← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 116

Sashe 27

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ma." A nutse tace "Yawwa, Khairat dan Allah ki min wata alfarma, ki samu malam ki fa a masa na amince yanzu a saka sunana a jerin masu saukar." Da mamaki Khairat tace "Amma me yasa? Na ga da fari ke kika ce ba kya so saboda Abbanki, yanzu kuma kin ce a saka, Abban ya amince ne?" A tausashe tace "Ko aya Khairat, yanzu ma zan yi ne ba tare da saninshi ba, sai dai ban damu da ko me zai faru ba, ban ci jarabawar ba bai kamata na bari wannan damar ma ta wuce ni ba." Khairat ce ta amsa da "Gaskiya kuma hakane, to amma ta ya zakiyi sauka bai sani ba?" Kamar za ta fashe da kuka tace "Khairat ke dai ki fa awa malam, in dai har ya amince za'ayi dani, to zan samu ku i a hannun Mama ko da na iya wainar da za'ayi sadaka ne." "To shikenan." Cewar Khairat tana ci gaba da fa in "Bari na fa a masa dama yanzu ya shigo gida zai ci abinci." "Yawwa nagode, yanda kukayi ki kirani da wannan lambar, amma anjima da yamma za mu koma gida." Da haka suka rabu ita da Khairat, bai fi minti 15 ba ta sake kiranta da lambar malam in dan ita wayarta ba ku i ta sanar mata ai ya amince kuma ya yi farin ciki sosai, wannan magana ita ta saka Saleeema farin ciki marar misaltuwa tana jin ko ba komai dai za ta kafa tarihi a zuri'arsu cewa ita ce ta farko da za ta sauke Al ur'ani kuma a haddace. Dreban da ke ta jiransu Alhaji Auwal ya kalla ya musu nuni da shi yace "Ku je yarana, Allah muku albarka." Sai kuma ya kalli Saleema yace "Amma dai za ki dinga kawo mana ziyara ko?" aga kai tayi alamar e, da yatsa ya nunata yace "Da gaske?" Da murmushi ta amsa da "Allah ko Abba." Jinjina kai yayi yace "Shikenan to na yarda." Juyawa Saleema tayi ga Hajia Rabi tace "Mama sai anjima." Shafa kuncinta tayi tana fara'a tace "Allah ya miki albarka ata, ki gaishe da Mamanki." Jinjina kai tayi alamar to, Papi dake gefe Saleema ta arasa gareshi, ri o hannayenshi tayi duka biyun tana kallon fuskarshi tace "Papi nagode sosai da goyon bayan da ka bani, mu zamu tafi, sai wani lokaci kuma." Jaye hannunshi aya yayi ya ora a kanta yace "Allah ya miki albarka, Allah ya baki miji na gari, Allah ya saka farin ciki a rayuwarki, Allah ya baki zuri'a ta gari wacce za ta zama sanyin idaniyarki." ora hannunta tayi kan na shi tana murmushi tace "Ameen Papi, nagode sosai, kai ma Allah ya ara maka lafiya da nisan kwana." Ummeeta dake tsaye kusan Hameeda da kallon yama take binsu har saida suka shiga mota suna ta aga musu hannu suka bar gidan, duk da Saleema na jin za ta yi kewar mutanen, amma dai ta fi farin ciki da komawarta gidansu dan shine kwanciyar hankalinta. *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:41 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _18_ Tunda suka shigo gidan sai suka ga kamar sun yi watanni ba sa nan, cike da kewar iyayensu duk suka zube falo, daga iyayen har su kansu yaran sun girgiza ganin irin tarin tsarabar da aka saka musu bayan mota wacce sai yanzu da dreba ya yi ta shigowa da su suka gani, wani kwali na daban dreba ya mi awa Saleema yace "Wannan Alhaji ne ya ce na baki." a tayi tace "Ka min godiya sosai." Duk tarin kayan dake gabansu wanda komai aka saka daidai da na kowa, hatta da takalmi dake wurin kowa da lambar da afarshi ke auka, dan Saleema talatin da takwas take anfani da shi, Hadeeya kuma arba'in daidai aramar lamba, sai Hameeda talatin da tara, amma Hadeeya da ta wallafa rai tana son sanin me je cikin kwalin, saida ta matso kusan Saleema tace "Mu ga miye a ciki?" Ba tare da tunanin komai ba Saleema ta mi a mata wanda saida Safiya ta kalli Saleema da mamaki, dan ita ta san abin da ba'a ba kowa ba ne aka ba arta. Hadeeya na bu ewa jikinsu har rawa yake ita da Hameeda wajen ciro kayan ciki, wata mahaukaciyar lafiyayyar abaya kalar pink Hameeda ta bu e tare da yin tsaye tana gwada rigar a jikinta, Hadeeya kuma wasu takalmi dake ciki kalar rigar ta auka tana gwada a afarta wanda takalmin da ganinsu ta san masu tsada ne kuma sabin kalar da ba kowa ya sansu ba. Hameeda dake tsaye da rigar a hannu ce ta hango kwalin da ya saka gabanta fa uwa, da sauri ta saki rigar ta dur usa ta auki kwalin tana bu ewa, Hadeeya ma da ta gani zaro idanu tayi ta furta "IPhone 14 pro max." Ardiya ma zaburowa tayi tana walalo ido