Sashe 35
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dan gaskiya ba dan ba ya daga cikin al'adarsu auren dole ba, da ta nemawa *yarimanta* auren kamilar yarinyar nan, ita dai kyawunta take gani fiye da kima, sannan nutsuwarta take gani fiye da tunanin mai hasashe, ba dan yau ne ha uwarsu ta farko ba kar yarinyar ta ga wautarta, da ta fashe mata da kukan shagwa a sannan ta ce mata "Dan Allah ki auri ana, ko shi ma zai shiga sahun masu cikar kamala wacce aure ka ai ke samawa bawa ita." Amma sai ta shafo fuskar Saleema tace "Allah ya miki albarka, Allah ya baki miji na gari kamar * ana*, wanda zai kula da ke ya mutumtaki." Cike da kunya Saleema ta sadda kanta asa sannan ta amsa asan makoshi da "Ameen." Alamu ta mata da cewa "Ki je, na san yanzu Abbanki na jiranki." Rusunawa tayi kamar za ta sunkuya tace "Nagode ranki shi da e, Allah ya ara lafiya da nisan kwana mai albarka." Murmushi kawai tayi tana jin kewar yarinyar na lullu eta tun bata mata nisa ba, tana kallo jakadiyar da hadiman nan suka tisa Saleema a gaba har suka fice a falon na ta na musamman, tsintar kanta tayi da yi wa yaronta addu'a ya samu mata kamar yarinyar nan. Abbanta na tsaye yana jiranta jikin mota, da idanu kawai ya rakata ganin wata shiga da aka mata tamkar wata gimbiya ko sarauniya, shi dai bai gushe yana kallon ar tashi ba har saida suka shiga mota aka auki hanyar mayar da su gidansu, a lokacin ne kiran sakataran gwamna ya kirashi ya shaida masa yalla ai fa na ta jiransu, ha uri ya bayar tare da fa in za su iso yanzu, dan haka yana aje wayar ya kalli aya galadiman da zaman banza kawai yake a motar hannunshi ri e da atuwar dorina yace "Ranka shi da e, ko za ku iya ajemu gidan gwamna *Nasir Abdu*?" Jinjina kai yayi yace "Yanda ka ke so yalla ai." Kallon matu in yayi ya bashi umarnin aukar titin dan su ba ba in gidan gwamnan ba ne wanda yanzu ne ma ya daina yawan kai ziyara gidan da mai martaba ya rasu, amma da kullum cikin kai caffa yake da kamun afa. *Bayan fitarsu* Mai gadi ne ya sake shigowa a karo na biyu ya samu Safiya yake fa a mata "Hajia wasu matasa ne suka zo, kuma sun ce Alhaji Auwal ne ya turo, to kuma na ga mai gidan baya nan shiyasa na ce bari na miki magana." Da kula tace "Ka ce musu ina zuwa." Karaf! Ardiya da fitowarta kenan ta ji me ake fa a tace "Muje na gansu." Ba ta jira komai ba tayi gaba mai gadin ya bita, Safiya kam ta e baki tayi ta gyara zamanta ta maida dubanta kan tv, farfajiyar gida ta samesu tsaye suka gaisa kafin aya a ciki yace mata "Hajia dama Alhaji ne ya aikomu mu kawo sa Rarraba idanu ta fara yi tace "To, sa o kuma? Wa ya ce a ba?" Gaba sukayi alamar ta biyosu aya na fa in "Gaya nan waje." Bayansu ta bi har ofar gidan duk da babu mayafi a jikinta, irin motunan nan ta samu masu afa uku kuma ba adaidaita sahu, dan musamman an yi su ne dan aukar kaya har guda biyu, aya moton ledoji ne ba e a shirge, sai ayan kuma dake auke da buhunan flawa da bududuwan mai da buhu siga. Ardiya dake kallon kayan da mamaki kafin ta tambayi abinda ke ranta wani matashi yace "Yawwa, Alhaji ya ce wannan a yi sadaka, duk ma ota da an uwa a tabbatar kowa ya samu, wannan kuma..." Ya fa a yana nuna inda buhunan suke yace "Ya ce a yi sabuwar tuya dan sadaka, sannan akwai matan da suke masa wainar sadaka duk sati zai turosu su kama aikin yanzu." arni arnin da ya daki hancinta ne ta yamutsa fuska ta nuna inda ke da ba en ledojin tace "Me a cikin wannan?" aya daga ciki ne yace "Nama ne, sa guda ne aka yanke, ko hanji Alhaji bai yarda an cire ba ya ce a kawo gaba aya." Wani wula antaccen kallo ta bisu da shi tare da yatsina baki ta juya tana fa in "Bari in kira muku uwar yarinyar." Da mamaki suka bita da kallo da tunanin dama ba ita ce uwar ba kuma ta fito? Ba tare da damuwa ba suka ara gyara tsayuwa, dan ko za su kwana sai sun jira an sauke musu kayan nan, dan daga yadda Alhaji Auwal ya dinha basu umarni alamu ya gwada yana daraja mutanen sosai. Jim ka an Safiya ta samesu daga ofar akin mai gadi tsaya suka nuna mata, mai gadi ta umarta da ya bu e musu ofa su shiga da kayan ciki sannan a sauke, komawa tayi falo ta barsu ita kuma ta fara kiran wa'da zasu zo dan taimaka mata a kan aikin nan. *Governor's house* Kasancewar yau lahadi gwamna yana gari kuma yana gida, hakan yasa akan ara mishi tsaro saboda yawan ba in da yake ara samu musamman na ananan an siyasa masu tasowa, a iya ganin Saleema