Sashe 30
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta bamu ba da wata ila a kawo miki gawarshi an iskan gari sun kasheshi." Rara o idanu tayi tace" Saleema? Ita ce ta bayar da shawarar a aura masa ar aiki? Na sani dama wannan yarinyar ce ta canza maka tunaninka." Sai kuwa ta arasa inda Mu'awwaz yake kanshi sadde ya ma rasa me ke masa da i ta finciki hannunshi tana fa in" Muje kai, in dai ni na haifeka bbu wanda ya isa ya aura maka wannan kucakar." akinta suka nufa suna kusan shiga Alhaji Auwal yace" Ji ni da kyau, mahaifina lokaci ani ya ebo ma auren, ranar juma'a da za ta zo za'a aura auren a masallaci, idan ki ka ce ba za'ayi ba kuma kika kaini bango, to ki sani sa'ilin da surukarki za ta shigo gidan, lokacin ke kuma za ki tattara kayanki ki barmin gida. " Mu'awwaz ya kalla da ya juyo ya kalli mahaifin na shi yace" Kai kuma ka sani ida har ka yi yun urin yin wani abu to za ka gami da acin raina, dan sai na rabaka da komai da yake nawa, duk wani da i da kake ji da dukiyata sai na tabbatar ka kai adamin da zaka iya yin barar abinci sannan zan ha aka da hukuma su hukuntaka." A fusace ya juya ya barsu tsaye sun shiga zulumi da ki imar da basuyi tsamlanin zai yi ikrarin ambatar musu ita ba. Sakin hannun Mu'awwaz tayi ta kalli Hajia Rabi da ita dai tunda suka fara aga muryoyi ta ce su yi ha uri Gaishata ta daka mata tsawa ta zuba musu idanu, nuyya ce ta yi ko zai kafta mata mari ba za ta tashi ko da tsaye ba bare ta damu. A hassale Gaishata ta wurga ma Hajia Rabi harara sannan ta banka ofar akin ta shiga har hawayen takaici da ba in ciki na ziraro mata da tunanin me za ta wa Saleema ta huce ma? _____________ Wajen Saleema kuma maganar saukar da za'a yi ne kawai a gabanta, yanzu haka wayar Mamanta ce a kunnenta cikin nutsuwa tace "E malam ta kawo min, ga takardar ma a hannuna." Daga angaren malamin yace "Yawwa Saleema, to kin gani yanzu kwana uku ya rage, kuma abinda kika bu ata za ki yi magana a kai ranar babban abu ne da ya dauki shafuka har uku, a haka ma a komai na saka miki ba, farkon za ki ga mu addima ne, na san wannan kin haddaceshi ba tun yau ba, abu ma fi mahimmanci shine ki haddace ko da rabin shafi na farko, tunda kinga minti biyar ne ake ba wa kowane alibi dan karatu." Numfashi ta sauke tare da kallon Khairat dake gabanta tace" To malam, nagode sosa Kamar yana gabanta ya mata murmushi yace" Ba komai Saleema, kuma ina fata ba za'a samu matsala daga wajen mahaifinki ba?" Ajiyar zuciya ta sauke tace" Malam ko da akwai matsala ma ni zan kar eta, sanin lahirata ya fi min komai, idan na bi ta mahaifina zan tashi ne babu duniyar kuma babu lahirar, to idan haka ta faru wace riba na ci ta zuwana duniya?" Cike da jin da i da kuma jinjina nutsuwar yarinyar yace" Hakane Saleema, Allah ya miki albarka, Allah ya ma karatunki albarka, in sha Allah wata rana mahaifinki zai yi alfahari da ke." A sanyaye tace" Allah ya sa malam, nagode." Da haka suka rabu Khairat ta koma dan dama takardar karatun da zata gabatar ta kawo mata, Saleema kuma shiryawa ta yi ta fita kasuwa ta siyo kalar yadin hijabin da zasuyi anko uta da sauran alibai, ba ta dawo ba saida aka inko mata shi yanda take da bu ata sannan ta dawo. Ko da ta shigo ta samu Mamarta da anwarta *Lubna*, gaisawa sukayi sosai cike da mutumtawa da kewar juna kafin tace mata " ar mamanta kenan, gashi dai daga arshe kela za ki yi saukar nan, burinki zai cika." Murmushi Saleema tayi sannan ta kalli Mamanta tace "Mama, kar fa ki fa ama kowa tunda kinga ba taro za'ayi ba." Harara Safiya ta dalla mata tace "Kina tsoron ya sani amma ki ka dage sai kinyi?" A ladabce tace "Mama ba tsoron ya sani yanzu ba na ke, wallahi ko da zai sani ne minti aya da gama karatuna a makaranta ban damu ba, na san dai ba zai wuce ya sake hanani wani abun ba ko kuma ya dakeni." Dariya Lubna tayi tace "Ba ma zai dakeki ba yanzu tunda kin zama budurwa, kuma ai babu wanda ya sani a dangi, nima yanzu ne na sani data kirani ta bani ku in nan da za'a miki wainar sadaka da kuma gallelen ragon da ta ce a siya dan a kai makarantar." Cike da farin ciki Saleema ta rumgume Lubna tana fa in" Kai amma na ji da i sosai Aunty." Da fara'a ta shafa kanta tace" Ai ke ar Mamanta ce." *Ranar Sauka* Gidan shiru yake kamar ko yaushe babu alamar wani hidima, hatta da Saleema da abun ya shafeta ita da mahaifiyarta, a aki suke suna kitsawa