← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 116

Sashe 114

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

masa akan ma'aunin daya dace na hankalin an adam. *Tun* yamma da ta fita taje gidan awarta suka hirarsu, kafin daga bisani ta canca a ado inda ta ce ma awar "Muna da rendez-vous ne da Hajia Balaraba Seini, ni yanzu can zan wuce." Da mamaki sosai awar ta kalleta tace "Balaraba Seini? A ina kika santa ke kuma?" Wani sha iyin murmushi tayi tace "Hmmm! Ku zauna nan ba ci gaba a rayuwa, kin manta ina hul a da mayan mata?" Jinjina kai tayi dan ba za ta karyata ta ba tunda ta na gani tace "Lallai! Abun babba ne, Allah ya bada sa'a, ba dan ba sa kar an wanda basu san da zuwanshi ba ai da na biki." Murmushi kawai ta mata tare da mata sallama ta fita a gidan, abokin aikinta da sukayi aiki tare a shekara uku da suka wuce ta samu ofar gidan yana jiranta, aukarta yayi a galleliyar motar tashi suna tafe suna hira, a zahiri sun ha u dan a gaisa sannan ya ajeta masaukinta a yadda ta fa a masa, a ba ini kuma tana kallonsa ne a matsayin wanda ke tu ata a cikin babbar mota zai kaita gidan gwamnati. Tun a kan babban titin ta fara raba idanu tana kallon irin t saron dake wurin, ajiyar zuciya ta sauke tana sakin oyayyen murmushi saboda tuna idan ta ce ita ce Maman Saleema ta kuma zo godiya ne kan abinda aka musu irin tarban da za'a yi mata na musamman, a hankali ta kai hannunta kan robar ruwan dake kusa da giyar motar ta auka, bu ewa tayi fuskarta auke da murmushi ta kifa kai ta arasa shanyewa dan dama ka an ne. Kallonta mutumin yayi yana fara'a yace "Nima dai gobe zan shigo na ga jikin mai gidan." Kallonshi tayi tare da washe masa baki ta zura hannunta ta sauke glas din asa tare da jefa robar sannan ta sake agashi tace "Allah ya yarda, nima kuma kafin mu tafi zan samu lokaci na kai maka ziyara har gida." Da sauri ya kalleta yace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Ina robar...? Ya fa a yana taka birki, da mamaki ta kalleshi tace" Robar me?" Zaro idanu ya sake yi yace" Ruwan da kika sha, baya jefar da sharar a layin..." Glass in da aka wasa yasa shi saurin juyawa ya kalli angaren da yake, a hankali ya sauke glass in yana kallon sojan dake ri e da bindiga fuskarshi a ha e a harshen faransanci yace" Yalla ai fito." Kallon jami'in tayi tace" Yalla ai lafiya dai?" Da hannu ya mata alamar tayi shiru sannan ya bu e ya fita, ganin suna magana har yasa hannu aljihu zai biya tarar da aka masa ( Kwateeee) yasa ta bu ewa ta fita, wato shi tsautsayi idan lokacinsa yayi kai kake binshi ba shi yake binka ba ma, sun gama duk abinda zasu yi, an fa a masa tararsa ya biya, kawai Ardiya cike da warewa a harshen farasanci tace "Me ye haka malam? Ya zaka ata mana lokaci? Ka san ko ni wacece? Ka san ina zamu je da zaka tsayar da mu kana mana maganar banza? To ganin Hajia Balaraba zan je, ni ba uwarta ce ta musamman." A sanyaye mutumin ya matsa kusa da ita yace "Kinga shikenan muje." Sama da asa jami'in ya are mata kallo yace "A haka? Anya kuwa?" A hassale tace "Kana mamaki ne? Idan baka yarda ba na kirata a waya yanzu na sa a baka takardar sallamarka, wata ila ka yarda." ara ri e bindigarshi yayi da kyau ya shiga takowa inda take yana fa in "Bana tunanin akwai wanda kika zo gani a Presidential, amma bari na fara tabbatarwa, dan kama kika min da masu unar ba in wake." Kakkauran wayarshi dake aure a ugu ya ciro ya fara magana da jami'an dake gidan shugaban tare da tambayar ko akwai ba uwa da Hajia za ta yi ne? Amsa ta farko da aka bayar ita ce yau madame ta aga zuwa ganin likitanta a Egypt, dan haka ba ma ta asar, aje wayar yaui ya sake kallon Ardiya da kanta ke kallon doguwar katangar ba ta san me yace ba dan da zabarmanci yayi maganar. Cikin dakakkiyar murya yace "Kika ci ganin madame kika zo?" "E." Ta fa a har da aga girarta, wayarshi ta musamman ya shiga daddanawa yana jinjina kai ya sake cewa "Ai kika ce ta san da zuwanki ko?" "E, ba uwarta ce ta musamman." Ta fa a tana tsareshi da idanu, mutumin nan da ya ga ruwa take neman kwanto musu ne ya kalleta yace "Madame, ni na iya tafiya ko?" "Ba komai ka je kawai, nagode sosai." Ta fa a tana auko jakarta daga motar, kallonshi jami'in yayi yace "Ba tare kuke ba dama?" Da harshen zabarmancin da shima zaman tare ne ya sa shi iyawa yace "A'a yalla ai, a hanya ne na ganta." Jinjina kai yayi yace "Shikenan, za ka iya tafiya." Ba ata lokaci ya