← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 116

Sashe 24

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ji a jikinta kawai ba ta samu ba, amma dai za ta je dan ta samu tabbacin haka. *Washe gari* Ta jima wajen Papi suna hira tana fa a masa wani abu da ya zo kanta daren jiya kafin bacci ya auketa, ganin ta samu goyon baya ari bisa ari sannan ta fito daga angaren na shi ta nufo falon dan aukar jakarta ta tafi makaranta dubo sunanta. Kai tsaye madafa ta nufa ta samu Nafissa da amarya suna aiki, an kama musu tayi saboda Nafissa take so ta ma magana, tana ganin Amarya ta bu a mangaza ta ra awa Nafissa abu a kunne, kallonta tayi da mamaki tace "Kin tabbatar?" Lumshe ido tayi alamar e tace "Ki yarda dani, ki warara kanki." A tsorace ta furta "Gaskiya ina jin tsoro." Girgiza mata kai tayi ta ri e hannubta tace "Ki ji tsoron Allah kawai, yana tare da mu kuma zai taimakemu, saboda niyyarmu mai kyau ce." Jin amarya na fitowa yasa Saleema raba hannunta da na Nafissa tace "Yawwa ni na tafi, sai na dawo." Jinjina kai tayi tace "A dawo lafiya." Da harara amarya ta bita tana ayyana "Allah raka taki gona, na san ma ba samu zakiyi ba tunda ba karatun ne a gabanki ba." Amarya na idar da girki ta kira Ummee, tana zuwa ta bata abincin Papi ta ce "Ki kaiwa Baba akinshi." Wani yatsina fuska tayi tace "Papi kuma? Ba ga Nafissa nan ba." Rai ace amarya tace "Ke in za ki kar a ki kar a, doka ce kuma ubanki ya orata, in ba za ki kai ba na kira Mu'az ya kai sai na fa a masa ke kin Da sauri ta finciko kwanon ta juya kamar za ta cira bakinta tana bubbuga afafu ta nufi akin cike da takaicin me ye sai ita za ta kai masa abinci, tana shiga akin ba sallama dan ta nuna bata so ba fa, ajewa kawai ta yi ba ko ina kwana duk da yana zaune falon haka ta juyo ta fito, da kallo ya bita kawai ya girgiza kai a ranshi yace "Allah ya shiryaku." Tare da dreba suka tafi makarantarsu, a kam ta samu alibai da dama da suma suka zo duba na su sunan, ba ta ;ata lokaci ba wajen fara duba sunayen da suka fara da harafin H, shiru babu alamar na ta sunan, haka ta dinga dubawa daga farko har arshe amma babu, jiki a sanyaye ta koma gefe ofar wani aji ta zauna ta tangale kanta da ginshi in wurin, sannu sannu ta ji idanunta sun fara kawo mata ruwa, kamar an daketa sai kawai ta fashe da kuka. Cikin an ajinsu ne wata ta dafa kafa arta tace "Saleema." agowa tayi saboda ita ka ai ta san me take ji, ganin haka yasa ta sake fa in "Saleema, ki yi ha uri idan ba ki samu ba, kinga ni ma ban samu ba kuma ban damu ba, saboda na san akwai gaba kuma haka Allah ya tsara, kinga dayawa ma basu samu ba amma kowa ya ha ura, wannan shekarar jarabawa ta zubar da alibai dayawa, ki warara kanki in sha Allah wata shekara sai ki ga kin samu." A hankali ta rage kukanta jin ba ita ka ai ba ce akwai dayawa, share hawayenta tayi ta mi e tsaye ta kalli budurwar tace" Nagode Chafa'atu, nagode sosai, Allah ya sa haka shi ya fi zama alkairi." "Ameen." Ta fa a tana murmushi, da sauri Saleema ta nufi hanyar fita ta samu dreba na jiranta ta shiga suka tafi, haka kawai ta ji zuciyarta ta bushe da tunanin hukuncin da mahaifinta zai mata, a ganinta idan ma duka ne ai ba yau ne farko ba, ya jima yana dukanta tun bata san ciwon jikinta ba, dan haka za ta auka idan ma dukan ne, ai dai ba zai auki ranta ba idan ba Allah ya nufi hakan ba, kyauta kuma ya ba wa su Hadeeya duk abin da ya mallaka bai dameta ba, in dai bai hukunta mahaifiyarta da laifinta ba to komai ya yi. Cikin takon nutsuwa ta shigo falon, a hankali ta shiga bin kowa na akin da kallo saboda yanda ta ga sunyi zugum-zugum, babban abin da ya aga hankalinta shine ganin mahaifinta a gefen Alhaji Auwal zaune fuskarshi yanda kasan hadarin gabas, sai dai kuma a gefe da ta ga Nafissa dur ushe tana kuka ashirban sai ta an murmusa kamar hankalinta a kwance yake. Duk da arnan kallon da mahaifinta ke aika mata bai hanata arasawa kusa da shi ba ta zauna asa irin zaman tahiya tace "Abba ina kwana." auke kanshi yayi daga kanta da mamakin ita yarinyar nan ba ta gane acin rai ne? Kusanshi fa ta zo bayan ta san zai iya tattakata, Alhaji Auwal ne ya dawo da shi daga tunanin da yake ta hanyar fa in " ata ya batun sakamakon?" Kallonshi tayi sai kuma ta sunkuyar da kai a hankali ta girgiza kanta alamar ba magana, da