Sashe 57
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
jin dadi tace "Hakan ya yi kyau, kuma ina goyon bayansa." Ba wata hira suka yi mai tsayi ba, illa dai daga arshe kafin suyi sallama sarauniya Ramlat ta nemi Saleema da cewa " ata, muna barar addu'arki, kada ki manta da mu a cikin addu'o'inki, Allah ya yaye mana matsalolinmu." Cike da tabbaci Saleema tace" In sha Allah ranki shi da..." Katseta tayi da" A'a, ki kirani da Ummi, nima Umminki ce." Jinjina kai tayi tace" To Ummi, in sha Allah, Allah ya yaye duka damuwa." Da haka sukayi sallama Saleema na mamakin matsalar da matar ta ambata, wace irin matsala kuma? Suna gidan sarautar? Ba rashin ci, ba ta sha, ga mulki da iko a hannu, ga dukiya daidai gwargwado, ga hadimai zagaye da su wanda ko wanka sai ka so ne za ka yi saboda kasancewarka an adam, to me ye zai damesu a rayuwa kuma? (wata aukakar matsala a rayuwa, rayauwar talauci in da godiyr Allah da wadatar zuci da i gareta, Allah ka bamu wadatar zuci da godiya a gareka). *Bayan* sallah magriba Mamanta ta dawo a gajiye, kayan data shigo da su ta jawo tana dubawa, Safiya dake shafawa afafunta mai bayan wankan da tayi ta kalleta tace "Ki ware mana leshen nan daban da safe sai ki kai mana inki." Kallonta Saleema tayi tace" Mama an samu ne?" Cike da gajiya tace" Na sameshi da yar." an mamaki tace" To amma Mama ina zamu inki yanzu? Kayan da zamu saka nan da kwana uku?" Murmushi tayi tace" Ba kwana uku ba, biyu ne, krki damu kanki da wannan, ban zo gidan nan ba saida Lubna ta ha ani da wani mai inkinta, kuma ya tabbatar a kai masa za'a samu." Turo baki tayi tace" Allah yasa kar ya ata mana lokaci, dan ni bana juran acin rai daga ma inka saboda abu ne da ni ma zan iya yi, dama ce kawai ban samu ba." Murmushi kawai Safiya ta sake yi ba ta ce mata komai ba, gu ar amaryar data kara e gidan yasa suka kalli juna Safiya tace" Ki tashi ku tafi, ina ga wanka ne zasu tafi." Girgiza kai tayi tace" Um um Mama, a dawo lafiya." Da sauri Safiya ta arasa shiryawa ta bi bayan masu tafiya ta bar Saleema a gidan, ta riga da ta yi niyya ne ba zata halarci komai na bikin ba tunda ta ji Zeid ne zai auri Hadeeya, ta san dole zata iya ha uwa da Mu'az, ita kuma mantawa take so tayi da shi na har abada, duk da hakan ma na neman gagararta, amma dai za ta koya wa kanta arfi da yaji. aixin da ya yi yawa a akin yasa baccin aukarta a gadon mahaifiyar na ta, Safiya ma na dawowa ta sameta bata tasheta ba, saida ta sake watsa ruwa tayi sallah isha'i da ta samesu a hanya tayi shaf'i da wutiri, tana tsaye gaban madubi tana aure gashinta da aramin ribom ya turo ofar akin ya shigo, ta madubi ta dinga kallonshi har saida ya isa kusanta. Ba tare da tunanin komai ba ya ri ugunta ya kwanta a gadon bayanta ya lumshe idanu, da sauri ta shiga are jikinta tana hangen inda Saleema ke kwance ta madubi, cikin ra a tace "Sakeni mana, idan fa ta tashi ta ganmu?" Cikin sanyayyar murya yace "To sai me, ba mijinki bane ni?" arfi ta wace kanta tana juyowa ta fuskanceshi tace "Ai dai da kunya, ko Hamdeeya ba zan so ta ganmu haka ba bare Saleema data mallaki..." Tsurawa Saleema idanu tayi da ta gyara kwanciyarta, juyawa yayi shima ya kalli Saleema sai kuma ya kalleta yace "Ke fa yarinyar nan har yanzu Baby kike aukarta ko? To da tayi aure ya zakiyi?" A ta aice ta arasa aure gashinta tace "Na yi laifi ne? Ita aya gareni." Hannunta ya kama da niyyar janta su fita yace "Muje akina to." "Me zan maka?" Ta fa a tana kallonshi, janta yayi yana fa in "Muje zaki gani." Binshi kawai tayi dan ta san kwanan zancen, kamar yadda shima yau in yayi niyya idan har bata biyoshi ba to ko zasu yi abun kunya a gaban ar da take auka Baby. *Washe Gari* Duk kai da kawowar da ake gidan bai hanata shieyawarta tsaf ba ta fita dan kai inkinta da na Mamanta na ankon leshen da zasuyi iya su kawai gidan bayan wasu ankon da duk mahaifinsu ya yi wanda Saleema har yau take jin tamkar ta masa kuka, dan kuwa duk wanda aka fito Ardiya tqaye take ta fara amsar ku in na ta dana yaranta, hakan yake sa shi ita ma ya bata da mahaifiyarta dan ba zai iya waresu ba, a alla ita dai ranar da ya basu ku in ankon dana inki da sauran bu atunsu na shigar bikin iya su biyar kawai ban da Hadeeya dake amaryar saida ya zube musu ku i tsabarsu har jaka ari hu u, saida ta masa wallan tausayi ganin hidimar ba ita kenan ba fa. Yanzu haka wannan leshen ita kawai da Mamanta saba'in da biyar ya basu, kai