← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 116

Sashe 49

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gadon tana saka hijabinta ta fice ta basu wuri, saidai ba ta arasa falon ba ta tsaya a iya corridor dan gaskiya tun jiya kunyar fita take. Ganin Saleema ta fita ta mi e za ta ra ashi, da sauri ya sha gabanta tare da ri o hannunta, da sauri ta fizge ta kalleshi tace "Ka daina ta ani." Marairaicewa yayi yace "Soffee, dan Allah kada ki bari damuwa ta samu muhalli a gangar jikinki ma bare ruhinki, kin fi kowa sanin illar da hakan zai haifar mana." A gatsalce ta kalleshi tace "Me wai? Cikin jikina? Kai ma ai kasan ba mai zama bane, kamar yadda ba in cikinka na baya ya yi sanadiyar zubewarshi, yanzu ma haka ce za ta faru, da haka na gane ba sona kake ba, rayuwata kake nema *Isuhu*." Kecewa ya yi da dariya ya an ja baya ya nuna kanshi yace" Isuhu? Ni?" Ba alamar wasa tace" E in, ko arya na yi ba sunanka bane, na fa a Isuhu." Gumtse bakinshi yayi yana dariya yace" Shikenan na ji, yanzu dai dan Allah kiyi ha uri, ke ma kinsan abinda ta yi bata kyauta ba, ni fa ubanta ne, ta ya za ta kai arata ga wani? Kenan ni ban isa na yanke hukunci a kanta ba?" Fashewa tayi da kuka ta ja baya har saida ta zauna bakin gadon tace" Shine sai ta wannan dukan za ka nuna mata kuskurenta, wallahi ban yarda ba, haka kawai za ka dinga narkar min yarinya kamar wata jaka." usawa yayi gabanta yace" Shikenan na ji, daina kukan to, fa a min ya kike so na yi? Na miki al awarin zan yi amma bana son damuwarki." Kallonshi tayi tace" Ka amince ta koyo abinda ranta yake so." e fuska yayi tare da kawar da kai yace" Ban da shi, ki nemi wata alfarmar." e kukanta tayi tace" Shikenan, amma ka manta da nima matarka ce." aramin tsaki yayi ya kawar da kai yace" Soffee, bana so fa, ki daina irin haka kamar wata yarinya, ta ya zatayi laifi na hukuntata kuma ki dinga hushi dani? Dan kinga ina damuwa ne da damuwarki?" ewa yayi tsaye ya karka e rigarshi yace" Ki ci abinci a kan lokaci, kada ki ci ano dayawa, sannan ki sha magungunanki a kan lokaci, ki samu isashen bacci, dan Allah ki min wannan alfarmar ko dan abinda ke cikinki." Har zai tafi sai kuma ya tsaya cak, ba tare da ya juyo ba yace" Kada ki sake ki harareni idan na juya." eyarsa ta kalla dan magana ta gaskiya har tayi haramar hararen tashi, amma jin haka sai ta kasa binshi da hararar, saida ya fice ta daki gadon da hannu tace da fa in" Ba zan yi in ba, ba zanyi ko aya da ka fa a ba." *08:20 na dare* Kiranta yayi ya ce su ha u a gidan cin aminci na *Kebab*, ba gardama ta ce masa za ta zo yanzu, duk da ta san dare ne kuma mahaifinta na gidan, amma a ganinta da ta ce masa za ta je kar an wasu takardu an wuce wurin, addu'a zai mata har da guzurin ku in adaidaita. A gaggauce ta shiga shiryawa, Ardiya dake zaune da na'ura gabanya ana ta faman lissafi ta kalleta tace "Wai ina za ki je na ga kina ta shiri? Ko ba o kikayi a waje?" Turaren da take murzawa a hannayenta ta shafa a wuyanta sannan ta juyo ta kalleta tace "A'a, fita zanyi." "Ina?" Ta fa a tana ura mata idanu, saida ta auki wayarta a hannu da jaka ta rataya tace "Mama Yaya Mu'az ne ya zo na zo mu ha u yanzu." A hassale Ardiya tace "Ke saurara bana son iskanci, wai me ye tsakaninki da shi? Ke baki da zuciya ne? Ba ki ga kayan Yayarki ya kawo jiya ba?" Sassauta murya Hadeeya tayi sosai ta zauna kusa da ita tana daddana wayarta tace "Momma kinga, wani abu nake shiryawa, ban san ko zaiyi aiki ba, amma dai na tabbata zai kawo tsaiko a auren nan." an wayar ta sake yi tana kallon videon Hadeeya kuma na fa in "Ba na nuna miki ba jiya, to ai shima na tura masa kuma na ce masa zan orashi a tik tok, shine ya tsorata ya ce kar na zubar mata da mutumci, nafa a masa idan bai amince da aurena ba sai kowa ya ga tsiraicinta, shi ne ya ce zai kirani muyi magana." Zuba mata idanu tayi na wasu da u, sai kuma ta washe baki da yanayin jin da i ta nunata da yatsa tace" Kinga anfanin boko kenan, ata mai basira." Hannu ta bata suka tafa hakan yasa suka fashe da dariya, tsagaitawa Ardiya tayi tace" Kin san me? Ba za ki je ba yanzun, Hadeeya ke yarinya ce, dan a haufe Mu'az ya haifeki dan baiyi aure da wuri bane, na tabbata akwai abinda ya shirya miki, shiyasa ya nemi da ku ha Da mamaki tace" To Momma ya zanyi kenan? Idan fa amincewa