sauri ya kalli Alhaji Yusuf da zai yi magana a zafafe ya masa alama da ido ya yi shiru, ha ewa ya yi yana jinjina kai kamar zai tashi sama, a tsanake ya kalleta yace " ata, kar ki damu kanki kin ji, fa a min ya kike so? Kina son samun kanki a aji na gaba ne? Ko kuma kina so nan da awa aya ki ga sunanki a kafe a wata takardar?" Kallonshi tayi tace "A'a Abba, nagode da karramawarka, amma na fi so na samu dalilin arina, idan akayi haka an zalunci dayawa wanda ba su da yanda zasuyi." "Kuma har abada ba za ki samu ba indai da arinki ne." Cewar Alhaji Yusuf har da saka afa aya ya tureta daga kusanshi, sai da tayi kamar za ta yi sujada dan abun bazata ne, gyara zamanta tayi sanda Alhaji Auwal ke fa in "Ka ga kar ka kuma dukar min yarinya, karatun ba na Allah ba ne? Ko dabararta za ta bata ne?" Cije le asa Alhaji Yusuf ya yi kamar zai ciji iska, Alhaji Auwal kuma kallon Nafissa ya yi da ke ta sharar hawaye yace "Zan nemeki, ki bamu wuri yanzu." ewa ta yi ta nufi madafa, kallon Hajia Rabi da amarya yayi yace "Dan Allah ku bamu wuri za mu tattauna?" A kasalance suka mi e musamman amarya da ta bi Saleema da harara, har yaran ma duka ya korasu sannan ya kalli Alhaji Yusuf yace "Bari na nuna maka wani abu game da arka." Kallon Saleema ya yi a tsanake yace "Matso nan Baby." ewa tayi ta koma kusa da shi ta zauna asa, a nutse ya kalleta yace "Saleema, wannan yarinyar Nafissa ta zo min da wata magana yanzu, amma ban yarda da ita ba saboda na san ana..." Gyara zamanshi ya yi yace "Ta fa a min wai Yayanta ne ya ke so ya kashe min ana Mu'awwaz saboda ya gano akwai wata mummunar ala a tsakaninshi da ita Nafissa, kuma ta tabbatar da zai aikata saboda Yayan na ta an daba ne, shi ne ta tsorata take sanar dani wai na yi wani abu a kai, da fari ma in fa a ta yi sai da na yi da gaske ta fa a min dalili, to magana ta gaskiya na an ta a ganin abin da ya sani zargin Mu'awwaz, sai dai ba na jin zai iya neman ar aikin gidan nan, to yanzu ke ya kike gani? Na tura Mu'awwaz wata asar ne? Ko kuma na sanar da hukuma su shiga tsakaninsu." Da sauri Saleema da dama komai shirinta ne ta kalleshi tace" A'a Abba, kar ka yi ko aya." Da alamar tambaya ya tambayeta da" Me yasa?" A nutse cike da hankali tace" Abba, ta min bayani akan Yayan nan na ta, an shaye-shaye ne da babu abin da yake sai zaman banza, ba ya da tunanin kansa bare ya yi tunanin rayuwar wasu na shi, a ganina idan ka shigar da maganar wajen hukuma, to kamar mun da awa kanmu wu a ne, dan shakka babu za'a san abin da Mu'awwaz ya aikata, idan kuma ka fitar da Mu'awwaz asar waje, to fa wannan an daban zai iya fallasashi da tunanin ya gudu ne saboda tsoron kar ya auki fansa, idan kuma har maganar ta fito fili, to hukumar kare ha in mata da yara anana za su iya saka ido a kan lamarin, idan haka ta faru kuma za'a ce a gudanar da bincike, a arshe kotu za ta shiga lamarin da orafin Mu'awwaz na aya daga cikin ma su cin zarafin mata musamman marasa galihu." A sanyaye sosai kamar za ta yi kuka tace" Abba, kuma ka san hukumar kare ha in mata ba ta wasa da lamari irin wannan, za su ata lokaci da ku i har ma da iko wajen ganin sun kayar da mu wannan shari'ar, gwamnati ma ba ta ja da su Abba, dan su suna da goyon baya daga turawa ne." arashe maganar da sigar dake nuna tana son tsoratar da shi, ai kam a tsorace Alhaji Auwal yace" Hakan na nufin mutumcin gidan nan zai zube kenan?" Cikin ra a kamar za ta yi dariya tace" Abba, ai har siyasarka ta shekaru ma lalacewa za ta yi, abokan hamayya sun samu abun tsokanarku da shi, gaskiya a duba wata hanyar." e ha a Alhaji Auwal ya yi ya kalli Alhaji Yusuf da ya kafe Saleema da idanu da mamakin ina duk ta san wannan abubuwan? Wa ya bata wannan hikimar? Cike da jimami yace" Ya ka ke gani Alhaji Yusuf?" auke idanu yayi daga Saleema yana an matse fuska yace" Gaskiya ne Alhaji, a duba wata hanyar daban." Jinjina kai ya yi yace" To kenan ya kake gani?" Kallon Saleema ya yi yace" Ke shiga ciki." Jinjina kai tayi ta fara yun arawa a kasalance za ta bar wurin, inda shi kuma ya kalli Alhaji Auwal yace" Ina ganin a kira yaron sai a bashi ku i ma su yawa da zai sa ya bar maganar kawai, kuma ma yarinyar ai ba fya e ya mata ba, da son ranta haka ya faru tunda ba karan-kanta ta zo ta fa a ba." Da sauri Alhaji Auwal ya
Chapter 24 · 0% Book details