dan jin wai da gaske suke ko dai wasa? Uban wa zai ba Saleema wayar da ta haura million aya? Ta na ganin camera in wayar ya tabbatar mata da gaskiya, Hadeeya ri e wayar ta yi gam tana ta dubawa tana jin ina ma ta zama ta ta, take ta kalli Saleema tace "Bari na tura miki abubuwa, ba komai a ciki." Saleema ko a jikinta, yo ita me zata yi da waya? Mi ewa ma kawai ta yi ta barsu nan ta shige akin Mamanta dan yin wanka, Hadeeya da Hameeda ai sai suka shiga ture-ture da aukar hoto suna turawa a wayoyinsu suna nuna fa da IPhone 14 aka auki hoton, wayar da har yanzu su dai duk yanda suke tare da an masu ku i kuma ma aryata ba su ga wanda ya yi jarumtar ri eta ba bare su da har yanzu Abbansu ne ke siya musu idan suka birgeshi. *Suna* zaune kan sallaya Saleema ta kalli Mamanta tace "Mama, kwana hu u ya rage saukar makaranta, kuma na ro i malam ya saka sunana, yanzu ku i nake so a wajenki da zan inka sabon hijabi irin na sauran alibai, sai ka inda hali ki min waina da za'a yi sadaka." Ajiyar zuciya Safiya ta sauke tace "Me yasa kikayi haka? Kina so mahaifinki ya wula ancemu ne?" Turo baki tayi da alamar shagwa a tace "Dan Allah fa Mama, kinga wannan ce ka ai damar da nake da da Abba zaiyi alfahari dani, baki ga ba azu gidansu Yaya Mu'az yanda yake hararata." a ido Safiya tayi tace "To, Yaya Mu'az kuma? Yaushe ya zama Yayan na ki?" Cike da kunya ta sunkuyar da kanta amma ba tace komai, jin shiru yasa Safiya nisawa tace "Shikenan, amma yanzu dai kinga bana da ku i gaskiya, kuma ko da za'ayi saukar nan sai dai mu ja baki muyi shiru kar kowa ya ji, dan bana son fitina a halin da na ke cikin nan." Marairaicewa Saleema tayi tace "To amma Mama ina zan samu ku in?" A tsanake ta kalleta tace "Karki damu, bari Abban na ki ya shigo, zan san yanda zan yi na samo miki." Fara'a tayi tace "Nagode Mama." ewa tayi ta bu a wata aramar drower ta auki chocolate a cikin tsarabar da aka basu ne, da kallo Safiya ta bita har ta fita a akin, murmushi ta saki tana fatan Allah ya kareta a duk inda take, har yanzu wayar nan tana hannunsu Hadeeya, amma ita ba ta damu ba, sannan tsarabar ma na sauran kayan Ardiya ce ta raba ta aiko Hamdeeya ta kawo wai na Saleema, kayan ba su taka kara sun karya ba, ta san za suyi tunanin ai ita an bata wannan babbar kyauta, amma abun mamaki Saleema kar a ta yi sam alamu ma ya nuna hankalinta ba nan yake ba bare ta yi orafin wannan an abun za'a bata? Tabbas halin ko in kula na abin da ya shafi ci ko na duniya mai arewa halinta ne, sai dai ar ta ta tafi ta halin ko in kula akan abun, dan ita tana gane an cuceta sai dai kawai ta yi shiru, amma ita Saleema sai dai ka ga alamar bata san abun a kai ba bare ya dameta, gale da kyautar da mahaifinsu ke ba an uwan ita ya hanata ka ai take an damuwa, shi ma da an kwana biyu ta shiga sabgar gabanta. Suna zaune kan teburin cin abincin ya fito cikin farar jallabiya, zaunawa yayi inda ya saba zama kullum, Saleema dake kusa da shi ta sadda kanta saboda kallon da ya mata, mi ewa Safiya tayi a kasalance ta fara zuba masa abincin, shi kuma hakalinshi na ga Saleema yace "Na fa a miki idan har ba ki samu jarabawar nan ba dama zan auki mataki na arshe a kanki." A hankali ta aga idanunta ta kalleshi a ladabce tace "Ka yi ha uri Abba, a gaba zan yi in s..." Tsawa ya daka mata da cewa "Ke! Ni sa'an wasanki ne?" Da sauri ta sadda kanta asa saboda alamar da Safiya ta mata da idonta, cike da masifa yace "To bari ki ji Saleema, idan ma aure kike so ki fito da miji na aurar da ke, amma ki sani na daina asarar ku ina a kanki, wallahi na daina zuba miki wandala da sunan karatu, dan haka ba ke ba sake fita a gidan nan da sunan za ki tafi makaranta, *na dakatar da ita daga yau*." Duk zuba mishi idanu sukayi har Safiya dake tsaye, sai kuma ta girgiza kai tana lumshe idanunta, Saleema ma idanunta cike da hawaye ta kalleshi sai kuma ta kalli mahaifiyarta da tunda ta zo ta fahimci kamar har yanzu jikinta ba ta jin da inshi, abin da take son fa a masa tsoro kuma ya hanata dan kar ya bigeta, sai kwatsam mahaifiyarta ta yi tambayar cewa "Amma Alhaji ka hanata zuwa islamiyya shekara takwas da suka wuce, ka hanata inki tun tana arama, yanzu kuma ka dakatar da bokon ma, toe za ta yi idan ta zauna a gidan?" Kallonta yayi a zafafe yace "Wannan hukuncina ne kuma na gama yankewa,
Chapter 27 · 0% Book details