya dur usa, kayan da Saleema ta yanka ya mi o mata yana satar kallon Saleema yace "Mama kinga yankan da yarinyar can tayi? Ai yayi kyau ko?" Dubawa Maman ta fara yi tace "In dai ita ce ta yanka ai ba sai na ata yawuna ba, ata * ar baiwa ce*." Murmushi yayi yace "Kuma kinga ma daidai da awon Sa'adatu in ne." Saleema da ta fahimci ya zo su shirya ne kallon Maman tayi tace "Mama ki fa a masa ya daina min tsawa a gaban mazan shago, sai yayi ta min bala'i kamar ina cizonshi." Tintserewa sukayi da dariya shi kuma a agauce kamar su ul da baka yace "Ita ma Mama ki fa a mata ta daina yi wa kowa magana a shagon, sannan ta daina aga hijabinta idan tana aiki." Zaro idanu Maman ta yi ta kalleshi da kyau sai kuma ta kalli Saleema ta saki murmushi, Saleema kuma cike da wauta da yarinta na mace tace "To ai zahi ke damuna, kuma fa Mama idan ya kunna fankar sai ya juyata gabanshi shi ka ai, to haka Manzon Allah ya ce ne? Ya ce fa ka so wa an uwanka abinda kake so wa kanka." ewa yayi tsaye yace "To na ji zan dinga juya miki, amma idan kika ara aga hijabinki Allah sai na hana kowane gardi shiga shagon nan, ke kanki in kikayi wasa sai na zane jikinki da tsumagiya." Da mamaki ta kalleshi baki wangale sai kuma ta ma ale kafa a tace "Abinda ma na kusa daina zuwa, tunda ai na iya ko Mama?" arashe da kallon Mama, da sauri ya matsa kusanta kamar zai sunkyya sai kuma ya tsaya yana mata wani kallo kamar zaiyi kuka yace "Ba yanzu ba Saleema, har yanzu akwai yankan da ban koya miki ba, kinga ta so mu je muyi aikinmu." Jinjina kai tayi ta cire hannunta, da sauri Fareeda dake ta kallonsu cike da sha'awa tace "Abincin fa? Ki gama ci tukuna." Girgiza mata kai tayi tana saka takalminta tace "mNa oshi, tunda ya zo muka shirya ma na daina jin yunwar." Dariya yayi ya wuce gaba ta bi bayanshi dan dama fanfon na soro, a nan ta wanke hannunta inda Mamansu ta bisu da kallo a ranta tana ayyana "Allah ya tabbatar mana idan alkairi ne tarrayarku, yarinya ce mai hankali da shiga rai." Suna komawa shagon tsaye dukansu sukayi ya an nuna mata inda za ta gyara sannan ya koma ya zauna, tana gama yankan ta mi a mishi ita kuma ta auki yadin hijabin da ta siyo saboda wani yanka da take son koya na hijabi, tunda ta fara yankawa ya fara yala dariya yace mata "Ba fa haka nan ake yin shi ba, ki bari a koya miki mana?" Girgiza masa kai tayi tace "Ka daina min dariya, ka min fatan nasara kawai." Jinjina kai yayi yace "shikenan ai." Saida ta gama yankawa ta hau telar da Mubarak ya tashi ta game abunta, tsaye tayi tana duba hijabin sai ta ga baiyi yadda ta ganshi jiya a jikin wata ba, tsaki tayi ta cillashi kan wata kujera dake sha e da kaya tace "Bai yi ba wallahi." Ba tare da ya kalleta ba yace "Na fa amiki ai, amma dake ba kya ji baki ji ba." Cike da tabbaci tace "Gobe ma zan siyo na sake gwadawa." Kallonta yayi yace "Asarar ku i? Dan ba naki bane ko?" Turo baki tayi tace "Ai na Mamata ne." Jinjina kai yayi bai ce komai ba, hanyar fita ta kama tana fa in "Malam sai anjima, zanyi sallah na wuce gida." Da kallo ya bita har ta fita a shagon kamar ya ri e, dan wannan lokaci da yanayi shi ya fi komai yi masa da i a rayuwarsa ta yanzu, saidai bai da ikon hanata tafiya gidansu tunda ba *mallakinshi* ba ce. *Alhamdulillah.