← Book details Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 116

Sashe 71

Baiwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

san tana zuwa wajen nan da sunan inki ba, a ce ita ce haka ya sameta? To yanzu me zasu fa a musu? arku ta rasu? Rashin sanin abun yi yasa Huzeifa sake juyowa inda Sharhasila take lokacin da Mama da Fareeda suka tallabi Saleema aka saka a adaidaita sahu, kifeta ya sake yi da mari ya nuna mata hanyar fita daga shagon a ufule sosai yace "Fita daga nan Sharhasila, karki bari na sake ganinki, ke mai kama dake ma bana son sake gani a rayuwata, na tsaneki na tsaneki Sharhasila, sannan na sakeki saki aya." A sukwane ya nufi hanyar fita sanda Sharhasila ta ora hannuwa a kai ta fashe da kuka, tsayawa yayi tare da kamo hannunta ya wurgo bayan anwarta da tsoro yasa ta fit a shqgon, da hannu ya shiga nuna mata yace" Ni kika kashe Sharha, saboda kin *kashe yarinyar da nake so*, ba zan yafe miki ba wallahi, na tsaneki, kin ci albarkacin ana da yake cikinki, wallahi da kema na kasheki in ya so a kasheni." A hanzarce ya shiga adaidaitar suka aga zuwa asibiti, suna tafiya kuma dreban na dawowa, anwar Sharhasila ce ta fa a mishi an tafi kai ta asibiti, dan daga kwatancen daya mata ta gane ita yake nema, bayansu ya bi cike da zulumin me ke faruwa. Da fari kamar gaske haka ake kar esu, amma da aka ga raunin sai likitocin suka ce dole a zo da wani jami'in tsaro saboda tayiwu fa a ne aka yi, lokacin da aka tabbatar musu tana raye hankali tashe Huzeifa da ba mai son hayaniya ba yace "Duk da tana da rai har yanzu ba zaku dubata ba, wannan ai dokar banza ce da wofi, kenan sai abar rayuka su salwata saboda doka?" Malamar asibitin cike da tausayawa tace "Ka yi ha uri, ni ba abinda zan iya yi muku, yalla ai ne bai bada damar ba, kula yana ganawa da abokinshi ne ya ce kar a takura masa." A gigice Huzeifa ya fita daga asibitin dan yin abinda ya dace, a shirye yake da ya mi a kanshi a matsayin mai laifin indai za'a duba Saleema ta farfa o. Fareeda na kai kawo daga wannan bango zuwa wannan, Mama tana zauna kan benci ta kifa kanta sai gunjin kuka take tana ta maimaita "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Ita bala'in nan ta na dubanshi ne ta wata fuska daban, shiyasa take fatan Allah ya zame musu gata kawai, suna haka *Mu'az* daya fito daga ofishin babban likitan ya gansu, tausayin halin da ya gansu ne yasa shi tsayawa yana tambayar Fareeda lafiya Mama ke ta kuka? Da sauri Mama ta taso a rikice ta kalleshi tana fa in "Yalla ai dan Allah ka taimaka mana, yarinya ce muka kawo amma sun i dubata wai sai jami'in tsaro ya zo, dan Allah ka taimakemu ka mana rai." Da yanayin tausayi yace "Tana ina yarinyar? Me ya sameta?" A tare suka nuna mishi akin da aka kwantar da ita, da sauri ya shiga takawa ya nufi akin, yana bu ewa idanunshi suka sauka kan Saleema daya kwashe watanni rabon da ya sakata a idanunshi idan ba hotonta waya aya tak da yake da a waya kuma yake kallo ba kullum. A rikice ya isa gareta tare da kai hannayenshi yana neman rumgumota yana fa in "Saleema, Saleema, ke, ke! Dan Allah ki bu a idanunki, likita!!!! Likitaaaa." Juyowa yayi da gudu zai fito sai ga Fareeda da Mama sun taho a sukwane jin arajin balagaggen matashin nan, a hukace y nuna Fareeda da hannu yace "Saleema ce wannan, me kuka mata? Me ya sameta? Jini fa take zubarwa, kira min likita..." A duburburce ta juya ba tare da sanin ina zatayi dan kiran likitan ba, saidai tana fitowa ita ma suka ha e da likitan wanda wannan araji da yayi na arshe ya fargar da duk wanda ke kusa a lokacin. Mu'az da wata malamar asibitin ne suka tsaya a kan Saleema dan ceto rayuwarta, wacce kafin komai saida aka fara ara mata jini, sun dai yi mata aiki da ya inin jijiyar wuyan hannunta dake harbawa a matu ar sai ance, wanda hakan shi ya fi agawa Mu'az hankali har yake tunani zuwa yamma idan bata farfa owa zai sa Abbanshi a maganar ne a auketa a jirgi marasa lafiya a fita da ita ko ina ne ma dan ta samu lafiya. Huzeifa ya dawo tare da wani jami'in, saidai sun samu har an mata aiki, jin ba'asi da neman fitina yasa jami'in har ya uresu saida suka fa a masa yadda komai ya faru, adireshinsu ya tambaya tare da ba da tabbacin dole Sharhasila ta fuskanci hukunci ko ar wacece, Alhamdulillah dake jami'anmu da zafin nama da kuma ba wa kowa ha inshi, sai ga Sharhasila a hannunsu a karo na ba adadi wanda ita hakan ba ba on abu bane a wurin, dan indai rikici zai ha ata da kai to ta yankeka ko ta sokeka aramin aiki, hakan kuma ya