Sashe 14
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ita dan bata so ya kawo mata wargi duba da tambayar da za ta mishi ba ta ta a kwatanta yi masa ita ba sannan tace "Ina ka kwana?" Da sauri ya saka idonshi a cikin na ta kamar wanda aka ba wa tsoro, sai kuma ya saka fuskar mamaki yace "Mama, me ya sa kika tambaya? Wani abu ya faru ne?" Sake ha e fuskarta tayi tace "Sai wani abu ya faru zan tambayeka?" an girgiza kai yayi yace "E to Mama, na ga dai haka bai ta a faruwa ba ai." Tsareshi tayi da ido tace "Amsar tambayata?" an matse bakinshi yayi yace "Abinci na fara ci a restaurant, sannan na wuce majalisarmu, ba mu tashi a nan ba sai arfe uku na dare, daga nan mu ka arasa gidansu *Zeid* a can na kwana." Wani sakaran murmushi ta yi tace "Ka kwana ko ka rintsa? Ai ka gama kwananka tun a majalisa." Gyara tsayuwa ta yi tace "Sallah da, ka yi sallah kafin ka shigo?" ance ido yayi yana mata kallo mai kama da hangen nesa yana so ya gano me ke damun Mamanshi yau? Cikin mamaki yace "Na yi sallah Mama." Harara ta galla masa tace "Yanzu ka yi ko?" Sosai eya yayi alamar kunya bai ce komai ba, girgiza kai tayi tace "Allah ya shirya." "Ameen Mamana." Ya fa a yana binta da kallo, ganin za ta yi nisa ya matsa kusanta yace "Mama." Juyowa tayi tana kallonshi amma ba ta ce komai ba, da ar din amsar da za ta bashi yace "Mama wani abu ya faru ne?" Da mamaki tace "Me ka gani?" Sunkuyar da kai ya yi yace "Na ga ai kina ta min wasu tambayoyi ne kamar aramin yaro ko wata mace." Wani kallo ta mi shi tace "Au! Ina matsayin mahaifiyarka ba zan tambayeka ba tunda ka wuce munzalin?" Girgiza kai yayi yace "A'a Mama ba haka nake nufi ba, abun dai ne ya zo min wani iri, baki ta a haka ba fa Mama." Jim! Ta yi ta kalleshi kuma ta san gaskiya ya fa a, gyara tsayuwarta ta sake yi tace "Gaskiya kam, ni ma kuma na san tambayoyin da na maka sabon abu ne, amma dan Allah da na tambayeka ba ka ji da i ba?" Murmushi ya sakar mata tare da dafa duka kafa unta ya ora ha arshi a wuyanta yace "Na ji da i sosai Mamana, hakan ya nuna min yanda ki ka damu da ni." Turo an bakinta tayi gaba cikin shagwa a tace "Zuwan yarinyar nan ya zamar mana alkairi, daga jiya zuwa yau ta haska mana abubuwa da dama da suke shige mana duhu, musamman ma a kan sallah da ta tunatar da mu yanzun, sai na ji kamar zan zauna na yi ta kuka saboda kurakuren da muka tabka a baya, amma in sha Allah na auki niyyar gyarawa da wannan nasihar da ta mana." Hannu ta zura ta bayanta ta shafi kumcinshi a shagwa e sosai tace" Gaskiya yarinyar kirki ce, ina ma za ta zama surukata?" Da mamaki ya aga kanshi ka an yace" Mama, wacece wannan?" Hararan wasa ta jefa mi shi tace" Wa fa ban da Saleema." Wani asaitaccen murmushi ya saki tare da maida ha arshi a kafa arta, haka kawai ya ji wani shau i da da i na sunan da ta ambata, shiru ya yi ya lumshe ido a kafa arta kamar bacck zai auke shi. Tureshi tayi tace" Kai agani, har yanzu ban shiga madafa ba." Takwaf-takwaf ya yi da fuska yace" Mama yunwa fa na ke ji, shiyasa na shigo da wuri." Nuna mishi ofar madafa ta yi tace" Ka shiga madafa ba za ka rasa abun da za ka ci ba." Turo baki ya yi gaba ya nufi hanyar madafar ita ma ta arasa in da za ta je sam ta ma manta da Saleema na madafar. *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:38 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _11_ Yana shiga madafar ya tsaya cak! Ya na are mata kallo daga baya, rumgume hannaye ya yi da tunanin to ita haka take shigarta kullum? Ko kuma dai ba unta ce ta sa haka? Sai kuma wata zuciyar ta raya masa "Idan ba unta ce ai an uwanta ma ba untar suke, me ya hanasu kama jikinsu kamar ita?" "Tarbiyya ce kawai." Wata zuciyar ta bashi amsa, abaya ce jikinta da kallabinta wanda sam jikinta bai bayyana ba, a hankali ya sauke hannayenshi daga irjin ya shiga takawa gareta, bayanta ya tsaya ya an dubi tukunyar da ke kan wuta wacce take soya naman da ta samu a fridge, tsilalar da yake na jajjagen da ke jikin naman kuma aka saka cikin mai me zafi, wannan tsuwar ce ta hanata jin tako daga bayanta saboda tana ta arin kare kanta kar mai ya ki onata. Ba ta ankara ba, ba ta san da faruwar abun ba, hannaye bibbiyu kawai ta ji sun zagaya