* 14/06/2022 12:41 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _38_ Ko da ta zo gida ta riski farin cikin da ya mantar da ita komai, ashe duk shirye shiryen nan mahaifinsu kujerar makka ya biya musu, kuma bai fa a musu ba sai yau da zasu aga zuwa babban birnin Niamey saboda tafiyarsu gobe da asuba, dama kuma bai fa a musu bane saboda tafiyar hali ce, ba lallai ta yiwu ba saboda yanayi, dan haka suka shiga shiri ba wanda ta samu damar fa awa ko da ta waya, haka ta kwana cike da zumu in asuba ta yi su tafi tare da mahaifinsu da an uwanta. Sai dai wajen Ardiya kwanan ba in ciki tayi, saboda ta ji banda Hadeeya sai ta tambaya me ye dalili? Ko tana gidan mijinta ai zai iya biya mata, shine fa yake gaya mata ai tuni ya tuntu i mijin Hadeeya ya kuma shaida masa ciki ne da ita, da lokacin yana arami ne za'a iya zuwa da ita, amma yanzu cikinta ya shiga wata kusan na bakwai, rasa abinda ke mata da i tayi, ta yi ta tunanin ta ya ma Hadeeya za ta mata haka? Shiyasa kenan lokacin bikin Safiya ta zo da wata uwar riga ta shadda har asa, Hameeda tayi tayi ta cire ta sha iska ta nuna a'a ta barta haka, Hadeeya ciki har wata bakwai amma ba ta sani ba? Kenan ita mahaukaciya ce? Ta tambayi kanta. Tana ji tana gani asuba na yi Hameeda da Hamdeeya da Saleema suka kama hanya cike da musu fatan sa'a da zuwa lafiya a dawo lafiya. Sai a hanyarsu ta tafiya ne Saleema ta samu ta sanar ma da Huzeifa, cike da murna ya mata fatan nasara tare da mata al awarin yi mata addu'a har ta je ta dawo. ______________ Bakin rantsatsen gyalenta ta kama ta share hawayen dake mata kwaranya ta sake duban Yayan na ta cikin muryar jimami da alhini tace "Yaya ka kirashi ya dawo, wata ila kai ya ji maganarka, har an fara jin amshin shekara amma har yau ce min yake zai dawo, na gaji da wannan halin na shi, ga fargaban rashin sanin me yake damunshi da kuma tunanin me yake aikatawa a can." A nutse dattijon da ba laifi an girma sosai saidai ilimin addini da kuma bin dokikin Islama yasa jikinshi tamkar na wani ingarman doki ga fuskarshi da ke cike da haiba, hannu yasa ya an ja jelar farin rawanin dake kanshi ya mayar baya sannan ya sake zuba mata fararen idanunshi da suka fito tass a cikin babban farin gilashin na ara gani, cike da dattako yace "Ramlat, a kullum ina fa a miki ki kwantar da hankalinki, sannan ki daina zubar da hawaye a kanshi, ranar da kika kirani a waya munyi magana dashi sosai kuma ta fahimta." Gyaran murya yayi wanda manyanci ya kawo hakan sannan yace "Abinda ke damun mai sunan Baba ba aramar matsala bace da zamu fa a mata kai tsaye ba, na nazarci lamarin sannan na yi duba da zahirin daya bayyana a gareni." Shiru ya sake yi na wasu da u kafin ya ora da "Ramlat, Babanmu ya kusa aure da izinin Allah, duk wani sihiri da sammu dake kanshi ya kusa rugujewa, sai dai wani akwai abu..." Da sauri ta kalleshi tana ara gyara zamanta tace "Me ye Yaya? Yaushe? Da gaske ya kusa aure shima?" Jinjina mata kai yayi yana lumshe idanu kafin ya kalleta yace "Ban san yaushe ne ba, saidai Allah ya nuna min shima zai yi aure kafin ya bar duniya, kinsan wani mafarkin ilhama ce ta faruwar wani abun, dayawa daga abubuwan dake faruwa damu ana nuna mana su a mafarki, saidai rashin sanin fassararsa yasa muke kasa sanin me ke shirin faruwa da mu?" Da sigar aguwa da damuwa tace" Amma Yaya baka ka ce baka san ranar ba? Kenan har yanzu ba lokaci?" A tausashe yayi murmushi ya gyara zaman babbar rigarsa yace" To me yasa zamuyi hanzari? Kin san me na gani kuwa Ramlat?" Hannu ya mi a mata yace" Matso nan anwata, zo ki ji." Mi o masa hannunta tayi ta matsa kusa da shi tana kallonshi tare da ci gaba da share hawayenta, cike da son kwantar mata da hankali yace" A mafarkina na ga Abdus-samad hannayensa biyu ri e da wata farar kwalba, bayan an lokaci sai wannan kwalbar ta bu e da kanta kawai ruwa suka dinga fitowa, ruwan na gama zubewa sai fuskarshi ta fa a saboda murmushi, yayin da tsabar hasken annurin fuskarshi ya isa ya haska gidan nan da kewayenshi... Shin kin san me hakan yake nufi?" A hankali ta girgiza masa kai tace" Ban sani ba Yaya." Cike da sanin ilimin abun yace" Kwalbar na nufin matar da zai aura, ri on da ya ma kwalbar kuma alamu dake nuni yadda zai ri e matar da zai aura da kyautatawa kuma hannu bibbiyu, ruwan cikinta na nufin za ta haihu
Chapter 69 · 0% Book details