Sashe 28
Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta zauna a gidan ta dinga kama muku aiki har ta fito min da wanda ta ke so nan da wata biyu na aurar da ita." Da sauri Saleema ta furta "Aure Abba, amm..." Kallon da ya mata ya sa ta yi shiru, wafa yayi tare da fa in "Idan la ba ki da saurayin ni zan miki, kuma ma ai ba zaki rasa ba tunda har kika i maida hankali ga karatu, na san soyayya ce ke hanaki." Ardiya da take jin da in haka cike da kissa tace "Ai shekarunta sun isa na aure, ba ka ga duk wata wahalar da take sha kafin ganin al'adarta ba?" Kunya ce ta sa Saleema du ar da kanta, inda Hadeeya da Hameeda suka yi dariya a tare, Safiya kuma kallon Ardiya tayi tace "Me yasa kike min hakane? Dan ba arki ba ce?" e baki Ardiya tayi tace "Kowa dai na gidan nan ya san gaskiya na fa a, na tabbata soyayya ke hana Saleema karatu har sha'awarta ke ara tunzura, idan ba'a aurar da ita yanzu ba wata rana abun kunya za ta auko..." Cokalin da take zuba miyar da shi dake hannunta ta buga a kan teburin da arfi tana rintse ido tace" Ya isheki haka." Duk kallon Safiya sukayi da tayi kwaratsin, nuna Ardiya tayi da cokalin za ta yi magana, da sauri Alhaji Yusuf ya mi e tare da jawo Safiya jikinshi ya an rumgumata, ba ya so ta aga murya sosai, ba ya so ta yi fa a da Ardiya, ba ya so ta aga hankalinta kamar yadda likita ya fa a masa a kiyaye duk wani tashin hankali da aci ranta saboda cikin dake jikin na wata uku. Yun urawa ta yi za ta tashi tana sake fa in "Wallah..." Hannu ya kai kan bakinta ya toshe cikin ra a yace "Ya isa haka Sofeena, rabu da ita kinji uwargidana." A hankali ta dinga sauke numfashi tana ara tusa kanta a irjinshi, shafa bayanta ya dinga yi yana kallon fuskar Ardiya dake kumbura tana musu wani mugun kallo. Saleema kunya ce ta sake kamata a ranta ta ayyana" Tofa! Mun dawo kenan, wai Abbanmu ba ya girma ne shi?" ago kai Safiya tayi ta kalleshi idanunta taf da hawaye tace" Dama ina son magana da kai." Cike da kulawa da guje duk abin da zai ata mata rai ya tallabo ha arta yace" Ina jinki, ko sai mun shiga ciki?" Turo baki tayi cike da shagwa a ta an saci kallon Ardiya da har yanzu ke kallonsu tana mamakin mijin na su, mamakinta bai wuce yadda in suna tare yake nuna ba wata sai ita ba, ko aikace wasu lokuta ya na nuna mata ta fi Safiya mahimmanci, amma duba yanzu yanda yake ta nani eta a gabansu wai dan tana da ciki, hmmmm! Ta fa a tana ayyana "A haifeshi mu gani." Safiya da ta fahimci haka cikin shagwa a tace "Dama ku i na ke so, kuma ka ga watan da ya wuce ba ka bani komai ba." Ajiyar zuciya ya sauke jin matsalar ta ta ba wata babba bace, dama dan bata aiki ya auki al awarin bata jaka saba'in kowane wata, duba da Ardiya tana aiki kuma tana aukar albashi, dan kar abun ya mata yawa ya shi aukar wannan matakin, duk da wasu lokuta idan ya bata ma sai ta ce ba ta bu ata ko kuma ta auki rabi, wani lokaci kuma shi yake mantawa kamar dai yanda ya yi watan da ya wuce. Cikin sassauta murya yace "Shikenan, zan ganki anjima, yanzu je ki huta akinki ina zuwa, bana son hayaniyarki." Jinjina kai tayi alamar to tare da nufa hanyar akin na ta, da kallo duk suka bita har Hadeeya ta ta e baki, dan ita ba ta ta a ganin haka ba sai yau, Saleema kuma zaman ne ta ji zai isheta tunda babu mai tsaya mata a wurin, mi ewa tayi za ta bi bayanta ba kunya ba komai Alhaji Yusuf yace "Kar ki sake ki takura min mata da matsalolinki, ciki ne da ita kuma bana son abin da zai aga mata hankali." Rufe idanu Saleema tayi sai kuma ta girgiza kai tace "Ba wajenta zan je ba, falo zan zauna." Tana wucewa Hadeeya ta kalleshi cike da wauta da ga anci tace "Abba, ka ga ni dai irin wayar da na ke so ka siya min, ta ya ma Saleema za ta ri e wannan wayar ni ina fama da wannan Samsung." Ko kallonta bai yi ba yace "Um um! Ban da arzi in da zan siya miki wayar nan." Turo baki tayi ta kalli Ardiya tace "Momma..." Da yatsabta nunata tace "Kar ma ki fara, ubanki bai iya sai ni ce zan iya?" an kallon Ardiya ya yi sai kuma ya girgiza kai ya ci gaba da cin abincinshi, Ardiya dake kallonshi tana ta hassala ne tace "Shi ne ma ba zaka kulani ba." agowa yayi yace "Me ya faru?" Cike da masifa da harshenta na hausa da baya fita da kyau tace "Shi ne zaka wula antani a gabanta? Ka yi ta wani rumgumeta dan na gane ita ma mowa ce a wurinka." