Sashe 23
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
musu da ita, saida ta ga ya fara jefa abincin ka ai ta bar akin tana sake jadadda masa za ta zo aukar kwanon da kanta, maza ya cin ye duka kafin ta dawo. arar da wayarshi ta yi yasa ko amsa mata baiyi ba ya du a wayar, wani iska ya feso daga bakinshi ganin Sharhasila ce, urawa lambar idanu yayi da tunanin ya auka? Dan tun da ya fara zana jarabawar nan bai kirata ba saboda zafi da kanshi ya yi, yau ne ya gama yake tunanin zai je gidan dan su ha u saboda ara aratowar lokacin bikinsu, gashi kuma ta kira bai san dalili ba. auka ya yi ya kara a kunne yana sallama, a ta aice ta amsa wa "Alaika salam, Baby shine ka manta da ni ko kirana ba ka yi?" Lumshe idanu yayi kamar ba zai amsa ba, sai kuma ya numfasa cikin nutsuwa yace "Ban manta da ke ba, zan zo gidan yau." Cike da shagwa a da kuma sakarci tace "Ka ga ni zan zo, zan zo gidan na ku, ina son ganinka ne." Waro idanu yayi a sau e yace "Gidanmu kuma?" Turo baki tayi ta amsa da "E, gidanku, na yi kewarka Baby." Dafe gaban goshonshi yayi yace "Ba sai kin zo ba, ni zan zo anjima, kin ji?" Cikin shagwa a tace "Ka yi al awari?" "Na yi." Ya fa a a tausashe, murmushi tayi wanda saida ya ji sautinsa a kunnuwa tace "To Baby ka taho mana da ice cream, ni zan ba ka wani abu idan ka zo." Rufe idanu yayi yana mamakin wauta irin ta Sharhasila, "To." Kawai ya fa a yana auke wayar daga kunnenshi ya aje ya ci gaba da cin abincin. *Ga mai son shiga grp ina ya tuntu i wanda ke musu post zai samu kanshi a ciki in sha Allah.* *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:41 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _16_ Fitowarta kenan daga wanka tana tsane jikinta da babban towel, su Hadeeya ta samu suna ta mitar aikin da sukayi na gyaran akin Papi wanda har kayan abinci sai da Alhaji Auwal ya sa aka canza musu wuri aka maidasu madafa, Ummee haushi kamar zai kasheta da tana aikin, yanzu haka duk a gajiye suka kwanta har arfe 11:00 ta yi. Kayan baccinta ta saka ta zauna bakin gado tana addu'o'in da ta saba yi, ta shafe jikinta kenan za ta kwanta aka wasa akin, mi ewa tayi da niyyar bu ewa dan Hameeda tsaki ta ja tana fa in "Daren ma ba za'a bari mu huta ba." Ta kai hannu za ta auki hijabinta aka turo ofar, ido hu u sukayi da Mu'az da yayi turus yana kallonta daga asa har sama, bakinshi bu e ya kasa furta ko a, hankali ya lalubi idanunshi ya rufe dan in ba haka ba zai mutu a tsaye. Sa'a aya ta yi saurin rarumo hijabi ta rufe jikinta ba tare da ta sanya ba, sosai kunya ta kamata ta sadda kanta asa, riga da wando ne jikinta na bacci, rigar ta na da hannaye iya damatsenta, saidai ta fito mata da surarta, haka ma wandon duk da bai kamata ba, amma tsayinshi iya bakin gwiwoyinta ne. Hadeeya da ta mi e zaune ce tace "Yaya, lafiya?" a idanunshi ya yi ya kalleta sai kuma ya yi gyaran murya yace "Ughym! Umm..ammm...! Dama jarabawarku ne ta fito, na zo na ji lambobinku ne dan na duba muku." Da sauri Hadeeya ta taso tana fa in "Yawwa, Yaya ni lambata 4452..." Saida ya saci kallon Saleema da ta wanka masa harara ta ja tsaki ta koma ta zauna kan gadon kafin ya turawa abokin na shi lambar da sunan Hadeeya ya duba masa, cikin anin lokaci aka fa a masa Hadeeya da Ummee sun samu har ma da Hameeda da ita ta zana jarabawar ne kawai amma ba ta kai ga ajin ba (candidate libre), cikin anin lokaci akin ya hargitse da ihu da shewa na an matan, da gudu suka fita dan sanar da iyayen da har yanzu suke zaune a falo suna kallo suna hira. A hankali ya tako ya zo gabanta cikin sanyin murya kamar mai tsoronta yace "Saleema, lambarki?" A zafafe tace "Ba na bu ata malam, ka ga shigo mana aki da ka yi ma ba tare da an baka izini ba ya isa, dan haka kar ka hassalani dayawa." Kawar da kai tayi tana sake ha e fuska sosai ita dole ya ata mata rai, dur usawa ya yi niyyar yi dan ci gaba da bata ha uri, haka kawai ya ke jin ranshi ba da i saboda ranta ya ace, da sauri ta jaye afafunta dake kusa da shi tana an galla masa harara, mi ewa yayi tsaye yace "Ki yi ha uri Saleema, na shigo ne dan na ga baku jima da shigowa akin ba bare a ce har kun kwanta, amma