da warwarewa saboda tsaro, inda lokaci lokaci sukan yi waya da Aunty Lubna suna jin yanda komai ke tafiya daidai daga angarenta. Wayar mahaifiyarta ce ta yi ara da sauri ta auka da tunanin Khairat ce da take jiran ta kira ta bata malaminsu dan ta masa bitar haddata da ya ce yau da safe zai ji daga bakinta, ganin Hajia Rabi ce yasa ta mi awa Mamanta tace "Mama Hajiarsu Mu'az ce." Cike da tsokana tace "Ki aga mana, sarakuwarki ce fa." Turo baki tayi gaba tace "Maaaama." Dariya Safiya tayi ta kar i wayar ta ora a kunne da sallama, Saleema na jinsu suna gaisawa kafin daga bisani ta mi o mata wayar tace "Tana son magana da ke ne." A ladabce Saleema ta kar i wayar ta ora a kunne, a sanyaye sosai ta furta "Assalama alaiki, Mahmah." Shiru aka yi ba amsa, da mamaki ta ago wayar daga kunnenta ta duba sannan ta sake mayarwa tace "Hello!" arfan numfashin da ya sauke a cikin kunnuwanta ya sa ta kallon Mamanta da kyau da mamaki, cikin taushin murya kamar mai mata ra a yace "Baby shine kika manta dani ko? Ina wayarki take? Tun da aka kawo miki nake ta kiranki amma bana samu, anya ma kin saka layin a wayar? Matata me yasa kike min wula anci ne haka?" Gaba aya sassan jikinta saida suka amsa, yanda yake maganar kamar zaiyi kuka da saurin da yake maganar sai ta ji wani abu mai kama da tausayinshi a zuciyarta, a hankali ta mi e tana satar kallon Mamanta har ta fice a akin kafin tace" Ni ban wula antaka ba, kuma ma ai...ni fa..." Shirun da tayi yasa yace" Ke fa me? Har yanzu ba ki gama shawara da Maman ba ne? Saleema jiran amsar nan ta ki kinsan halin tashin hankalin da na shiga kuwa? Na rantse miki da Allah ko tashin hankalin da na shiga sanda na ke neman takardar wani aiki a wata Projet bai kai wanda na je ciki ba yanzu." Cike da shagwa a ta turo baki idanunta a rintse ita a dole kunya take ji kamar tana gabanshi tace" Malam ka mana shiru ko, kai bakinka ba ya gajiya da surutu? Ba na fa a maka na amince ba." Daga angarenshi da mamaki yace" Kin fa a min? Yaushe kuma?" Cike da yarinta da sangarta tace" Yanzu mana." "Wayeeehuuuu!" Ya fasa mata kunnuwa da wata irin mahaukaciyar ara, kafin ta ce wani abu ta ji muryarshi da alama ru ume Hajia Rabi yayi yana fa in "Ta amince wallahi Mama, wayyo da i, Mama kasheni kar farin ciki ya min yawa." A kunnenta tana jin yanda suke ta murna shi da Hajia har ta gaji da tsayuwa ta kashe wayar dan alamu sun nuna farin cikin da ya shiga ya mantar da shi waya suke. Kashe wayar tayi tare da nufa akin su Hadeeya dan kar o wayar nan, sam ta manta da ita a rayuwarta, tun ranar wayar ke hannun su Hadeeya amma ba ta damu ba. wasa ofar akin ta yi tare da sallama, daga ciki Hameeda tace "Shigo." Tura ofar tayi ta shiga tana zuba idanunta a kansu, da alama tun da suka farka basu tashi a gadon ba, dama ba su karya tare da su ba, yanzu kuma gasu kwance da kayan bacci a jikinsu kawunansu a hargitse gashi a sake sai aukar hotuna suke, a ganinta me ye abun auka kuma daga tashi daga bacci? Shin hoton hauka da ake auka kowane lokaci? arasawa ta yi ta tarawa Hadeeya hannu tace "Waya za ki bani?" Da sauri Hadeeya ta kalleta tare da marairaicewa sai kuma ta kalli Hameeda, kamar za ta yi kuka tace "Dan Allah *aunty* Saleema ki bar min ita har a gama bikin murnar samun jarabawar awata, gobe ne da an gama sai na baki." A hankalce ta kalli fuskarta da mamakin ita ce yau Hadeeya ke kira da aunty? Aunty fa? an ta e baki tayi tace "To ke ba ga wayarki ba?" Cike da sigar tausayi tace "Aunty wannan ba ta aukar hoto da kyau, wannan wayar fa babbar waya ce." Hameeda dake zaune gefe ne tace "Wallahi aunty da ma zaki bar mana ita, kinga fa har ta bu e tik tok, baki ga irin mabiyan da ta samu ba." ance idanu Saleema tayi tace "Dama abin da za ki yi da wayar kenan?" Da sauri Hadeeya ta kalli Hameeda tana aika mata garga in me yasa? Sai ka ce ta manta suna tare da ustazar gidansu ne, sai kuma ta kalli Saleema tace "A'a aunty, wa'azizzika nake orawa, tsaya ki gani." Ta fa a tana matsowa kusanta ta fara nuna mata wasu gajerun wa'azizzika tace "To kinga irinsu ne nake orawa, ba sa wuce minti aya zuwa second talatin, kinga ko ya mutum ya aru da ni ai ke ma kin samu lada." Jinjina kai Saleema tayi dan sosai abun ya kama hankalinta, numfasawa tayi tace "To ki bani kwalin wayar, da alama akwai layi a ciki." Da sauri ta sauka a gadon ta auko ta kawo mata, har ta juya za