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ki yi ha uri to, ba dan ranki ya ace na yi ba, na fa a miki yanda likita yace game da lafiyarta, dole mu kiyaye ata mata sannan mu lalla ata." Jinjina kai tayi tace "Shikenan to ya yi, sai ka yi ta lalla atan ai." ewa tayi a hassale ta nufi akinta, da sauri ya tashi ya bi bayanta dan ba zai so ita ma ta yi hushi ba, dan wallahi al awari ya la kanshi cewa ba zai kuma kusantar Safiya ba sai ya ga cikinta ya girma, dan yanzu gani yake motsi ka an zai sa ta yi ari. *09:00* Safiya ta sameta akinta har ta yi shirin bacci tana zaune kan gado tana karatu, da fara'a ta araso ta zauna kusanta ta mi o mata ku i, da sauri ta amsa tana murna ita ma, idaya ku in tayi ta kalleta tace "Mama duka wannan ne suka bayar?" Da murmushi ta jinjina mata kai alamar e, ita ma jinjina kan tayi ta fa a jikinta tace "Nagode Mamana, gaskiya Abbanmu yana sonki." Murmushi kawai ta sake yi amma ba ta musa mata ba, dan gaskiya ne ya na sonta kuma yana yawan fa a mata haka, sannan a aikace ma yana nuna mata, duk irin yanda take da sani kan ya auro Ardiya ne saboda iliminta da wayewa, sannan ya na sonta da kuma anta kyawawa, amma tana da tabbacin soyayya ta gaskiya yake mata, dan kuwa ba ta nemi komai ta rasa a wajenshi ba, duk abin da zai ma Ardiya shi zai mata, idan zai kashe ma Ardiya million aya to ita ma haka, matsalar Saleema ce ma kawai ta sa wasu lokuta yake fa a mata magana mai aci ko a gaban yaran, wanda hakan take aukarsa a matsayin sa ani na ma'aurata. Amma ko daren jiya da suka je asibiti aka fa a masa tana da ciki, kai tsaye wajen cin abinci suka wuce ya kashe mata ku i sosai a kan abinci kafin su zo gida, jimawar da sukayi yasa Ardiya rufeshi da masifa har saida ya fa a mata dalilin ka agata tayi daga jikinta ta kalli fuskarta tace "Kin san me? Ba i mukayi a gidanmu." Da mamaki tace "Ba i kuma? Su wa ye?" Irin kallon tuhuma da tsokana ta mata tace "Alhaji Auwal ne da mahaifinshi, sai kuma... Yaya Mu'az inki." arashe tana mata dariya, waro idanu tayi tace "Mu'az kuma?" Da sauri ta nemi saukowa daga kan gadon tace "Mama mama, na ro eki Mama kar ki bari Abba ya biyewa haukan Mu'az, shi fa sam ba ya da hanakali." Dariya ta yale da ita tace "Zamu gani dai waye mahaukacin, yanzu tashi ki je Abbanki na nemanki." e fuska tayi kamar za ta yi kuka tace "Maaamaaa." Ita ma kya e fuska tayi tace "Na'aaaam.." aure fuska tayi tace "Tashi ki je." Jiki a sanyaye ta mi e ta auki hijabinta iya gwiwa ta saka sannan ta fice cike da fatan ba abin da take tunani ba ne zai faru. Dan in kuwa hakane to tabbas Mu'az bai da sanya a lamura kuma ya mata shigar sauri, amma fa hakan ba ya na nufin za ta amsa bu atarshi ba ne, duk da kuwa bayan dawowarsu ta yi tunaninshi sau aya, dan sosai kalaman nan na shi a ha uwarsu ta arshe suka tsaya mata a zuciya da ma walwarta. Tashin muryar Alhaji Auwal yasa ta nutsuwa sosai ta sadda kanta sosai duk da fa uwar da gabanta ke yi ta wasa ofar tare da sallama a sanyaye sosai, ba tare da ya amsa ba Alhaji Yusuf ya bata umarni da "Shigo." Tura ofar tayi a hankali ta shiga takawa a nutse ba tare da ta aga ta kalli kowa ba, ita dai kawai ta ji idanun mutane a jikinta suna yawo, sannan daga amshin turaren one million ta gane kusurwar da Mu'az yake zaune dan shi ke anfani da turaren, daga kallon afafu ta gane inda mahaifinta yake, a kusa da shi ta zauna a ladabce tana fa in "Ina wuninku." "Lafiya lau Saleema." Alhaji Auwal da Papi suka fa a a tare sai Alhaji Auwal da ya ora da "Baby kin ga har na fara kewarku tun yanzu, ina ma za ki koma gidana da zama?" Sai kuma ya yi dariya yace "Ko da yake abinda ya kawomu kenan, amsarki ita za ta bayyana mana shin za ki rayu da mu ko akasin haka, dan babu wanda ya isa ya miki dole in dai ina raye." Wani kallo Mu'az ya watsa mishi ta asan idanu da tunanin "Za ko kaga abin da zan yi, a cikin gidan nan zan irka mata ciki in ya so kwa shafa mana fatiha bayan ra awa anmu suna." Maida dubanshi ya yi ga surukin na shi dake kallon Saleema yana fa in "Mu'az ne dama ya ce yana sonki, kuma ya ce kin san da maganar, yanzu haka sun zo neman aurenki, kin amince a bashi aurenki?" Alhaji Auwal