kumkuminta an kwantar da kai a bayanta cikin wata tattausar murya yace " *Leema* sann..." Tunda ta ji irin ru umewar da aka mata ta sa ma ranta mace ba za ta mata haka ba, ko da ta ji muryar Mu'az tun bai gama maganar ba ta juyo a mugun tsorace kuma a fusace ta auke fuskarshi da mari ta bayan hannunta. Kallon kallo su ka tsaya kowa da irin fitinannen kallon da yake aika wa an uwanshi, ita kam mamaki da acin rai ne suka lullu eta cike da dana-sanin zuwa gidan nan da ta yi wanda sam babu alkairi a ciki sai jafa'i da ta ke gani kala-kala. Shi kuma mamakin arfin halin ta da kuma tsoron da ya ke hangowa a idonta mai auke da acin rai na aljabi yasa shi sakin murmushi, a hnkali ya jaye hannunshi daga kumcinshi ya a ja baya ka an, cikin raha alamar dai abun bai wani ata ransa ba yace "Na samu abinda na ke so, wannan shi ne abinda ya kamata na gani a tare da wacce na ke so sa'ilin da wani wanda bai da hurumi a kan ta ya kai hannunsa jikinta, hakan alamu na cewa za ki iya yankar duk wanda ya yi arin ta a min *halaliyata*." Wasu mugayen hawaye ma su zafin gaske ne suka kwaranyo mata daga kurmin ido na takacin wannan rana da ta risketa, tunda ta balaga ko Mamanta kunya take ji ta rumgumeta bare kuma Abbanta, amma yau ato da ba ta da ha in komai da shi ne ya kwanta a bayanta tamkar wata matarsa. Hannu tasa ta share hawayen ta furta " (Godiya ta tabbata ga Allah wanda saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika)." Da sauri ta yi azamar ra ashi za ta bar wurin duk da kuwa ta na jin naman da take suya ya na neman onewa, da sauri ya tare gabanta har tana neman fa awa kan shi ya yi saurin fa in "Dakata." Da sauri ta kalleshi cikin muryar kuka da kuma unar da ke cin zuciyarta tace "Ka matsa min a hanya, idan ba haka ba wallahi zan maka ihu." Cike da isa ya rumgume hannaye a irji yana murmushi yace "Bismillah, yi, ko ba ihu ba? Yi ihu ki ce kwarto ne ni." Da mugun sauri ta li e kunnuwanta tana fashewa da kuka ta dur ushe asa tana fa in "Dan Allah ka rabu da ni, ka tafi ka bani wuri, wai me yasa ba ku da a'a ne? Ku wasj irin karnuka ne?" Da wani mugun sauri ya finciko hannunta da alamar ya ji zafin kalmar ta arshe, ba tare da ya saki hannunta ba ya ha ata da bango ya matse mata wuri sosai, tsabar tsoron da ya kamata yasa ta du ar da kanta ta gandarawa hannunshi cizo. Amma da ke ranshi ya ace da ta ha ashi da kare sai ya yi kamar bai ji ba, matse hannunta ya sake yi sosai har ta saki ara tana matse fuskarta, Mu'az kam mutum ne mai son raha da barkwwanci, sai dai akwai abun da sam ba ya auka kuma a take ranshi ke acewa. Cikin jin zafi ya kalli fuskarta yace "Wa ye kare? Ni ki ke ha awa da dabbar da ake ajiyewa dan tsaro kawai?" Wani kukan ta sake sakawa mai ban tausayi tana neman sulalewa asa a asan ma oshi ta furta "Hannuna." Da sauri ya kalli hannunta da ya matse, a hankali ya sassauta mata ri o yana jin tausayinta na mamaye zuciyarshi, saida ya saki hannunta gaba- aya sannan ya sunkuyar da kai yace "Ki yi ha uri, kuma nagode da marina da ki ka yi." Juyawa ya yi har zai fita sai kuma ya tsaya, a hankali ya tako ya dawo gabanta ya tsaya duk da ta rufe fuska tana kuka, cikin tattausan murya mai kashe jiki yace " *Ina son ki*." Da sauri ya juya ya fita a madafar ya ma manta me ya shigo da shi da fari, tana jin ya fita da sauri ta arasa gaban gas in ta kashe wutar, tana kwashe naman ta na sako da hawaye har ta kammala abinda ta fara sannan ta barsu a nan ta fita a madafar, tana haurawa sama tana tunanin tafiyarta gida ne, ba zata iya zama a gidan nan ba ko ka an, ba ta sani ba ko mahaifinsu ya san haka gidan yake ya turosu? Amma dai ba ta zauna ba ita kam, dan in suka zauna daga ita har annenta cikunna ne za su bayyana garesu nan da kwana ka an, dan ita tsoronta kar shi ma uban haka ya ke ya fara are musu kallo. Tana shiga akinsu da kuka ta share hawayenta ta nufi inda jakarta take da kayanta da basu wuce guda uku ba bayan na bacci, Hadeeya na kwance da waya a hannunta, Hameeda ma kwance take suna kallon hotuna a waya ita da Ummee, da kallo duk suka bita sanda ta auki jakar tana tattara kaya tana zubawa ciki, saida ta gama tsaf ta auki zunbulelen hijabinta ta saka, ta auki jakar