dai a inda motar ta faka duka jami'an tsaro ne suna ta shawagi, dake an san da zuwansu ba su wahala ba sai cajesun da aka ara yi har aka raba Saleema da alkyabbar da ta so zuwa gida da ita mahaifiyarta ta gani, wani jami'i ne daga cikin gidan ya dinga musu iso har suka wuce falo uku kafin su isa a na hu u, kujerun alfarmar ya nuna musu a harshen faransanci yace " Restez ici, monsieur le Gouverneur ca arrive maintenent." Alhaji Yusuf ne ya masa murmushi yace "Merci." Ba jimawa kamilin dattijon ya fito mai cikar zati da haiba, yana fitowa kuma Saleema ta sadda kanta asa, har ya araso a nutse da fara'arsa ya cakumi hannun Alhaji Yusuf da ya mi e dan girmamwa, gaisawa suka fara yi da harshen faransanci hakan yasa Saleema mi ewa tsaye ita ma da tunanin to fa yan boko an ha u kenan, a sanyaye ta gaisheshi, da wata sabuwar fara'ar ya kalleta yace "Haleema, comment va tu?" an satar kallonta Alhaji Yusuf yayi ya gimtse fuska dan ya san sai ta kwafsa mishi, wacce ko ha a lambobi ke bata wuya ta ina za ta san me ya ce bare ta amsa? Kawar da kanshi ya yi yana jin ranshi na neman bacewa yanzu yanzun nan. " Je vai bien." Jin haka daga bakin Saleema ya sashi saurin kallonta, amma sai ji yayi gwamnan ya sake fa in "Et ta mere?" A sanyaye cike da ladabi tace "Elle va bien." Sakin hannun Alhaji Yusuf yayi yace "Alez y on va manger." Kallon juna sukayi, ta haka Saleema ta fahimci kamar abin da ke ranta ne shima a ranshi, dan alamu sun nuna yana girmamashi sosai, amma kuma bai yi yun urin yin abinda ya ce in ba, jin ua sake maimaita musu su je su ci abinci yasa Saleema kallonshi a nutse tana fara'a tace "Moi j'etait plein, je manger a la maison." Kallon Alhaji Yusuf yayi da mamaki yace "Hanata ka yi?" Murmushi yayi kawai yayi dan shi dai ua fahimci idan bai mutu jiya ba saboda mamaki to yau kam zai she a barzahu, to in ba riga yaushe Saleema ta iya jin faransanci? Maida kallonshi yayi ga Saleema yace "Haleematu." Sadda kai ta sake yi tace "Na'am yalla ai." Cike da kulawa yace "Kinyi karatu mai kyau jiya, Allah ya miki albarka." Kamar za ta yi ruku'i ta sunkuya tace "Nagode yalla ai, ameen." Wani basaraken kallo ya mata ta asan idanu yana fa a murmushinshi yace "Aure fa? An shirya? Ko karatu za'a ci haba da yi?" Bayan kunya da maganarshi ta bata har da murmushi ma, da sauri ta rufe fuskarta da tafin hannayenta tana murmusawa, kallonta Alhaji Yusuf yayi sannan ya kalli yalla an yace "Yanzu haka dai sa ranarta za'ayi, yaron ma ai an gidan Alhaji Auwal ne." Mamakin jin kalaman daga bakin mahaifinta yasa ta saurin agowa za ta kalleshi, sai kuma ta kalli yalla an da take yanayinshi ya canza daga sakakkiyar fuskar nan zuwa ba yabo ba fallasa yana ya e yace" Alhaji Auwal dai dana sani?" " E shi." Ya fa a da girmamawa, jinjina kai yayi da yanayin rashin walwala yace" Allah yasa alkairi." "Ameen." Alhaji Yusuf ya fa a, nuna musu kujerun yayi yace "Bismillah, ku zauna." Zaunawa sukayi shi kuma yace "Ina zuwa ko." Da kallo duk suka bishi har Saleema na mamakin me ya ha e fara'arsa lokaci aya haka? Gashi kamala ce da matsayi yasa shi zama babban mutum, amma shekarunshi ma bai wuce arba'in da shida zuwa da bakwai ba. Ganin shigewarsa ta ci gaba da kalle Kallen tana mamakin yanda gidan yake shiru ba alamar wasu mutanen bayan shi da masu gsaronshi, kuma hakan ya faru ne sakamakon nan angarenshi ne, a irin wannan lokaci idan ba shi ya nemesu ba su kan barshi ne ya huta, musamman yau da zai yi ba in da shi ka ai ya san me ya tsara ma kanshi, hakan yasa ya dakatar da kowa daga shigowa sashen nashi har amaryar da take ganin tana yadda take so haka ya taka mata birki ba dan ta so ba saboda ta so sanin me zai faru dan ta fa awa Ardiya. Fitowarshi tare da wani jami'in a bayanshi yasa suka sake mi ewa, jakunkunan takarda irin wanda ake zuba kaya a manyan kamfani ko shaguna ya nuna mata dake hannun jami'in yace "Haleematu, ga wannan ko, nagode da kuka amsa gayyata ta." Hannu ta kai za ta kar a cike da kunya tace "Nagode yalla ai, Allah ya saka maka da alkairi." Da sauri ya dakatar da ita da cewa "A'a ki barshi, ai bai kamata ki wahala ba, zai kai miki har mota." Cikin ladabi Alhaji Yusuf yace "E to yalla ai, da ya ke ba'a motarmu muka zo ba, daga gidan margayi mai martaba muke, sune suka aje mu nan." Da fara'a a fuskarshi tare da ganin kamar wata damar ce ya samu da zai sake kusanci da su yace "Wannan ai ba