samo asali ne daga ahalinsu. (bana so na fa i sunan halin *Mu je da sauri* _(Rikicin na gaba)_ Babu hankalin wanda bai tashi ba da jin wannan lamari musamman Safiya da tsabar rikicewa sai Alhaji Yusuf ne ya biyota da yaron a baya, ta yi kuka kamar ranta zai fita, Alhaji Yusuf da Alhaji Auwal da shima ya zo suka shiga kai da kawowa daga yadda za'a nema mata lafiya zuwa maganar Sharha dake ri e, a lokacin ita ma Babanta ya san maganar ya fara nuna na shi ikon wajen ganin an fito masa da a dake auke da ciki. Har lokacin kuma Maman Huzeifa da Fareeda suna asibitin, Huzeifa kuma kunya da rashin sanin abinda zai fa awa iyayenta yasa a ofar shiga asibitin yake zaune ya yi kuka har ya gode Allah. Misalin 08:00 na dare Ambulance ta tsaya a daidai ofar shiga inda aka turo Saleema akan gadon majinyata za'a kaita babbar asibitin Reference dan an fi kayan aiki da kuma tsananta kula, a ganinsu nan duk wasa ake ba aiki ba, ana sakata cikin motar Alhaji Yusuf ya matsa kusa da Maman Huzeifa da ita dai bata da niyyar barin wurin nan sai ta ga yadda ta yiwu, cikin ha e fuska da kakkawar da kai yace "Zaku iya tafiya gida, kunga ai asibiti ma za'a canza mata, mun gode sosai." Cikin dasashiyar muryar kuka da ko ji ba'a yi da kyau tace "Dan Allah Alhaji kar ka hanamu ganinta, ka bari muje tare da ku muga halin da take ciki." Ba alamar sassauci yace "Dattijuwa zaku iya tafiya, dan Allah ku barta haka ta huta." an tsaki yayi tare da wucewa ya barta nan tsaye, da gudun ceton rai Ambulance in ta fita a asibitin wanda yasa Huzeifa mi ewa tsaye ya bi motar da kallo, yana tsaye motar Mu'az ta wuce ya bishi da hararan da har yanzu zuciyarshi tambayar wanene shi take? Shishiginshi yayi yawa kan lamarin Saleema? Me ye tsakaninshi da ita? Shi dai a saninshi fa a mishi take ba ta da saurayi, sannan ya lura shine a ga waccen Alhajin mai kirki da Hajia Rabi da ya sani ta dalilin inki wacce ita ma tana asibitin. Motar Alhaji Yusuf ce ta biyo baya sai kuma ya tsaya tare da fitowa a motar, Safiya dake kallonshi da tunanin me zaiyi kuma ga arta can a wani hali idanu ta zuba mishi, tsaye yayi gaban Huzeifa yana are masa kallo, a tausashe yace "Ina kuka san juna da Saleema?" Cike da ladabi kanshi a sadde yace "Alhaji tun a makaranta ne, wasu lokuta idan babu malami a ajinsu na kan shiga na koyar dasu abinda na sani, sai kuma dalilin inki da watarana suka ao kar a na Hajia Rabi." Fuka a ha e yace "Tun yaushe?" A sanyaye yace "A alla wata bakwai." Jinjina kai yayi yace "Akwai wani abu a tsakaninku ne da har take zuwa gidanku?" Da sauri Huzeifa yace "A'a wallahi, kawai dai ina koya mata inki ne, bayan haka ba komai." Da mamaki ya ance idanu yace " inki? Ka koya mata ba izinin mahaifinta?" an sosa eya yayi yace "Ka yi ha uri yalla ai, ta nuna min tana so ne sosai, burinta kuma na da mahimmanci a gareni..." A tsawace Alhaji Yusuf yace "A gareka in banza, ni ne mahaifin Saleemaa, ni na haifi ata amma kai za ka min iko da ita?" A ki ime Huzeifa ya kalleshi idanunshi na ara kawo ruwa dan shi fa tunaninshi da yake zaunen nan shine, zuwa wayewar gari zai tattara duk abinda yake da shi ya dam awa mahaifinta a matsayin sadaki sannan su aura musu aure dan ya samu damar jinyarta shima, amma ba wai ya tsaya a ofar shiga ba saboda kunya da tsarguwa, dan haka yake so su rabu lafiya kar suyi husuma da future sirikinshi, a ladabce yace "Ka yi ha uri Alhaji, kuskure ne ba zan sake ba, dan Allah ka yafe min." Sadda kai Alhaji Yusuf yayi bai ce komai ba, jim ka an ya fara shashe ar kuka, hakan yasa a rikice Huzeifa ya kai hannu zai ta ashi da sauri Alhaji Yusuf ya dakatar dashi ta hanyar aga masa hannu, aga kai yayi ya kalleshi hawaye sun wanke masa fuska, cikin muryar kuka da jimami da tausayin arasa da har yanzu ba wanda ya ce masa za ta rayu ya ha e hannayensa alamar ro o yace "Dan Allah ka yi nesa da ita, kada ku sake shiga rayuwata, da gata na raineta har ta kawo yanzu, ko ciwon kai bana iya tuna ranar da tayi mai tsanani idan ba ciwo na al'adarta ba, dan Allah dan soyayyarka da iyayenka ka fita a rayuwarta, bana son sake ganinku a nan daga yau, dan kai ka sa ta bijirewa maganata, idan kuwa ka sake nuna mata fuskarka, to ka sani zan yi hushi da Saleema hushi na har abada, dan inki baya cikin tsarin abinda zan iya barin ana su yi, dan Allah ka min wannan alfarmar a matsayina na ubanta, ka fahimci abinda ke zuciyata sannan ka kwatanta kanka da ni, kaima an ce zaka zama uba nan kusa ka an." Sakin hannayenshi
Chapter 71 · 0% Book details