ita dai gaskiya tana tausayawa maza. Kwatancen da Safiya ta ma drebansu tun jiya ya dinga bi har saida Saleema ta fara shinshino anya kuwa ba shagon nan bane zai kaita? Ai kam tana ganin an auki layin ta tabbatar da zatonta, tunda ya faka motar take le en shagon kawai sai take jin kunyar shiga saboda dalilin maganar da sukayi ne ta ce zata koyi inki har Abbanta ya daketa. Saida dreban ya juyo yace "Hajiar Alhaji nan ne fa." Da sauri kamar wacce ya gaurawa mari tace "Uhum." Bu e motar tayi a nutse ta auko kayan ta fito sannan ta rufe ofar, etara titin tayi ta shigo shagon da sallama, ganin babu Alhudahuda yasa ta sauke ajiyar zuciya ta arasa shiga ciki. aya a cikin matasan dake inki shagon ta samu kuma wanda sukayi al awari da Mamanta, dan haka ba ta tsaya komai ba tana mi awa ta biyashi rabin ku inshi ta tafi da tabbaci jibi ta dawo ta kar a, kamaar wacce bata da gaskiya haka ta yi saurin komawa mota, tana shiga ta rufe kenan ta ga tsayawar motonshi zai shiga shagon, kamar dama shine bata son gani sai kawai ta sauke ajiyar zuciya, ba ta dain kallonshi ba har ya shiga shagon su kuma suka bar wurin. *Ranar Kamu* A jigace ta zauna kan kujerar robar tana kallon yadda ta gama tsara wurin zaman amarya da ango, murmushi tayi dan ita kanta tayi mamakin yadda ta iya shirya wurin yayi kyau haka, ba wai ziga kanta take ba, ta tabbatar yayine tunda har Ardiya da ta sakata aikin ta ce yayi kyau sannan ta ce mata sannu da aiki, da baiyi ba tun a fuska za ta gane. Ta gaji sosai, dan lamarin bikin na gidansu mamaki yake bata, shekaran jiya an yi Guitar wanda hakan al'adar Ardiya ne kasancewarta buzuwa, haka aka kwana ana ka a jita mata da maza ana rawa da tsalle tsalle da iface iface (kwate tarhanine, tagmasss ). Jiya kuma partyn auyawa aka yi, haka gidan nan ya hautsine mata suka dinga canza halittarsu da shigarsu suka zama auyawa kata'in, yau kuma ga kamu wanda shine arshe dan gobe za'a aura aure kowa ma ya huta. Hameeda ce ta fito daga angaren Abbansu, ganin wurin yasa ta waro idanu tace "Wow, Saleema wai da gaske ke kikayi?" asan ma oshi ta amsa mata da "Um." Da sauri ta koma inda ta fito tana fa in "Kai ku fito an gyara wurin." Jim ka an dandazon an matan dake ciki suka dinga fitowa, mi ewa Saleema tayi ta shiga falonsu dan ta samu ta shirya, sam bata sakewa a cikin mutane, biki ko na gidansu ne sai ta dinga ari ari da kunya. Tunda ta shiga ciki bata fito ba saida ta yi sallah magriba, lokacin ita da kanta tana jin irin hayaniyar dake tashi ta san mutanen sun gama hallara, lokacin ne ta cire hijabin ta gyara aurin an kwalinta sannan ta saka takalminta ta fito bayan ta rufe akin dan Mamanta na waje. Tana fitowa falo suka ci karo da Ardiya auke da aton cake, da sauri tace "Yawwa Saleema kar i, fitar musu da shi dan Allah." a tayi tana jinjina kai, tana fitowa farfajiyar ta tsaya cak! Tana kallon farfajiyar, mutane ne duk zazzaune sai an mata tsakiyar fili ana ta dabsar rawa, wani banbara wai ta ji kanta da bata sako mayafi ba, sai ta ji ba zata iya shiga filin da kayan jikinta ba, riga da siket in na leshe da suka matu ar amsar jikinta suka fito mata cas a jiki, duk da ba ta kwalliya ba kuma aurin kallabin ma a sau e tayi shi, amma sai tayi kyau ga kuma gyaran da aka fara mata tun lokacin saka ranar aurenta, dake ya kar eta musamman sabulun da har yanzu da shi suke wanka ita da Mamanta, sai take ta yalli ita ma kamar wata amaryar. Juyawa tayi da sauri da niyyar komawa aki ta auko hijabi dan ba gyale gareta ba, sai kuma Ardiya ta fito tare da awayenta, ganinta yasa ta fa in "Saleema baki kai ba har yanzu? Me kike jira?" A raunane tace "Aunty hijabi zan auko." Cike da takaici Ardiya tace "Hijabinme ke kuwa? Bikin anwarki ne fa, wa ya damu da ke a nan bare ya cinyeki." A sa ule ta juya ta tunkari tsakiyar filin hannayenta har rawa suke saboda akwai maza sosai a wurin suna ta shewar ganin an mata, da harara Ardiya ta bita tana fa in "Kidahumar banza." aga a cikin awayenta ne tace "Wai da gaske mijinki ne ya haifeta?" Yatsina baki tayi tace "Wai ba." Tsaki ta ja tare da arasawa su la filin taron suka samu wuri suka zauna. Tunda ta shiga filin idanun ma fi yawan mutane ya koma kanta, musamman da babu wanda zai ce ya ta a ganinta babu hijabi a wurin sai yau, sai abun ya zama sabo a gurin su kansu da ita kanta, insa wanda suka samu damar ganin bayanta kuma suke sauke idanuwansu akan ugunta da ya matu ar basu