← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 116

Sashe 92

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace "Na aika maka abun sha? Amma ai ni ban aika maka komai ba?" Matse bakinshi yayi yace "Sanyayyar madarar da kika turo min dan ji a ma oshina mana." A mugun firgice ta sauko daga kan gadon tana dafe irjinta da fa in "A'a yalla ai, kar ka sha, bani na aika ba wallahi, kar ka sha koma menene." Tsai yayi da dubansa kan ofar shigowa yace "Ban gane ba? Lafiya?" A rikice ta sake dafe kai tace "Yalla ai wallahi Allah bani na tura maka ba, hasalima ban san a inda kake ba, idan da ni ce zan fara sanar maka tun kafin ka fita, kaga Abdul..." Ta fa a har haki take kafin tace "Idan kana son wani abu ne yanzu ka fa a min zan sarrafa na turo maka, amma dai wannan kar ka sha bamu san wa ya aika ba." Ajiyar zuciya ya sauke mai arfi yace "Shikenan, na ji, kwantar da hankalinki, ba zan sha ba." Ita ma arfar ajiyar zuciya ta sauke ta koma ta zauna a hankali kamar za ta fashe da kuka, kamar saukan ruwan sama muryarshi a yanayin ra a ya furta " *Kina sona ne*?" Tsit! Wurin ya auka sai saukar numfashinsu, tamkar yana gabanta haka ta sadda kanta tana jin kunya sosai, sai kuma tayi saurin cewa "Nima ban sani ba, ka kula da kanka dan Allah." Tana gama fa it! Ta yanke kiran, auke wayar yayi a kunne ya bi wayar da kallo yana murmushi, sai kuma ya aje kofin hannunshi yana tunanin wa ya turo masa da abun sha da sunan *matarsa*? Son ganin bayan nasa har ya kai haka? To ko daga yanzu ba zai ci daga hannun kowa ba idan ba ita ko Mamanshi suka bashi hannu da hannu ba. ______________ Ganin sak amakon yasa shi aga kai ya kalleta ya nuno mata sakamakon yace "Hamdeeya, yanzu wannan ne sakamakon na ki? Ina arinki da na sanki da shi ne? Kinga zauna..." Ya fa a yana nuna mata kusa da shi, zaunawa tayi tana turo baki tana kauda kanta, duk da kuwa Hamdeeya tana shekara sha aya ne yanzu, amma ba ta san girmama mahaifi ba, cikin nutswa Alhaji Yusuf ya fara fa in" Kina ji ko, kinga yanzu ke ka ai kika rage a gabana mace, sauran an uwanki babu wacce har yanzu take ta tsarawa rayuwarta abu mai kyau, dama dama ma Yayarku Saleema tana auren babban mutum mai matsayi, amma kinga Hadeeya ciki kawai take yi tana haihuwa, Hameeda ce ma da ta fara gyaran takardunta tana son fara aiki a ma'aikatar tura ku e, to kinga ke a gaskiya ina so sai kin fara aiki kafin kiyi aure, amma kuma sai ki fara zuwa da wannan sakamakon? Ta uku fa kika zo? Ba kya ganewa ne a makarantar? Ko kuma dai wasa kike da kula awayen banza?" Cike da rashin girmamawa ta turo baki tace" Ni fa ina ganewa Abba, kawai dai darasin malamin lissafi ne ke wahalar dani." Murmushi yayi ya shafa kanta yace" To dan wannan ai ba abun tashin hankali bane, kina so na samo miki wanda zai dinga koyar da ke har gida ne?" aga kai tayi tace" E, amma bana son mai duka da fa Dariya yayi yace" Wa ma zai dakeki har gidan nan? Shikenan zan samo miki." ewa tayi ta nufi akinta tana fa in" Saleema ba gabanmu ka ke sa ana zaneta ba idan bata gane karatunta ba." Da kallo ya bita kafin ya girgiza kai yana sake kallon sakamakon na ta, a ganinshi tana aukar na uku yaushe za ta zama abunda yake burin ta zama, gwara ta fara zuwa ta aya tamkar Hadeeya da hakane ai za ta cika mishi burinshi. Aje sakamakon yayi ya mi e da niyyar shiga na shi akin, ofar falon aka banka o da yanayin tashin hankali tare da sautin kuka, dakatawa yayi yana kallon ofar, da sauri ya shiga takawa ya tarbeta da tashin hankali tyana fa in "Subhanallah, Hadeeya! Lafiya? Me ya sameki haka?" Ya fa a yana kallon fuskarta da ta lalace tsabar bugun da tasha, zubewa tayi kan gwiwoyinta tana sake fashewa da kuka tace "Amma kasheni zaiyi, Abba Zeid ne zia kasheni wallahi, ni dai Abba na gaji kawai ka ce ya sakeni." Ardiya ce ta fito hannunta ri e da waya tana dannawa, amma ganin Hadeeya da halin da take ciki yasa ta saurin sakin wayar ba tare da ta sani ba ta nufosu tana fa in" Hadeeya, lafiya? Me ya sameki?" Kamata tayi tana son tayar da ita tsaye Safiya ta fito ita ma daga akin ri e da hannun Ahmad, ita ma da kulawa ta araso tana tambayarta, Alhaji Yusuf ne ya sake kallonta yace" Ke wai me ya faru?" Cikin kuka Hadeeya ta tsaya da yar kan afafunta tana fa in" Abba Zeid ne, daga na tafi wajen bikin Yayarshi da ta haihu, shine ina dawowa gida na sameshi da mace a akina, dan na mata dukan