ai na wasa ofa, kuma sai da na an jinkirta kafin na shigo, tunanina hakan ya ba wa wacce ke farke damar kimtsa jikinta." Sake marairaicewa ya yi yace" Saleema, ni fa ba kowace mace ke birgeni ba, ba kuma kowane tsiraici na ke son gani ba, tunda na ke a rayuwata ban ta a jin ina son wata a mace ba sai ke, ke ce mace ta farko da na ji ina so na yi rayuwar aure da ita, ke ce macen da na ji ina sha'awar ta zama uwar ana, Saleema..." Yanda ya kira sunanta yasa ta aga kai ta kalleshi, ci gaba ya yi da cewa" Tabbas arya na fa a idan har na ce surarki ba ta birgeni, amma ki sani na yi tarayya da mata da suka fi ki kyau da wayewa, sai dai ba su min ba saboda sun rasa *aji*, a gareki ne na fahimci duk wata mace mai aji, to tana tare da *kamun kanta*, wallahi abu aya ya sa na ke sonki da aure, wannan abun kuma shine *tarbiyya*, ina da ya inin tarayyata da ke za ta zama tsanin hawana hanya madaidaiciya, kamar yanda na ke da tabbacin zuri'ata indai ta tsatsonki za su fito, to za su zama abun alfaharin kowa, sannan na zama uba ma fi dacen a a duniya." Da sauri ya dur usa gabanta yayi tsugunno irin na maza yana kallon fuskarta kamar yadda ita ma take kallonshi da yar take yaftawa yace" Saleema, ki nemi za in ubangijinki a kan lamarina, kar kiyi gaggawa dan ni ma ba zan yi ba, duk da kuwa ina matu ar son yin aure saboda wani babban dalili, idan har kika ji kin gamsu za ki aureni, to ki sanar da ni a ko da yaushe, ni kuma na miki al awarin fa a miki komai a game da ni, har da ma wanda iyayena kansu ba su sani ba, dan bana so mu fara zama na gaskiha ba tare da kin san wannan abun ba, dan gaskiya ba na jurar matsala daga abun da na ke so, musaman ma..." Saida ya yi asa da kanshi kafin yace" Musamman ma ke, wallahi zan iya miki kuka idan kina hushi dani." Da sauri ya ago ya kalleta yace" Kin gane? Ni kwata-kwata ban saba da rayuwar wahala ba, ban ta a jin abu ya birgeni lokaci aya ba kamar yadda kika shiga raina, an reneni cikin gata da bani duk abin da na ke so, dan Allah Saleema kar ki hana min kanki a karon farko na rayuwata." a ido tayi da kyau tana kallonshi, an jan hijabinta tayi ta ara rufe afafunta da take jin ta kamar a tsirara, ba tare da ta auke dubanta gareshi ba tace" *Aku*, aku sarkin surutu." ace mata hanci yayi yana dariya yace" Ke ma da kin aureni za ki koyi surutu." Da sauri ya mi e tsaye yana sake fa in" Yanzu bani lambar ta ki kema na sa a duba miki?" Girgiza kai tayi tace" Gaskiya a'a, ina ji a jikina ma ban ci ba, ba sai ka wahalar da kanka ba." Da mamaki yace" Me yasa? Ya za ki cire rai haka?" Cike da jimami tace" Ka share kawai, nagode da kulawarka." aga kafa a ya yi yace" Shikenan, bari na canza kaya sai na je na dubo miki." Da mugun sauri ta mi e tsaye har tana sakin hijabin ya zube asa ta yi ram da rigarshi tana fa in" A'a, a'a dan Allah kar k..." Sai kuma ta saki rigarshi ta ja baya tana dur usawa ta auki hijabin kanta asa cike da kunyar abun da ta aikata, ganin ta yi shiru babu ma alamar za ta ce ala sai kawai ya fita shima ya na ji a ranshi lallai lallai dole ya dinga nisantar yarinyar nan dan gudun samun matsala, dan in dai zai dinga ganinta a haka, sannan har wani dalili ya sa su ha a jikinsu, to fa tabbas komai na iya faruwa a yadda yake tsananin son yin aure dan ya ci halalinsa. Da farin ciki Hameeda ta shigo akin tace "Abba ya ce ki zo." Ba ta amsa mata ba ta mi e bayan Hameeda ta fita a akin, zane ta aura a kan wandon sannan ta saka hijab in ta fito, falon ta samesu suna ta murna inda ta ji Ummeeta na fa in "Gaskiya Abba ni dai aton sa za'a yanka min, awayena su ci nama su oshi." Tana arasowa ya kalleta yace "Saleema ke ba ki fa a mana sakamakonki ba?" A sanyaye tace "Abba da safe zan je da kaina na dubo." Da mamaki yace "A'a, me yasa to? Gashi a sau e Yayanku na diba muku." A ladabce tace "Abba na fi so na duba a can." Kallon Amarya ya yi yace "Ai ina tunanin an Bac ma gobe ake fito musu da sakamako?" Saida ta yatsina fuska ta kalli Saleema tace "Haka ake saka rai." Jinjina kai yayi yace "To shikenan, Allah kaimu goben sai ki je tunda haka kika fi so." Juyawa tayi ta koma aki ta kwanta gaba aya take