Sashe 40
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kayan dake ciki, sannan ya an fesa *chairman black* sama sama saboda ya an fi arfi. Yana mur ofar akin fadawan da jiran fitowarshi suke duk suka dur usa aka kwashi kirari, takun nutsuwa da asaitarsa yasa duk suka sadda kawunansu saida ya yi gaba sannan suka mi e, wasu ne suka shiga gaba suna kula da duk wanda zai taho daga gaba, inda uku ke baya suna take masa baya ana masa firfita da wani sakaran mafici da ana yi ne kawai dan isa. Suna fita a falon nan ma wasu dandazon masu jiran fitowarsa ne, nan take masu busa dake gefe su uku suka shiga busa wacce ke nuni da sarki mai mara wa ne ke tafe, da wannan takon na alfarma wanda kowa dake bin bayanshi da gabanshi haka suka dinga tafiyar har suka isa fadar inda aka tanadi wajen zamanshi dan na i kamar yadda suka bu ata. Manyan ba in da suka halarci wurin masu matsayi da iko na fa a-aji duk suna zazzaune a kujerun da aka tanada musu, inda wurin ya cika da mabiya kala kala kowane da na shi shugaban da yake bin umarninshi, busar sarewa kuma har yanzu tana tashi, ga kuma kirari da zigar da kowane san- ira ke yi wa wani babban dan samun abinda zai saka bakinshi. an jarida na gefe asan carpet in da aka shinfi a kowane hannunshi ri e da abinda zai auki rahoto da shi, lokaci kawai suke jira a basu dama su fara gabatar da abinda ya tarasu a wurin. Tunda ya yi haramar zama kan kujerar suka rufeshi da manyan rigunansu suna ta gyara kimtsi tare da shaidawa kowa kanshi asa, sun yi ka an su ga zaman sarki, a nutse ya zauna kan kujerar tare da rufe idanunshi ruf saboda jin kamar ana caccakarshi da tsini wu a da allura daga asa, wani irin masifaffen zafi ne jikinshi ya auka lokaci aya fiye da na mai zazza i da ake yayyafawa ruwa, take hankalinshi ya gushe, nutsuwarshi ta gudu ta barshi, ya gigice ya ki ime lokaci aya. Sanda kowa ya gama zaunawa duk an zuba mishi idanu sai wanda zai yi na in, kamar da wasa sai gani sukayi mi e tsaye cirrr! Kamar wanda ya ha iyi ta arya yana zazzare idanu daga cikin gilashin, waziri da sauran fadawa ne suka tashi tsaye suna kallonshi da tambayar lafiya a nutse? A rikice ya kalli limamin fadar tasu cikin muryarshi da ta nuna tashin hankalin da yake ciki yace "Liman, *an aura auren ne*?" Da mamaki Liman ya kalleshi cike da tausasawa y dubi agogon hannunshi yace "Ranka shi da e a yanda muka tsara tafiyar da komai, ina ga nan da minti biyar za'a aur..." Bai dire kalmar da kyau ba mai gadon kamar yanda dayawa ke kiranshi yace "A dakatar da shi, a dakatar yanzun nan." Yanzu kam kowa da mamaki a fuskarshi ya kalleshi saboda aura auren ne fa zai bashi damar zama sarkin d zai mulki al'umma, to idan ya ce a fasa bayan haka aka tsara, me yake nufi kenan? A gigice Liman ya kalleshi yace" Amma ranka sh..." Bai jira fa ar kowa ko masu take mishi baya ba kawai ya shiga takawa da mugun saurin da tunda Allah ya halicceshi bai ta a sanin yana da shi ba sai yau, irin yanda zuciyarshi ke bugawa ga wani zafi da take masa tare da ga an jikinshi, yanayi ne da yawancin lokuta ya ke shiga idan aka masa maganar aure, to gashi yanzu har kujerar da mahaifinsa ma ya bari tana neman gagararshi hawa. *Tunda* ya ficedaga fadar ya bishi da kallo daga cikin ba in gilashin dake idanunshi, rawanin daya rufe mishi baki ya hana ganin murmushin da yayi a zuciyarshi ya ayyana " *Ba sai ka yi auren ba sannan za ka zama sarki*? To ka yi mu gani, in dai ina raye haka ba zata faru ba *Abdus-Samad*." Galidimomi har ma da waziri da liman duk suna bi bayanshi, dan tashin hankalin d zasu shiga idan aka fasa auren nan Allah ka ai ya san shi, dole ne ma a hura musu wuta daga sama dan su tsayar da wanda zai hau kujerar nan, amma idan ba haka ba lokaci yayi da zaman kujerar babu sarki zai zo arshe. Falon mahaifiyarshi da ya shiga kai tsaye yasa duk suka ja birki, dan duk haukansu basu da damar shiga wurinta kai tsaye haka. Duk saurin da yake sai gashi labarin ya rigashi isowa wajen mahaifiyar tashi, saboda tazarar dake tsakanin fadar da kuma falon na ta, da ya bi ta sassau ar hanya da ya iso da wuri, sai dai hankalinshi baya jikinshi da yar ya kawo kanshi nan, shigowarshi tasa hadimai biyun dake tare da ita suka rusuna sosai suna gaisheshi, baida abi'ar wula anta na asa da shi, sai dai har ga Allah idan ya ji gaisuwar nan to tabbas wanda ya mutu ma yana jin kira, da sauri suka fice a akin suka barshi daga