zai yi?" Girgiza mata kai tayi tace" Ba ma haka bane, zai yi wuya ya amince a sau e haka, kinsan me?" Ta fa a tana mi o mata wayar tace" Tura masa sa o cewa ba za ki samu damar zuwa ba, da sauri Hadeeya ta shiga yin abinda ta umarceta da shi, tana turawa tace "Yawxa na tura." ar wayar Ardiya tayi ta kasheta gaba aya sannan ta kalleta tace "Kada ki kunna wayar nan har sai gobe da safe, kuma idan ya kiraki karki aga, idan ya turo miki sa o ki duba amma karki mayar masa." Da mamaki Hadeeya tace "Amma Momma me yasa? Idan ya yi zuciya ya shareni fa? Ni fa gaskiya Momma ina sonshi." Da fara'a tace "To ai auren na shi nake son jawo miki, idan ya ga kina rawar afar nan zai ji haushinki, sannan zai ga kin fi shi matsuwa, amma idan kika shareshi bayan ke kike ri e da wannan makamin, dole zai ci gaba da nemanki, dan ba zai so ki tona sirrin future iyalinshi ba." Tintserewa sukayi da dariya suka kuma tafa hannu, jinjina kai Hadeeya tayi tace" Shiyasa nake sonki Momma." "Nima haka." Ta fa a tana mi a mata wayarta, kar a tayi ta fita a akin zuwa na su dan dama kayan kwalliyar mahaifiyarta yasa ta shigowa akin, tana ganin fitarta ta ri e ha a da yatsu biyu ta jinjina kai tace "Mu'az kenan, in kana tunanin yi mata wayo, to ai ni na girmeka, ka ga ba zaka min wayo ba, ka jira ka an, lokaci zai ha aka da matarka." Sai kuma tayi murmushi ta ci gaba da aikinta zuciyarta fari tass tana jin sun gama samun abinda suke so. *Mu'az* na ganin sa onta da sauri ya shiga aika mata kira amma take ake fa a masa wayar kashe, ranshi da yayi ololuwar aci jefa wayar yayi kan kujerar mai zaman banza ya taka birki, ri e ha a yayi yana tunanin duk yadda aka yi akwai mai taimakawa yarinyar nan kan lamarin nan, amma yarinya kamar Hadeeya da wuya ta iya haka, shi da ya so su ha u sai sun ci abinci a hanyarsu ta komawa ya kakkafta mata marin da zai gigita tunaninta sannan ya kar e wayar gaba aya, dan dama bar mata wayar da Saleema tayi bai mata ba, dan ta fara masa rigima ne kawai ya rabu da ita, gashi da wayar da ta bata take neman wula anta ta, shi kam bai ta a ganin an ubanta ka irin wannan ba. Gashi a halin da ake ciki yanzu ba zai so yayi garaje, dan yin haka zai iya jawo kowa ya san abinda ya fara shiga tsakaninsu da Hadeeyar, duk da zai iya murje idanu ya nuna shi bai yi da wata manufa ba, amma Saleema ta fi arfin ya mata haka, ya na jin kunyarta sannan yana darata yarinyar fiye da kima, baya aunar duk wani abu da zai aga mata hankali bare ta shiga damuwa, uwa uba a ce ta dalilinshi ne. Safiyar yau ko da suka tashi da aikin gyaran jikin arta ta farka, da fari ta so dam a komai hannun ar uwarta Lubna, amma dake tana so Alhaji Yusuf ya ga tana ta aiki da jikinta sai ta zage damtse ta fito farfajiyar gidan, wajen hura wutar gawai kanta tasha wahala dan abu ne da baka saba ba, kuma da ta tabbatar yana gidan haka take komai da arfi arfi wai a dole ya gani ko ya ji haushi, dan ta san ya damu da an cikinta sosai. A tsanake ta shiga tu a sabulunta da zallar madarar ruwa peak (mai neman arin bayanin yadda ake ha a sabulu na gyaran jiki, na amarya, na mai jego, ki garzaya ki biya ku in littafin *ni zan ladabi* na Sajida, zaki samu cikakken bayanin yadda zakiyi, abun armashi kuma shine zaki iya yinshi a matsayin sana'a, da ari biyar kacal yar uwa ki gyara rayuwarki), tana cikin aikin ya fito zai fita, ya jima tsaye yana kallonta amma ta yi kamar ba ta ganshi ba tana ta aikinta, girgiza kai yayi ya wuce kawai dan ya kula magana take nemanshi da ita. Tana gama tu a sabulunta ta saka mishi kurkum mai haske da ja saboda kalar fatar Saleema sannan ta juyeshi a bokiti ta kai aki ta aje inda babu rana, sai da ta gama ha wan da za ta shafa mata a jiki saboda duhun fatarta tana bu atarta ta ga fuskarta na yalli da she i yasa za ta ata wannan ha in, tana gama ha awa ta tasheta a baccin da ta koma bayan sallah asuba, saida ta fara bata sabulun Anakonda wanda shima ta sakashi a cikin ha in sabulun nan ta ce ta yi wanka, dan zai taimaka sosai wajen cire mata datti da wata tsohuwar fata, bayan ta fito ta tsane jikinta sosai sannan ta zauna kan leda ta fara shafe mata jikinta da farin wan (shi ma dai wannan ha in zaku sameshi a wannan littafi na ni zan ladabi, iya katin waya ma ya isheki ki dogara da kanki yar uwa,
Chapter 49 · 0% Book details