ja motarshi, har ga Allah Ardiya tsayuwar jiran ta ga kyawawan motocin da zasu arasata take, sai dai madadin mota mai kyau, wasu lafiyayyan mata ne suka sakata tsakiya da kayansu na kakin soja ayar ma wal kwabo ne a kanta sai hular da ta rufe da shi. *Kwananshi* hu u yau a asibitin, amma madadin a ce yana kwance yana jinya sai ya zama na hankalinsu tashe yake na rashin sanin inda Ardiya take kwana biyu, gashi sun oyewa mutanen gidan suna so su fara sanin me ya sameta kafin wani ya ji, nema suke ta yi har unguwar da ya zama ita ce ta arshe da Ardiya ta ziyarta, sai dai if yadda ka san saceta aka yi. Kwana biyun da tayi ta canza kama sosai, kuma a haka ba dukanta sukayi ba sai dai yunwa ce kawai da ishin ruwa, tun ranar da suka kaita can suka rufe da wata bagwariya ta cizga mata wani sahihin marin da ya sa hannayenta fitowa a kumatun Ardiya tun shi ta nutsu ba ta sake ko tari ba idan ba da izninsu ba, tuhumar da suke mata shine me ya kawota gidan kuma har ta yi ikrarin ganin madame ta zo kuma ta san da zuwanta, sai gashi madadin tarba ta musamman ana tuhumarta da ar jam'iyar adawa ko ar tawaye, tabbas ta ga rayuwa kuma ta gane me rayuwa ke nufi. Yanzu haka da take takure jikin bango kallon babban jami'in tayi da ya ora waya a kunne da girmamawa ya amsa da "E madame, yanzu haka muna tare da ita." Ba ta auke dubanta gareshi ba saida ta ji yace "E madame, abu aya kawai take ta fa a, mun so samun bayanai a kanta kafin ki dawo, amma cewa take ita mahaifiyar gimbiya Saleema, kuma mun tuntu i mai martaba sarki Abdus-samad in, ya ce mahaifiyar matarshi tana tare dasu a Mara i, dan haka koma wacece kawai ana so ayi anfani da ita ne dan a cutar da su." Shiru yayi alamar yana saurarenta, da sauri ya juyo ya kalli Ardiya yace" Ke me ye sunanki?" Da sauri kamar za ta yi fitsari a wando tace" Ardiya, Ardiya ne, wallahi tallahi ni matar Baban saleema ce gimbiya." Maimaita sunan nata ta ji yayi kafin yace" Ok madame, to madame." Ba'a fi minti sha biyar ba aka sake kiranshi aka basu umarnin sakinta, godiya ta dinga yi a zuciyarta tana gyara aurin an kwalinta, tana saka takalminta kenan ya nunota da yatsa yace" Nan gaba sai ki kiyaye, ki daina arya da sunan wani dan kina son shiga wurin wani, ba dan an kira gimbiyar mara awa ta tabbatar uwa kike gareta ba, da ban san ranar fitarki a nan ba, ki *tsarkake zuciyarki*." Yana fa a ya shige ya barta nan ita kuma ta shiga takawa da kyar tana ayyana" Yanzu ma ita ce ta taimakeni? Yanzu ma alfarmarta na ci kenan? Idan hakane me ye anfanin yi mata hassada? Baya na ke yi yayin da take gaba da gudun tsiya, idan na ci gaba da watsa mata takin hassadar nan, zan fara aga kaina sama ne idan ina son hangota, dole na dakata daga nan... Ya isa haka." Ko da ta zo asibiti a wannan hali Alhaji Yusuf bai ko kulata ba, dan duk abinda ya faru Saleema ta fa awa Alhaji Rabilu da sai yau ya fa a mata hankalinsu tashe yake da rashin sanin inda take shi kuma ya fa a masa yadda aka yi, kamar jiranta ake aka bashi sallama, ko waiwayawa baiyi gareta ba suka bar asibitin. Ba ta ara sarewa ba saida ta ji yana maganar a ciro masa ticket na komawa, kuma da ciro ticket in da lokacin da motar za ta tashi bai fi minti talatin ba, tana ji tana gani ya tafiyarshi shi ka ai ya barta kuma Alhaji Rabilu bai ce masa a'a ba, sai ma tambayarta da yayi ita ma yaushe za ta tafi ya sa a ciro mata na ta ticket din, abu goma da gomiya tara, sai lokacin da ta duba jakarta da tuda aka sakota sai lokacin ta bu a ta ga tasss babu ku en da take ganin duk ta kar a a hannun mutane sanadiyar aryar da take musu da kuma babbar wayarta. Tsaf! Aka yashe mata tanadinta na komawa garinta wanda hakan ba aramin kassarata ya yi ba. aramin canji ta samu a gidan ba da ta zo, tsaf! Alhaji Yusuf ya fita a shirginta hatta da gaisuwar ina kwana idan ba a gaban mutane ba baya amsa mata, haka ma Hamdeeya sai wata irin sha uwa data shiga tsakaninta da Safiya wacce ta sa ta fi girmamata yanzu fiye da ta ta uwar da ta tafi ta barta a lokacin da take bu atarta, gaba aya ba ta jin dadin komai, hakan yasa aikin ma da take zuwa yanzu ba ta wani jin da inshi tana dai zuwa ne. Ana haka ta ji a bakin Safiya wai Alhaji Yusuf zai ma Hamdeeya aure a hutun da za'a yi na wannan shekarar da malaminsu Saleema Yayan Khairat wanda da Alhaji Yusuf in ya gala gane darasin rayuwa ya kai kanshi gabanshi ya fa a mishi irin
Chapter 114 · 0% Book details