tsiya shine ya rama ma... " A tsawace Ardiya tace" Ke..." Tare da saka hannunta da arfi ta rufe ma Hadeeya baki, kallon Safiya tayi dake kallon Hadeeya da tausayawa yadda jar fatar nan tayi wani iri duk ta guggurje tsabar duka, sama da asa ta kalli Safiyar ta ja tsaki kafin ta kama Hadeeya suka nufi akinta tana fa in "Muje ciki, ke baki iya sirri bane, ka an ake jira a gani dama a mana dariya." Alhaji Yusuf da bai gane komai bane yace "Ina kuma za ki kaita bayan tana magana?" Ba tare da ta juyo ba tace "Maganarmu ce ta iyali, idan ka damu da ji ka biyomu ciki, ba zan yarda a kasa matsala a farantin tsakar gida ba salon a mana terere." Wani murmushin baki da aikin yi Safiya ta mata tare da kama hannun Ahmad suka fita a falon dan dama farfajiyar za su je tana son kiran Saleema, kuma yanzu sam sai ta dinga jin wani irin nauyin yarinyar ko waya suke, kunyarta kasancewarta ar fari da kuma ita kanta Saleema yadda take mata wata hirar yake sa take jin kunyarta, shiyasa idan zasuyi waya ta fi tana tsakar gida yadda za ta dinga kallon shukoki suna cire mata duk wani ar da shakku. akin* ya samesu tana sake maimaitawa Ardiya abinda ya faru, rai ace a matu ufule yace "Lallai yanzu kam ba zan lamunci wannan lamarin ba, wallahi ararshi zanyi a hukumar kare ha in mata da yara, jaka ce na kai masa da zai dinga dukanki a kan wasu an iska? To ba zai yiwu ba, Allah kaimu safe lafiya." "Ameen." Ardiya ta fa a tana kawar da kai ita ma ta ora da "In ba iskanci ba ta ya ma zaki kamasa da mace a gadonki? Sannan ya dokeki haka? Ce masa akayi baki da gata ne?" Da sauri ta kalli mahaifin nata dake shirin ficewa a akin tace "Abba, Abba ararsa fa ka ce za ka kai, a Unicef?" Juyowa yayi yace "Ko ma a wace ungiyar ta kama kaishi zanyi, amma dai na gaji da wula ancinshi." Turo baki tayi ta kawar da kai tace "Ni dai wallahi Abba kar ka je, kasan fa su ba imani ne da su ba, idan ka kai ararshi kuma suka rufe min miji fa?" A tare suka wara idanuwansu kanta ba ma kamar Ardiya dake kusa da ita, dawowa yayi baya yace "Ban gane ba? To so kike a barshi ya kasheki kenan?" Cike da raini tace "Tunda dai bai kasheni ba Abba ai sai kuyi ha uri ko? Amma ni ina son mijina kuma fa har da yarinya a tsakaninmu ga kuma cikin jikina, shikenan ata su tashi ba tare da ubansu ba." A haukace tare da acin ran dake awainiya da ita ta kashe fuskar Hadeeya da osashen marin da ya sata kifewa asan gadon, da sauri ta mi e tsaye inda Hadeeya kuma ta tashi zaune tana kallonta a gigice, afa ta sa za ta fara wallo da ita yayi sauri rike Ardiya yana fa in "Me ye haka wai? Kanki aya kuwa?" A hassale ta nuna Hadeeya tace "Ka tambayeta mana, inba iskanci ba akan namiji kike neman lalata rayuwarki? To da kika zan kina sonshi kula ba kya son mu auki mataki, me ya sa kika zo mana nan? Tashi ki koma gidan nan sa dan ubanki ya jima bai kasheki ba." Tashi Hadeeya tayi ta koma kusa da ofar ban aki ta tsaya tana fa in" Ai na zo ne dan na nuna masa ina da gidan uba, kuma nan zan zauna sai na yi wata aya lokacin ya gane kurensa." Sake arin fizgewa tayi za ta nufeta tana fa in" Shegiya ar banza, ke dai wallahi kinyi asarar rayuwarki, akan n..." A tsawace ya saketa tare da turata kan gadon ta fa a yana fa in" Wai me ye haka? Wannan wane irin wula anci ne? A gabana za ki dinga sheganta min yarinya?" Wata uwar harara ta watsa mishi tare da juya kanta tana kallon bango ta rumgume hannayenta, wafa yayi ya kalli Hadeeya yace" Ai dai kin ce ba kya so a kai ararshi ko?" aga kai tayi alamar e, jinjina kai yayi yace" Shikenan, yadda kika za a, amma ki sani daga yau na tsame hannayenki akan lamarin dake tsakaninki da mijinki, tunda na yi iya arina amma ba ki gani ba." Juyawa yayi ya fita ta bishi da kallo tana gunguna asa kasa da cewa" To ka cire mana, zan kasa rayuxa da shi cikin farin ciki? Komai yana min na rayuwa, ita ma wannan abi'ar ina fata ya daina nan kusa." Ardiya ce ta nunota da yatsa tace" Wallahi ko zama zakiyi sai dai ki koma akinku na da, dan in kika zauna a kusa dani ina ganinki wallahi ba abinda zai hanani karyaki." Yatsina baki tare da ta e baki ta kalleta ta kasan idanu irin duba mai kama da harara sannan ta dice ba ta ce mata ala ba da tunanin safiya ta waye idan ta tabbatar lokacin fitar Zeid ne daga gida ta je ta auko kayanta, dan kuwa yaji za ta buga mai lasisi har sai ya zo neman da ta koma
Chapter 92 · 0% Book details