shi sai ita. Sarauniya da hannayenta biyu ke tallabe da kyakyawar farar tasar da take dama mishi fura a duk lokacin da baya azumi kasancewarshi mai irin azumin *Annabi Dawud*, yau ya ci abinci gobe ya sha ruwa, tunda ta ji labarin ta dakatar da komai ta shiga imuwar da ta kasa kwatantawa. Har ya zube gwiwoyinshi asa kusa da afafunta ya rirri afafun, idanu kawai ta zuba mishi tana kallonshi kamar bata gane shi ba, kallon fuskarta yayi da idanunshi da sukayi jajir alamar bala'in da yake ciki shi ka ai yasan shi yace "Ummiiiii! *Ummina ki lamunce min na bar asar nan*?" ara walalo idanunta tayi waje, sai kuma ta zabura da sauri ta aje tasar furar gefenta wacce ita ka ai ke dama masa ita a duk duniyar nan, hannayenshi ta agoshi yayi irin zaman nan daya tokare yatsunshi na afafu duka asa. Hawaye ne suka fara biyar kumatunta cike da dattijantaka tace "Babana, me yake faruwa ne? Me ya faru? Me ya sa ka ce a dakatar da aurin auren? Yarinyar ce bata maka ba da ka ga hotonta? Ko kuma ahalinta ne basu maka ba?" Girgiza kai yayi da sauri da alamar ro o yace "Ko aya Ummi, ni dai dan Allah ki min rai ki amince na bar asar nan, Ummi zafi nake ji ta ko ina, idan na ci gaba da zama a nan mutuwa zan yiiii." arashe da kwantar da kanshi kan cinyoyinta, dafa kafa arshi tayi a sanyaye tace "Babana me yake damunka? Ka fa a min mana, ni fa mahaifiyarka ce, yanzu fa sau uku kenan sai za'a aura maka aure sai ka ce ka fasa, shin an matan ne ke zuwa maka da wani abu da bai maka na? Ko kuma kai ne kake jin wani abu a game dasu?" A hankali ya ara girgiza mata kai, burinshi a yanzun bai wuce kawai ya ga ya bar asar nan ba da yake jin ta masa unci, shafa bayanshi ta fara yi ta sake cewa" *Auren ne ba ka so*?" A hankali ya aga kanshi ya kalleta, hannaye biyu yasa ya cire rawanin da gaba aya hular da ke kanshi, cike da tausayin kanshi yace" Ummi ina so, ina so na yi aure nima, na samu wacce zan kira da *iyalina*, idan ina cikin damuwa na fa a mata ta rarrasheni, idan ina farin ciki na sanar mata muyi tare, Ummi ina so na haifi an da zasu kirani da Abi, su kira *matata* da Ummi, sannan su kiraki Maami, amma..." Sai kuma ya ara wara idanunshi a kan fuskarta ya ri o hannayenta yace" Ummi ki ce na tafi, Ummi ba zan iya awa aya a garin nan ba, na ro eki Ummi ki ceci rayuwata." Jin kamar zai fashe mata da kuka yasa ta lumshe idanu a sanyaye ta furta" Ka sha furar sannan." Marairaicewa yayi kamar zai yi kuka ya girgiza mata kai, tsurawa juna idanu sukayi tana kallonshi da tausayi tace" Babana, kai a ranka me kake ji game da mace? Ranka yana acewa ne idan ka ga mata?" A firgice ya kalleta da tsoro da kuma mamakin furucinta, da sauri ya girgiza mata kai yace" A'a Ummi, Ummi ba wai ina in mata bane, hasalima dan kare kaina daga fa awa halaka na za i yin azumi duk kwana aya, Ummi ni ka ai na san me nake ji, dan Allah ki barni na tafi." Kukan da take ri ewa ne ya taho mata, hakan yasa ta fa a jikinshi tana kuka, bayanta ya shiga shafawa shi ma kamar zai yi kukan sai dai dakakkiyar zuciya ta hana, jin ana ara ingizashi ya bar asar yasa shi saurin jayeta daga jikinshi ya mi e, kallonta kawai yayi yace "Ummi na tafi, ki min addu'a a duk inda na ke." Juyawa yayi a sukwane zai bar falon, da arfi tace "Babana..." Sai dai bai tsaya ba dan ba yin kanshi bane, barin masarautar nan ne ka ai mudi'inshi a lokacin, dan haka kai tsaye akinshi ya koma ya ha a abinda zai ha a kawai ya fito dreba ya jashi zuwa filin jirgi. *Yana* fita anenshi da shi ma na in ne ya dawo dashi daga makarantar Say dake babban birni Niamey yana karatu kan shari'ar addini ya shigo, ganin mahaifiyarsu na kuka ya dinga rarrashinta, cikin kuka tace "Akwai abinda ke faruwa sa shi, tabbas akwai abinda Babana yake oye min." Ajiyar zuciya yarima *Abdul Karim* ya sauke yana ci gaba da shafa bayanta yace "Hakane Ummi, nima na fahimci haka, mu masa addu'a kawai." Shigowar sarauniyoyi biyu yasa suka kimtsa kansu dan kar a fahimci damuwarsu, musamman da sarauniya Ramlat ta fahimci kamar shiga gaban anta aka yi, zazzaune sukayi kowace da hadimarta kafin su basu wuri, cike da jimami uwar gidan tsaka da amarya suka jajanta mata kan abinda ya faru, amma sam ta i fa a musu ai ya ma bar garin yanzu haka, kawai tana so ta san me ke faruwa da anta kafin kowa ya farga. *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:49 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar