← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 116

Sashe 4

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

idan ya ce wani abu na masa ki bashi hak'uri dan Allah." Murmushi ta sakar mata sannan ta fice a d'akin, a farfajiyar ta sameshi zaune da na'urarsa yana dannawa, kujerar gefenshi ta ja ta zauna a nutse tace "Abban Hajia, ta sameni yanzu take fad'a min wai ka hanata zuwa islamiya, shine na ce na san dai wani laifin ta yi ko?" Ba tare da ya kalleta ba fuska a d'aure yace "Ba ta yi laifi ba, kawai dai na soke zuwa makarantar ne, ba kuma ita kad'ai ba har da yan uwanta." Hankali tashe zuciyarta a kid'ime ta furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Da sauri ya juyo yana kallon da tunanin me ye na salatin? A razane tace "Alhaji, islamiyar fa ka ce ka dakatar da zuwa?" A k'ufule yace "Haka na fad'a Safiya, ko kina da ja ne?" Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke tace "Me ya yi zafi haka? Islamiya?" Mik'ewa yayi a hassale ya d'auki wayarshi da na'urar sannan ya kalleta yace "Na riga da na gama yanke hukunci, na kula wannan karatun ne ya ke d'auke mata hankali tana kasa fahimtar wanda nake so ta fahimta, shiyasa na ciresu gaba d'ayansu dan hankalinsu ya tsaya wuri d'aya." Mik'ewa tayi tsaye tace "U'uzubillah! Alhaji ka san me kake shirin aikatawa kuwa? Kai tsaye fa kamar kana k'ok'arin ingiza yaranka ne ga mummunar hanyar da ba zata b'illar da su ko ina ba sai halaka." Cike da shashantar da zancen ya kalleta sama da k'asa yace "Allah ko?" Sai kuma ya ja tsaki ya wuce ya barta tsaye yana fad'in "A ganinki kenan." Da kallo ta bishi tana jin yanda hankalinta ke sake tashi dan gaskiya wannan babban bala'i neke tunkarosu, islamiya ? Inda za'a koya wa yaran sanin ubangijinsu? Shi ne zai tsigesu saboda karatun da anfaninsa iya duniya ne kawai, shi ma a haka ba kowa da yayi shi ke morarshi ba. Kamar wasa sai kuwa maganar nan ta zama babba, Safiya da abun ya dameta ta yi iya k'ok'arinta wajen sake tuntub'arshi, amma a k'arshe mummunan kashedi ya kirta mata cewa zai d'auki tsatsauran matakin da ya dace a kan ta idan ta sake mishi maganar nan, hakn yasa ta tuntub'i wanda take ganin sun isa su fad'a masa su ji. Duk shekarun da suka d'auka haka ba ta tab'a faruwa ba, amma sai dayawa suke ganin laifinta dan su ma bokon suka sha suka k'oshi, dan haka suke ganin me ye a ciki to? Abinda yake ganin ya fi mishi ne ya yi sai su zuba mishi ido, wannan tashin hankalin da zulumin da ta shiga na tsawon sati biyu ya haddasa mata rashin cin abinci da muguwar damuwar da ta kwantar da ita rashin lafiya, wanda daga k'arshe cikin jikinta ya zube a wata asuba ta idar da sallah. Kamar kowane lokaci idan haka ta faru asibiti ya kaita aka mata wankin ciki, daga bisani lokitocin suka basu shawarar ko dai za'a juyar da mahaifarta ne saboda tana daf da kaiwa matakin da hakan zai iya cutar da ita, amma sam Alhaji Yusuf ya ce bai yarda dan gaskiya har yanzu ya na so ya ga wani sabon jaririn daga wajen Safiya, saboda mata ce da ba ya shakka ko k'yamar sake had'a zuri'a da ita, haka kuma ya yi bak'in cikin rasa wannan cik in da yake ganin har ya wuce wata uku amma gashi shi ma ya tafi, karo na bakwai kenan. *SHEKARA D'AYA* Hankali tashe ta k'araso wajen mai gadin tana fad'in "Sani dan Allah ba ka ga in da Saleema ta yi ba?" A ladabce ya girgiza kai yace "Tun d'azu data fita dai nan ta yi..." Ya nuna mata hannunshi na dama ya d'ora da "To kuma ban ga dawowarta ba har yanzu." Cike da d'imuwa tace "To ka ga dan Allah ka daure ka duba min ita a shagon nan na bayanmu, nan na aiketa ta siyo min madara ga shi har yanzu ba ta dawowa ba, ina tsoron kar wani abun ne ya sameta." Cike da son kwantar mata da hankali yace "A'a in sha Allah ma ba abin da ya faru, bari na dubo na gani." Cikin damuwa ta amsa da "Yawwa nago..." Mak'alewa sauran maganar ta yi sakamakon tsayawar motar Alhaji Yusuf a k'ofar gidan, da sauri ta dawo cikin gida ta tunkari komawa falo, ba wai dan babu hijabi a jikinta ba ko tana tunanin ranshi ya b'ace kan tana magana da mai gadin shi, sam wannan ba ya a tsarinshi dama, hasalima da kan shi yake fita tare da su ya zab'ar musu kalar mayafan da yake so su saka. Tashin hankalin shine aikin da ya saka ta yi masa ba ta kammala ba gashi har ya dawo, shi kuma mutum ne da baya son wasa da cikinshi, duk yanda yake girmamaka indai za kai masa wasa da cikinshi to za ku samu matsala, dalilin da yasa kenan ko Ardayi na wajen aikinta ya kan umarceta ta sarrafa mi shi wani abun, dan baya son cin komai a waje. Tun ba ta gama shigewa falon ba muryarshi ta dakatar da ita sanda yake fad'in "Me kike nema a waje?" Cak ta tsaya tare da juyowa a hankali tana kallonshi har ya k'araso, zagaya hannunshi yayi ta k'ugunta ya jawota jikinshi yana kallon kyakyawar fuskarta da ta firgice da tsoro, d'an jaye jikinta tayi kad'an saboda k'ofar falon bud'e take, kuma mai aiki da su Hadeeya na nan zaune suna aiki, sannan ga mai gadi dake rufe k'ofar wanda shi ma zai iya hangosu. Jin ba ta ce komai ba yasa shi sake fad'in "Je t' coute (ina saurarenki)." A duburbuce ta fara fad'in "Dama... Sani ne na ce ya d..uba min Sal...eema waje." Kallon tuhuma ya mata yace "Ina Saleemar ta je?" Hannunta ta kai ga wuyanta ta d'an shafo tace "Aiken ta na yi nan baya ta siyo min madara, ...shi ne fa...har yanzu ba ta..dawo ba." Da mamaki a fuskarshi ya sake k'ura mata ido ya ja baya kad'an yace "Hajiar ta wa kika aika waje?" Marairaicewa tayi tace "Ka yi hak'uri dan Allah." A tsawace yace "Na yi hak'urin me? Ban fad'a muku kar wacce ta tura min yara waje ba idan ba makaranta za su tafi ba?" Kamar za ta fashe da kuka ta sake fad'in "Ka yi hak'uri, ka kira ka ce na maka kunun madara ne, sai da na duba na ga babu madara a mangaza, kuma na fad'a maka amma ka manta, shine..." A hassale ya sake fad'in "Shi ne kika aika min yarinya waje a wannan ranar? Ina mai aikin gidan take?" A ladabce tace "Ka san yau girkin Ardayi ne, tana mata girki ne tunda ita tana wajen aiki." A tsawace yace "To mai gadi fa? Shi ba mutum ba ne ?" A sanyaye tace "To ai kai ka fad'a mana mai gadi iya aikinshi gadi ne kawai, kar wacce ta mishi aiken da zai sa ya bar bakin k'ofa." Nunata yayi da yatsa yace "Wallahi idan wani abu ya samu 'yata kan ki zan huce." Baki wangale tace "Kai na kuma? Dan na aike ta?" Jinjna kai yayi yace "Kina wasa kenan?" Saleema ce ta shigo gidan rik'e da leda a hannu sai Sani mai gadi a bayanta, da sauri suka nufeta in da Alhaji Yusuf ke duba duka jikinta yana fad'in "Uwata ba abinda ya sameki ko?" Da mamaki Saleema ta kalleshi ta girgiza kai a hankali tace "A'a Abba." "To me ya tsayar da ke?" Cewar Safiya na kallonta da kyau, sunkuyar da kai tayi tana rarraba ido, Sani ya kalla yace "Ina ka ganta?" Cikin ladabi yace "Wani gida ne nan kusa da shagon da aka aiketa ta shiga shan ruwa." Da mamaki Alhaji Yusuf ya kalli Saleema yace "... *Alhamdulillah.* 09/06/2022 22:37 - MOM LATEEF *BAIWATA* *NA* _SAMIRA HAROUNA_ *SADAUKARWA GA* *AHALINA* *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* _(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_ *[G. M. N. A]* _Bismillahir rahamanir rahim_ _4_ Da mamaki Alhaji Yusuf ya kalli Saleema yace "Me ya sa baki zo gida ki sha ruwan ba? Gidan ya na da tsafta ne?" D'aga kai kawai tayi tana ci gaba da rarraba ido alamar rashin gaskiya, Safiya dake kallonta sarai ta fahimci gidan da ta je, wato ta tsaya wajen Hafsatu mai d'inki ko? Girgiza kai kawai tayi ta mik'o hannu ta karb'i ledar aiken ta shige ciki, cike da farin ciki Saleema jin Abbanta bai mata fad'a ba, Mamanta ma haka sai kawai ta shige ciki da zumud'in wayewar garin gobe dan ta je ta nuna wa Hafsatu d'inkin da ta yi kamar yanda ta buk'ata. *Tana* idar da sallah azahar ta fito kai tsaye k'ofa ta nufa wajen mai gadi tace "K'awata ta zo?" "A'a." Ya bata amsa, juyawa tayi za ta koma sai yace "Ga ta nan Hajia." Da sauri ta juyo da farin ciki ta kama hannun matashiyar da ba za su wuce tsara ba, kai tsaye d'akin Mahaifiyarta ta wuce da ita kamar kullum, tana zama kan kujera ta fara ciro litattafan da suke karatu da su, d'auko na ta tayi ta zauna kusanta tace" Yau me malam ya koya muku?" Nuna mata tayi tace" Gashi nan, shi ne zan koya miki ke ma, kuma malam ya ce wai ki maida hankali sosai." Da fara'a ta jinjina kai tana jin dad'in yanda malamin na su ke nuna kulawarsa a kanta, tunda aka hanasu zuwa makarantar ya ke turo k'anwarsa tana d'ora mata karatun, ya yi iya k'ok'arinshi ma su had'u da mahaifin Saleema dan su yi magana kan kar a dagula mata karatunta amma Alhaji Yusuf ya k'i yarda su had'u, dan haka Saleema ta kawo wannan shawarar duk da yana tsoron abinda zai faru, amma dai gashi izuwa yanzu har an shekara d'aya ba abinda ya faru, alamu ne na mahaifin bai iya saka ido sosai a kan yaranshi ba kenan, dan da yana saka ido akan motsin 'ya'yan shi mata da yanzu ya fahimta duba da har bayan sallah isha'i a na zuwa a d'ora mata karatun. *Washe gari* Mik'ewar da ta yi daga kan teburin ya sa shi kallonta yace "Mamana ba dai kin k'oshi ba?" "E Abba."
Chapter 4 · 0% Book details